← Book details Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shayin ya sake kalla wanda shine abincin sa a kwanakin nan ya daga kofin ya shanye. Salam yaji shi kamar yadda rayuwarsa yaji tayi salam. Agogo ya kalla yaga lokaci sannan ya mike yana nemo wayarsa inda ya ga sako ya shigo tun tuni bai duba ba.

A nutse ya buɗe wayar idanun sa suka faɗa kan saƙon Hafsa da ke yawo kan screen,Sai da ya ji zuciyarsa tayi wani irin dokawa a kirjinsa kafin ya zura wayar a aljihu ya tafi aiki.

A hanya zuciyar sa fal take da tunanin saƙon yayin da can ƙasan ransa ke cike da farin cikin me ya karanta kalaman sun masa daɗi...

*******

A nutse Tariq yake sakkowa daga saman sa yana ɗaura agogo ya yi kyau sosai idanun sa ƙyar bisa Bilkisu da ta rafka tagumi idanun ta kan TV duk sai yaji nutauwar sa ta masa ƙaura da sauri ya ƙaraso wurin yaɗan lafota jikin sa bayan ya zauna, cikin murya ta mai son kuka ya ke magana "wai dan Allah Habibty mai ke damun ki?, Karfa kisa hawan jini ya kama ni, da mai kike so inji da tunanin damuwar ki ko da tawa damuwar na abar sona ɗaya dana bawa raina bata yadda dani, ba zata iya daɗan damurta ba?"

Ƙara lafewa ta yi jikin sa, cikin muryar shagwaɓa tamkar wata ƙaramar yarin ya tace haba Zaujey wai kaima cikin damuwa kake?" Ɗan ture ta ya yi na wasa "kema kinfi kowa sanin cikin damuwa nake, kalli yadda na rame fa"

Tsai ta kalle shi da gaske ya ɗan faɗa, a hankali ta kamo hannun sa, ka daina damuwa ba kai bane kasani damuwa tunanin halin da Hafsa ke ciki nake nasan halin ta inta sawa zuciyar ta abu, ni kuma ba iya zuwa zan kullum ba dan lallashin ta" kaf ya maida hankalinsa kan Matar tasa, yasan Hafsa. Nada matsala tun randa tazo da sassafe sai dai shi ba gwanin tambaya bane, yayin da ita kuma Bikiisun ba gwanar bashi labarin sirrin wasu bace.

A hankali cikin kasalalliyar murya mai cike da takaici Bilkisun ta ce "Muktar ya saki Hafsa"

Wani abune da baisan mene ba ya ziyarci ransa, A ruɗe Tariq yace what Saki kuma anya Habibty ba Mafarki kikai ba ya faɗa a ruɗe.

Girgiza kai ta yi "wallahi ba mafarki bane ya sake ta" ta kuma jaddada abinda ta ce

Cikin tashin hankali yake fadin "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, saki fa, yaushe Muktar ya fara shaye shaye, waye ya faɗa masa har yanzu muna zamanin da ake saki, ya kuwa san me yake anya?..."

Yadda taga ya zage yana ta banbamin masifa kan sakin sai ya kwantar mata da hankali, Tariq ɗin da ke gaban ta yanzu bai mata kama da mutumin da zai iya banzatar da ita ya sake sakin wulaƙanci irin na Hafsa ba maras dalili.

Sun jima suna tattauna kafij ya ce ta je ta shiryo kar su makara, dan yaga yau ba zata iya tuƙin ba, miƙewa ta yi zuwa ɗakin ta kasancewar tayi wanka kaya kawai tasa suka bar falon a farfajiya ma shi ya buɗe mata gaban mota suka wuce.

A Faculty of Agriculture ya faka motar inda take PHD ɗin ta, kamar ko yaushe da hanzari ya fito tamkar wani driver ya buɗe mata Madam mun ƙaraso ya faɗa yana murmushi, tare da miƙo mata hannu, shamiƙe hannun ta tayi " kai dai baka girma wallahi kwanan fa zaka fara surukai matsa ni in fito," Dariya yasa " ni ina ruwana da surukai, in dai ina tare da ƴar yawalwalar matata to tsufa bani ganin sa."

