Sashe 20
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyi yake a kan katifar amma ya kasa yanke shawara. Yana so ya taimaki Hafsah amma yana duba gidansu. Family first, family over everything. Ganin dai duk yadda zaiyi ba zai iya shawara shi kadai ba yasa ya nufi dakin kannensa. A karon farko da zai tambaya shawararsu ba ta Inna ba.
Saboda yasan Inna cewa zatayi kawai yayi.
Zaune ya same su suna hira ko wacce ta amsa sallamarsa. Fitilar kwan dake ci ya kalla yaga hasken babu yawa sannan yace.
“Fitilar ma sai an gaya muku kun kunce ku wanke kwan ko?”
Juwairiyya ta kada kai. “Ai wankin Hajara ne kasan kuma duk sanda ta dauka sai ta fasa.”
“Wallahi yaaya karyane. Itace fa ta fasa dayan.” Ganin zasu fara musu yasa ya daga hannu.
“Duk ba wannan ba. Ni kawai shawara nake baku ku zama masu tsafta kafin kuje gidan ku. Musamman ma Hajara da naga Garban nata dan gaye ne…”
Hajarah ta sunne kai kasa ita kuma Juwairiyya ta kwashe da dariyar tsokana. “Tab Yaya wannan garan? Kayan miya yake tsaidawa fa…”
Hajarah ta harare ta.
“Bar ta Hajarah ai ita ko mashinshini babu.” Hajarah ta kwashe da dariya sannan ta mata gwalo tace,
“Sana’a sana’a ce dai. Kuma gonar ma tashi ce a wajen sa da yawa suke sarar kayan miya. Ko ba komai ba zan kwana da yunwa a gidan sa ba. Ehe…”
Kallon da Mukhtar ya musu ne yasa ba wadda ta kara cewa komai. Nan ya shiga gaya musu yadda sukayi.
“Maganar karin dubu ashirin akeyi amma kunsan kasancewa tare da ku yafi min dubu ashirin.” Suka yi murmushin jindadi sannan suka ce.
“Mu ma muna son ka.”
“Amma Yaya babu komai ka karba kawai in da wata matsalar daga baya ba sai ka ce ka fasa ba?” Juwairiyya ta fada.
Hajarah ta yi shiru sannan tace, “Ni dai kar aje a siye mana yaya. Kasan masu kudinnan.”
Sukayi dariya sannan ya mike.
“Toh zan dai yi tunani.”
Da haka ya bar dakin ya koma nashi ya kwanta. Kaso me yawa ya tafi ga karban aikin a ransa inda ragowar kason yake makale da family dinsa…
Kukan da Khairi ke ta faman zabgawa Momy ta faman lallashin ta yasa Usman da ke zaune yana faman duba takardun ɗaliban sa miƙewa, falon ya fito a nutse ya ɗauki yarinyar Momy bata ce komai ba zaton lallashin yarin yar zai yi ɗakin Hafsa ya nufa inda ya fito riƙe da hannun Khalil wanda ke ta wasa abinsa.
Tsallen murna yaron yake ya biyo Usman ɗin a baya yana tsalle suka fice a baya ya sanya Khairin shima Khalil kusa da ita yaja ya zauna inda Usman ya hau mazaunin driver ya ja motar Khalil ya leƙo gaban motar "Uncle unguwa zamu?"
"Gida zan mayar da ku" abinda kawai Usman ya ce kenan Kalil ya koma lakwas rai ɓace, a dai dai ƙofae gidan yayar tasa ya faka motar ko ciki bai shiga ba ys buɗe ya fito tare da saɓo Khairin a faɗa Khalil ya biyo bayan sa bugu guda Mai gadi ya buɗe ganin Usman yasa shi matsawa gefe alamar ya shigo sai da suka gaisa sannan ya yi cikin gidan.
Farida na zaune tana kallo ya shigo da gudu Khalil ya ƙaraso ya rungume ta, ta cafe shi tana faɗin ɗan lele na " ɗazun nake cewa zani ganin ku ashe kun tafe" aje Khairi Usman ya yi, ta ko zunduma ihu ba zata zauna na Usman ya miƙawa Farida ita, ta kuma maƙale shi, "kin gani ko kawai kik ɗauki yara kik kai wani wuri jibi tama manta da ke" ya faɗa lokacin da yake ƙokarin sauke Khairin.
Hararar sa Faridan ta yi "gidan iyayen nawa ne wani wuri?"
"Nidai koma mene yaran nan takuramin suke ko jiya inason in bacci Khalil ya zo ya takuramun sai dai muyi game, to ni ba Hafsa bane"
"Eyye sannu issasshe kaine ma wa na, ka shigon gida ba ko gaisuwa ka hauni da faɗa,"
Murmushi ya yi "ayi haƙuri Hajiya Aunty Farida, Ina wuni?"
Harar sa ta yi ka ɗauki yaran nan ku koma, tumma kan Baban su ya dawo, dangwarar da khairin ya yi tare da yin waje da gudu, tsaki taja tare da ɗaukan wayar ta tahau kiran Momy.
