Sashe 40
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shigowar Mum ya sa duk suka maida hankalin su kanta, fuskar nan a ɗaure tamkar ba ita ce Mum ɗin da ke ɗokin su ada ba, jiki ba kwari suka mata sanu da zuwa ba tare sa ta amsa ba ta dubi Abdallah cikin faɗa take faɗin " kai wannan wane irin iskanci ne da zaka ɗoran kafafu kan kujera, ko kuwa tarbiyar da ubanka maras tarbiyya ya ma kenan?"
Kallon ƙafafun sa Abdallan ya yi shikam ko ya makance ne dan kuwa bai ga kafafun sa kan kujera ba, Kursum ce ta ce "Mum ki kalla fa, ba'a kai kafar sa take ba" watso mata baƙar harar da ta y ne yasa ta yin shiru yayin da Abdallah din ya sauko daga kujerar, tsaki Muk taja tare da yin gaba Kursum tace kagani ko yata shi yasa nace bana son gidan nan yanzu Mum ta tsane mu.
Juyowa Mum ta yi cike da fushi tamkar da babba zatai magana tace "to dan ubanki ai sai ki haɗa kayan ki, ki tafi, shegiyar yarinya mai gadon baƙin hali....."
**********
Tunsa Muktar yazo office yake kallon saƙon Hafsa har ya fara mata typing reply sai kuma fasa ya janyo file ya hau dubawa sai dai kuma tunanin saƙon ya tsaya masa a rai, yasan in baiyi wani abun ba kallon saƙon zai iya sawa yayi abinda bai niyya ba, hannu yasa ya danna delete ya jima yama shakku kafin ya danna confirm.
Ganin ba zai iya komai ba a offis ɗin ya shi miƙewa ya bar office ɗin kai tsaye inda yake aje mota ya nufa, kunna motar ya yi ya nufi gidan su Hafsa.
Tana zaune tana tunani wayarta, ta dawo da ita ganin sunan Muktar na yawo kan screen ɗin yasa ta washe baki, ina ƙofar gida taji yace ba tare da ya jira sunyi gaisuwar da suka saba ba, bata damu ba ta miƙe cike da murna ta zari hijabi dan a shirye take, har ta fito ta dawo ta kuma kallon fuskar ta a mudubi, man leɓe ta ɗan murza sanin yana son ganin sa a laɓɓan ta, farin cikin da take ciki tamkar cewa yayi ta fito su tafi, kai tsaye ta nufi ƙofar gidan can ta hangeshi jikin mota harɗe da hannayen sa a jikin kirji ta kuma washe baki kafin ta nufi wurin......
*********
Rabon da ta tsinci kanta a cikin walwala har ta manta. Tun da satin nan ya kama har yazo ƙarshe bata jin ta samu sukuni a ranta ko na sakan daya sai gashi jin muryar Mukhtar gami da ɗora idanun ta kan sa sun sanya ta a cikin farin ciki marar misaltuwa. Ba wani abun yace ba, kawai jin muryarsa babu wannan kaushin ya saka har hardewa take a hanyar zuwa kofar gidan nasu. Tayi sa'a bata tarar da kowa ba a hanyar.
Ta jima tana kallonsa cike da so da kewa mai yawan gaske. Zuciyarta na bugawa da sauri, da kyar ta samu ta nutsu kafin ta ƙarasa.
Kamar budurwar da tayi sabon saurayi ta sunne kai kasa tana masa sallama hade da gaishe shi murya ƙasa ƙasa.
"Mu shiga ciki mana.." ta fada, tana ɗago kanta.
Ya kalleta sannan ya dauke kan sa da kyar. "Nan ma ya isa."
Take jikin Hafsah yayi sanyi saboda jin amon muryarsa da yake nuna sam yanzu bata cikin burikan da yake son cimmawa amma bata haƙura ba.
"Abu Abdallah, we are above all these..." ta saci kallonsa taga ya zaro wayarsa ya duba sannan ta cigaba duk da tana gani ƙirƙiri hankalinsa baya kanta.
"Dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya..." Kafin Mukhtar ya ankara sai ganin ta yayi ta durƙushe a gaban sa. Takaici ya cika masa zuciya, bai san lokacin da Hafsan sa mai aji ta zama mara zuciya haka ba, da kyar yace ta miƙe.
"Tashi mana Hafsah meye hakan?" Ya maimaita sannan ta miƙe da guntuwar murnar ta. Sai da ta goge hawayen da suka zubo mata sannan ta jingina da jikin motar.
Mukhtar ya kalle ta, zuciyarsa ta karye da ganin yadda duk ta zabge lokaci guda. Don kar ta sake bashin kunya a titi ya ce ta shiga mota akwai maganar da zasuyi.
Ba musu ta shiga gidan gaba shima ya shiga. Sun jima babu wanda yayi magana kafin Mukhtar din ya gyara muryarsa, yana tattaro dukkan jarumtarsa ya dora akan harshensa.
"Hafsah so nake ki nutsu ki fahimce ni. Zama a tsakanin mu ya kare, ba wai don na tsaneki ba. Ke din kina da muhimmanci a gare ni, kuma kin fi kowa sanin bana son naaci da magiya. Daga yau bana son na sake ganin sakon ki makamancin wanda kika turon jiya Hafsah..., Nayi niyar kawai in ƙyaleki ko in yi blocking ɗin ki sai naga ai akwai mutane tsakanin mu innayi blocking ta yaya zan dinga jin wani abu game da yaran, wannan yasa nace bari in zo da kaina zaki fi fahinta fiye da in saƙone"
"Amma Abu Abdallah ko dalilin sakin ai da sai ka...."
