← Book details Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 43

Sashe 15

Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Khalil ya ruga ya tsaya cikin daga murya irin ta yara ya ce "Good morny Mum" murmushi ta yi ganin ya yi gaba abin sa.

Juyowa Abba ya yi ya kalle ta "wai yaushe zaki mayar musu da yaran su karfa yaron nan yacire kunya ya zo amsar su"

"Mayar ya kuma? Ai na amso su kenan ta faɗa tare da barin wurin" girgiza kai kawai Abba ya yi yana darya shikam bai taɓa ganin inda uwar mata ke iko da jikokin ta ba sai kan matar sa, shafa kansa yayi "Hadiza ta akwai rikici"

Dariya ta yi tare da juya idanu

Tun da aka buga ƙararrawar fitowa break ya hanzar ta dan zuwa ganin Hafsan tunda ya shigo makarantar yaji yana son ganin ta sai dai kasancewar ba dabi'ar sa bace zuwa aji gun malami yasa ya daure zuwa a fito break ɗin.

Annurin fuskar sa ne ya ɗauke hango wurin wayam ba kamar yadda ya saba daga nesa zai hango kanta alamun tana zaune a sanyaye ya karasa ya zauna lokacin lokaci yana duba agogo da hanya ko zai ganta tayo wajen sai dai babu alamar ta duk son sa da fanke yau kasa ci ya yi ji ya yi duk ya gundure shi, rufe langar ya yi tare da miƙewa sakamakon buga ƙararrawar da akai ta komawa aji har ya yi hanyar office da zummar aje langar sa sai kuma ya yi ajin da aka bawa Hafsan primary 2 ne teacher per class ne, gaban sa ke dukan uku uku dan bai san mai zai ce mata ba har ya ƙarasa bai iya tsaida abinda zai ce ba ya juyo muryarta na faɗin "lah Uncle ina kwana?"

Juyowa ya yi fuskar sa ɗauke da murumushin da bai san ya iya irin sa ba ya ce " lafiya ƙalau, Aunty"

"Kaga baka ganni ba ko?, Abubuwa suka sha min kai walllahi"

Murmushi ya yi "aifa na ce yau wannan sarkin mallake kujera ko lafiya kinga na ma kawo miki waina baki fito ba ya miƙo mata" amsa ta yi tare da faɗaɗa murmushin ta kai amma Nagode walllahi kamar kasan ban karya ba shirya Kalil ke makarar dani.

Murmushi ya yi bari inje kar mu shiga lokacin ɗalibai tom ta ce ya yi gaba cike da kwarin gwiwa sam bai zata zai iya yin jarumtar nan ba ko da yake da bata leƙo ta ganshi ba har ta masa magana sai dai ya juya.

Juyuwar da ya yi yaga ta koma yasa shi sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da tafiya.

Tafe yake a nutse, lokacin da aka tashi zuwa titi mota ce ta tsaya gefen sa har ya yi gaba ya ji muryar ta na faɗin uncle ina kayi?"

Juyowa ya yi " cikin gari na yi, kamar ba hanyar mu ɗaya ba"

Murmushi ta yi "yau ƙoƙi zani gidan kakan ni na sai mu saukeka a hanya shigo"

Buɗe gidan gaba ya yi ya shiga suka gaisa da Malam Musa driver, sai dai ku saukeni a school of hygiene zanyi submitting form din ƙanwa ta," "tom" Hafsa ta ce, komai ta tina kuma ta ce " ina ne unguwar ku, form din kawai zaka miƙi?"

" Dala ne, eh shi kawai zan bayar" ya faɗa a takaice

"Ah tunda hanya ce Malam Musa sai mu jira shi ya bada ko?" Ta faɗa tana mai mayar da hankalin ta kan Malam musa, wanda ya gyaɗa kai tare da jan motar....

Faka motar da Malam Musa ya yi cikin harabar school of hygiene yasa Muktar buɗewa ya fito, ɗan sunkuyowa ya yi bakin tagar "ina zuwa yanzu zan miƙa in fito" murmushi kawai Hafsa ta yi ya yi gaba, yadda zuciyarta ta kasa yadda cewar wannan Makaranta ce ta gaba da secondry yasa ta buɗe motar ta fito, a nutse take tafiya tana bin tsirarin daliban da ke kai kawo, zagaye makarantar ta yi duka makarantar a idanun ta bata fi Faculty ɗin su ba, sai da ta gama yawon ta sannan ta dawo riƙe da alawar madara da ta gani gurin wata ɗaliba ta siya, Hango Muktar tsaye jikin mota yasa ta yin sauri ta karaso.

" Lah har ka dawo, Na bar ku kuna ta jira ko?"

Murmushi ya yi "a'a nima yanzu na fito" ya faɗa tare da matsawa daga jikin ƙofar motar bayan ya buɗe ta shiga shi kuma ya buɗe ƙofar gaba Malam Musa ya ja motar sukai gaba.

Kasancewar zasu sauke Muktar a Dala yasa Malam Musa bi ta cikin gari, ganin an biyo ta kasuwar kurmi ya sa Hafsa tunawa sunyi da Hidaya zasu so kamar ta ce su tsaya sai kuma ta tuna da halin Hidaya in taji ta zo ita kaɗai akwai rikici, adai dai ƴan Kado suka sauke Muktar yana ta faman zuba godiya kafin su wuce.