Momy na zaune tana hutawa kiran Farida ya shigo da murmushi ta ɗaga " Momy kece kika sa Usman ya kawo su Khalil"
Miƙewa Momy tayi tamkar tana kallon Faridan " gida kuma nifa ɗaukan ta yayi zai lalllashe ta bar in sa Hafsa ta zo ta tawo da su"
"Yawwa Momy kisa tazo yanzu, kafin Abban su ya dawo yama gansu"
Katse wayar Mum ta yi tare da yin ɗakin Hafsa zaune ta same ta gefe guda takar du ne, ba tare da ta zauna ba tace "ince kodai baki faɗawa Hidaya kina da CO ba, jiya Sam mantawa na yi bamuyi Maganar ba, na ce karki faɗa mata"
Fuskar Hafsa ta tuna ƙarara bata son batun CO ɗin murya aɗan dashe ta ce "ai bama maganar result da ita, nata ma gunki naji" ajiyar zuciya Momy ta yi.
"Yawwa kinga wai Usman ne ya ɗauki su Khalil ya mayar gida shine nake so ki je ki dawo da su,"
"Towo shima dai yaya Usman, yaran da bashi ke kula da su ba,"
Kwafa Mum ta yi basshi zai zo ya samen maza jeki ki dawo dasu"
Hafsa bata ce komai ba ta miƙe kasancewar ta kullum a kintse yasata mayafi kawai ta zara ta yo farfajiya inda suka ci karo da Abba." Yawwa Hajiya Hansatu ai gwanda ki cire damuwar haka ki yi walwalar ki, ina zaki haka"
"Gidan yaya Farida zani wai yaya Usman ya maida su Khalil shine tace azo a ɗauko su"
Murmushi Abba ya yi irin nasu na manya "ho Usman sarkin rikici, ai ya kyau ta da mayar musu da yaran su, muje ciki ya faɗa"
Binsa a baya Hafsa ta yi tana murmushi dan sam bata son zuwa gidan Aunty Farida a tsukun nan tasan damun ta zata yi kan course din da ta fadi. Momy naganin sun shigo tare ta tsuke fuska, "ya kika dawo kuma?"
"Abba ne ya ce ba inda zata tunda an maida su sai ki bari wani hutun in sun ra'ayi sa kawo miki, kayan su kuma in Usman din ya dawo ya kai musu" sin sin Hafsa ta shige ɗaki Mum ta hau faɗa Haba Abban Farida kana fa ji nace na ɗauko su kenan" murmushi ya yi tunda dai ya riga ya mayar su shikenan bacin haka ke waye ya ɗauke miki naki yaran ki bar musu yaran su wurin su yadda zasu shaƙu da abinsu.
Kwafa ta yi tare da miƙewa tabar wurin, shi Usman ɗin zaizo ya samen ne"
Da ɗan ɗaga Murya Abba yace "haba rabin ran ko kin manta da ɗan tsohon naki ne ya mayar miki da su ba, abin cin nawa fa"
Juyawa ta yi zuwa dining area ta haɗo abincin ta aje masa ta juya zata tafi, Haba masoyiwa ki zauna abincin zaifi daɗi badai Usman bane zan miki maganin sa"
Murmushi ta yi ta dawo ta zauna tare da ɗora motar ta, ya yi murmushi ya hau cin abincin sa.
*******
Tunda sukai batun koyawa Hafsan ya kasa tsaida shawara gashi gobe lahadi, sam baya son tunanin da zuciyar sa take kan yarinyar, yana son kuɗin da za'a biya shi yana son koyawa Hafsan sai dai take taken zuciyar sa yasa yake tsoron tusa kansa kusa da ita yana tsoron kamuwa da son ta, a hankali ya fito tsakar gidan su ajiyar zuciya ya yi, yasani yarinyar talaka ma ba lallai ta so shi ba, bare irin su Hafsa, yanzu sa ace tana son ka, kai zaka iya riƙe ta? Tambayar da zuciyar sa ta masa kenan.
Fitowar da ya yi a ƙofar gida ya zauna yau sam baya son zuwa wurin su Salisu baya son damun sa da suke batun budurwa, Juwairiyya da ya hanga ɗauke da kula ne ya sa shi miƙewa ya ƙarasa inda take "kawo ya ce"
"Akwai wata can yau Hajara kanta ke ciwo nace ta bari in kawo sai in zo in ɗauki ɗayar ta jirani"
"Ok kar ki bar gidan ba kowa bari in ƙarasa gangaren"
"tom" kawai ta ce ta yi gida shi kuma ya ƙarasa daga ɗan nesa ya hangi Hajara sanye da Uniform zaune kan tebur gaban ta kuma kula ce, take zuciyar sa ta ce mai kake jira dubu ashirin fa ba wasa bace, kana buƙatar samun kuɗi da yawa ko dan ƙannen ka su daina zuwa cikin maza haka suna yini.
Jiki a saluɓe ya ƙarasa wurin, Garba ne ya riga shi ƙarasowa tare da ɗaukan kular ta shi muje ya ce ta miƙe dakyar sai dai ganin Muktar ɗin yasa taja ta tsaya fuskar ta cike da tsoro cikin rawar murya ta ce "wallahi yaya bani na kira shi, kawai ganin sa nayi"
Muktar bai ce komai ba ya ƙarasa tare da sa hannu ya amshi kular, ya kan naki ya ce a nutse lokacin da ya ɗan kalli gefen da take. A hankali ta ce a Alhamdulillah har suka zo gida ba wanda ya yi magana a tsakar gida ya dire kular ya zari buta dan yin alwalar magariba.