Ɗaga mata hannu ya yi " Aure dai lokaci ne kuma raine da shi, namu lokacin ya ƙare ran kuma ya mutu, dan haka dan girman Allah Hafsa karki kuma turon saƙo irin na jiya, ina ma kin kusa gama idda?, ki cireni a rayuwar ki yadda na cire ki, zai fi miki..."
Kallon sa ta yi tsar so take ta gano Muktar ɗin tane wannan kuwa ko wani mai irin muryar sa ne, sai dai idanun ta shi suke gani, bata kuma cewa komai ba ta buɗe motar ta fice har ta fice ya kira sunan ta, juyowa ta yi batare da ta ce komai ba ya buɗe akwatun gaban Motar ya zaro farar takarda ya miƙo mata.
Kallon sa ta yi da alamar tambaya idanun ta na faɗin me zan da ita?, " Naga kamar baki yadda na sake ki ba, nace bari in rubuta miki, duda ma kin kusa gama ida, ina miki fatan samun miji na gari," kamar ba zata amsa ba, ta miƙa hannu ta amsa tare da yin ciki da sauri.
Can bayan gidan ta ɓoye cikin bushiyu tana kuka tana kallon Paper ɗin tabbas rubutun Muktar ne, sharkaf ta jiƙe paper ɗin da hawaye, maganganun Bilkisu kawai ke dawo mata, tabbas bata da hankali da tayi tsanmanin Muktar zai iya mayar da ita, goge hawayen ta tayi tare da miƙewa har ta fara tafiya sai kuma taja ta tsaya takardar hannun ta, ta yayyaga ta watsar aranta tana ji tamkar Muktar ɗin ne ta watsar.
A falo ta tarar da yaran ta sunyi jigum jigum, wuri ta samu ta zauna, ta hau jansu da wasa, duda cewar ranta ba daɗi...
Shi kuma Muktar yana kallon ɓacewar ta ya mari goshin sa tare da faɗin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, anya ni ne kuwa, ya ilahi, ya jima a ƙofar gidan sai da yaga motar Abban su Hafsan tayo Layij yayi sauri ya yi baya tare da barin wurin, tsananin nauyin Abban yake ji, baima san da wane ido zai kalle shi ba.
*****
Zaune suke a falon Faruk yana koyawa Kulsum rubutu yayin da Abdallah ke gefe yana karatu Khalil ya shigo ƙannen sa suka mara masa baya, Kulsum ta miƙe da gudu tana murna ga yaya ga yaya, shima dariyar yake suka riƙe juna, ina "Aiman" ya tambaya.
Sakin sa ta yi tare da turo baki, "ba ya tafi gidan Ummi ba, ni suka barni anan..." Bai bata amsa ba Mum ta fito cike da fara'a a'ah yau su Walidin din ne a gidan ƙaramin ƙanin Khalil ɗin yasa dariya tare da yin gun ta da gudu akai rashin sa'a ya faɗi yuf bayan karo da ƙafar Faruk.
Da hanzari Mum ta ƙaraso ta kwaɗe Faruk cikin faɗa take magana " kaga azzalumin yaro mai halin Ubansa, wato san tsaɓar mugunta shine zaku harɗe shi."
Abdallah ne ya tsaya da karatun nasa kamar zai magana ran sa ɓace sai kuma ya fasa yayin da Walid ke ta faman tsanyara kuka, Faruk ne yace "wallahi Mum ba harɗeshi nayi ba," tsaki taja tare da doka masa harara "eh ai na saba ƙarya, ka harɗeshi a ido na kace ƙarya nake"
Khalil ne ya matso "kai Hajiya Mum kodai kin fara rikicin tsufa ne, ai ba harɗe shi yayi ba"
Harar Khalil ta yi "indai wannan yaran ne da sukai gadon mugun hali to wallahi ba ababen goyo bane, haka uwar su ta je ta goya ubansu ya watso da ita bisa dutse" hannun Walid ta kama muje kaji Allah zai saka ma sukai cikin falon ta.
Khalil ne ya dubi Faruk ka yi Hakuri kaji Faruk ranta ne a ɓace, kafin Faruk yace wani abu Kulsum ta ce "ai mun sani yanzu Mun ta zama masifaffiya shi yasa ma ba ruwan mu da ita" ajiyar zuciya Khalil ya yi tare da yin ɗakin Mum ɗin tana ta faman wasa da Walid Khalin ya shiga da sallama, harar Walid da ya yi ne yasa shi taɓe baki zai kuka cikin kakkausar murya Khalil yace wallahi ka sake kamun kuka sai na bubbuge ka, mara kirki kawai maza fita kaje ka bawa yaya Faruk Haƙuri, mara kirki kawai ai kasan ba shi ya yadda kai ba dan sharri kana ji ana masa faɗa kayi tsit da sai ka ce faɗuwa kayi"
Mum ce ta ce ba inda zashi ai agaban ka ya fyalle shi, Khalil bai ce komai ba sai harara da ya watsowa Walid ba shiri yaron ya fice, inda Faruk yake ya nufa, cikin muryar nadama ta yara yace "yaya Faruk kayi haƙuri kaji" murmushi Faruk ya yi tare da kamo hancin sa ni banji haushin ka ba zonan ya kamo shi ya ɗora shi a cinya.
Nazir Wanda yake kusan sa'an Abdallah ya ce, ai Walid indai sharri ne ba daga nan ba, kaga dai ya baka haƙuri muna zuwa gida zaice kai ka faɗar da shi, dariya Faruk ya yi, tare da faɗin "yaron kenan"