Hangar Malam da Hafsa ta yi yana alwala lokacin da suka shigo layin yasata faɗaɗa murmushin ta tamkar ta matso kusa da shi.

Cike da fara'a ta ƙarasa inda ya ke alwalar, shima murumushin yake, rissinawa ta yi ta gai da shi kafin ta ce " yau zuwan nawa a sa'a na yi tunda ns fara tozali da rabin raina"

Dariya yi "assha ashema rabin rai ne abu bai yi daɗi ni da nake son fadar duka" itama dariya tasa a'a inna saka duka ran ina zan kai su Abba?" Karasowar Malam Musa riƙe da Jakar ta yasa ta amsa ta yi gaba tare da barin su suna gaisawa.

Kai tsaye gidan ta nufa, ƙarami ne ba can ba yafi rabin fuloti anma baza'a ce fuloti bane ginin ya yi kyau sosai dai dai misali ginin siminti ne ba shi da gate anma ba zaka kira shi gidan talakawa ba, gidan masu rufun asiri yafi dacewa da shi, da Sallama Hafsa ta shiga lokacin da ta wuce zauren farko, "a'a muryar waye nake ji kamar Muryar Bebilo" Gwaggo da ke zaune kan ƴar ƙaramar kujera ta mata tana wanke wanke ta faɗa" turo baki Hafsa ta yi lokacin da ta shiga riƙe da Jakar ta " Ni sai in koma, kurum dan mutun ya tsufa sai ya dinga faɗamin sunan tsoffi"

Dariya Gwaggo ta yi " kajimin ja'irar yarinya Ba sai ki koma ba, ai kinfi ni sanin hanya tunda ta ita kika bi kika shigo"

Malam da ya shigo riƙe da buta ne ya ce "koma kinji Hafsatu na, kyale ta kishi take"

murmushi Hafsa ta yi kamar dama da gaske komawar zata yi kafin ta ce "to ba inda zani tunds dai wanda nazo gunsa yana maraba"

Dariya suka sa dukkan su sannan suka soma tambayarta mutanen gida.

“Duk suna lafiya. Ina kawu Halipha?” Ta tambaya tana shigar da akwatin ta dakin Goggon. Kamshin turaren wuta ya doki hancinta har yasa ta rufe idonta. Son kamshi a jinin kakarta da mamanta yake amma ita bata wani damu ba. Tana yabawa da kamshi in taji sai dai bai dameta har ta saka da kanta ba.

Da akwatin ta a baya ta karasa shiga ɗakin wanda yake matsakaici ne. Gefen wardrobe ta hanga inda zata saka akwatin nata. Kamar ta tuna wani abun ta daga kai ta kalli jerin tukwane da tangaren da suke saman wardrobe din. A kullum burgeta sukeyi saboda babu inda ta taba ganin irinsu banda wajen Goggon. Kallon jeren take yi, girma girma kuma samfuri daban daban yasa ta soma kirga su.

Tana kirgen ne Goggo ta daga labule ta shigo ta tarar da ita. “Bebilo…” ta kira tana katse Hafsah wanda yasa ta buga kafa.

“Oh Allah, Goggo kin katse ni.” Goggon tayi dariya.

“Seti goma ne dani in fada miki domin ni yar gata ce. Daga baya na saida me ros da me bakin les dina. Ke har kumbo gare ni me sha biyu.” Goggon ta fada tana zama a gefen karamin gadon ta da yake kusa da babban gadonta wanda Hafsah take so.

“Ni ba ganewa nake ba fa Goggo. Wannan gadon naki ne dai nake so ki bani na tafi dashi gida kin ki.” Ta fada tana danewa kai gami da kwanciya a kan filon.

Goggon ta murmusa. “Sai randa kika bar mun miji zan baki.”

Hafsah ta tabe baki. “Toh me zanyi da mijin ki duk furfura? Kan shi ma duk sanko. Ni kuwa wanda zan aura in kika ganshi sai kinyi kishi.”

“Bebilo kenan. Allah ya nuna min ranar nan.” Goggon ta tashi ta fita.

Da yake Goggon ta jima da fita, hakan ya bawa Hafsah damar yin tunani akan maganar da sukayi. Wanne irin miji take so? Shin ita zata taba yin aure kuwa? Ba ma wannan ba, ita bata taba soyayya da kowa ba kuma finding her spec was the biggest challenge ever. Sau da dama Hidaya tana hada ta da mutane amma tana rejecting da taga hotunan su saboda sam basuyi mata ba. Ko saurayin Hidayan ma sam inda itace ko kalle bai isheta ba shiyasa ma bata son kalar hirar da ita.

A wannan tunanin ta tuno da Bilkisu wadda hakan yasa ta danna mata kira.

****

Zaune suke a tsakar gidan. Fili ne fetal an kawata shi da shukoki masu ban sha’awa da dain kallo. Wasu a cikin su suna da fure me kamshi sosai musamman ma da daddare. Daga gefe guda kuma wata yar rumfa ce haddadiya da akayi ta da itaciyar bambu. Idan mutum ya zauna a rumfar zai iya hango kwalliyar gidan nasu. Sau da dama Bilkisu ta kan fito nan ta zauna tayi karatu iska me dadi tana kada ta.

Hakan yasa da aTariq yace zai zo ta gayyace shi nan. A zuwan sa na biyu wanda shine yau ya saka ta tanadi karamin kafet da ta shimfida kasan teburin wurin.
Chapter 15 · 0% Book details