Girgiza kai ta yi "tom sai na dawo," ta faɗa tare da yin gaba cikin ƴar muryar so da ya saba mata yace nifa ba'a sallamen ba, juyowa ta yi tana murmushi tasan me yake nufi, aikuwa sai dai ka kwan anan ta yi faba ko me ta tuna sai ta juyo " na manta in na fito da wuri zani gidan su Hafsa," ta faɗa kawai ta yo gaba.

Murmushi yasa yabar wurin yasan Halin Abarsa in zai ɗige a wurin ba zata masa kiss a public waje ba, sai da ya ja motar sannan tunanin Hafsa da mutuwar auren ya dawo masa rai.

Wurin biyu Bilkisu ta isa gidan su Hafsa Mum bata nan, dama bata yi tsammanin ganin ta ba, tasan Mum da neman kuɗi, yaran duk sunyi jigum jigum a falo da alamu lokacin suka dawo daga boko, Aiman na ganin ta ya hau murma, cike da girmamawa suka gaishe ta, "lafiya Faruk ina Maman naku" ta tambaya.

"Anutse ya ce tana ɗaki tace kar mu dame tane" shiru Bilkisu ta yi kafin tace kunci abinci ne?"

Abdallah ne wannan karan ya yi magana, "a'a Mamin muke jira ta dafa, jiya Mum tace kar mu sake mu shiga kitchen mu haɗa mata gobara in Mami ba zata dafa mu ƙarata..." Ko mai ya tuna sai ya yi shiru.

Ajiyar zuciya Bilkisu ta yi tare da yin ɗakin Hafsan, wadda ke kwance tana kallon sunan Muktar da message ɗin da ta tura masa jiya, gashi dai alamu sun nuna ya gani anma reply yaƙi shigowa.

Jin alamun an shigo ɗakin yasa ta ɗago a fusace wai "Abdallah dan Allah mai kake so dani ne?, Nace ka kyale ni bana jin daɗi.....

**********

Cike da ɓacin rai Bilkisu takara cikin ɗakin tana faɗin " to ba shi bane haba Hafsa ina kike son kai hankalin ki, anya kuwa, akan namini kike son kassara kanki da kuma rayuwar yaranki?"

"Please Bilkisu...."

Ɗaga mata hannu Hafsa ta yi tare da dakatar da ita, "karki faɗa min komai dan ba zan fahince ki ba, bawai dan ni ban shiga yanayin da kike ciki ba, a'a sai dan kin fara ƙoƙarin fita hayyacin ki da sunan so, haba ke bama zakiyi tunani ba, ai saki ba kanki farau ba, ko shi Muktar ɗin kika kalla ya dace ki gane cewa zaki iya rayuwa ba shi yadda ya rufe idanu ya nuna ba zai rayu da ke ba, ko wannan kika kalla kyama kanki faɗa kema ki nuna masa bashi da gurbi a rayuwar ki"

Cikin kuka Hafsa ke magana " Wallahi Bikisu ba zan iya ba, ina son sa kema kin sani..."

Tsaki Bilkisu taja tare da takawa inda Hafsan ta ke ta, gefen gadon ta zauna tare sa kamo hannun Hafsan ranta cike da Haushin Hafsan itakam ta rasa wannan wanne irin rashin tawakkali ne, ba kuma tasan lokacin da aminiyar tata ta koma haka ba, " Dan girman Allah Hafsa ki daure ki buɗe idanun ki, ki kalli rayuwa ko dan yaranki, ki bar su, suji da damuwar rabuwa da kukai ba sai kin ƙara musu wani tashin hankalin ba, ina tabbatar miki wannan abin da kike shin zai ƙara ingiza damuwar su"

Shiru Hafsa ta yi tamkar da gaske tana ɗaukan shawarar Bilkisun sai dai a ranta mita take na dan dai ba ita Bilkisun Tariq ya saka ba, shi yasa take kuri sa cika baki.

Ganin tamkar ta ji maganar ta yasa Bilkisu sakin Hannun ta tare da cewa ni dama zuwa nayi in ce miki an buɗe portal za'a fara registration na post graduate dan ki ɗebewa kanki kewa gwanda ki nemi MS ne kizo kiyi fitar zata sama miki sukuni arai.

Cike da damuwa Hafsa tace "Masters kuma, ni yanzu na yi applying wani abu nan kusa, kar sanadin Haka yasa Muktar ko yayi niyar mayar dani ya fasa, kinsan sabida shi naƙi ci gaba da karatun na kuw ƙi neman aiki"

Wani ƙulu ƙulun takaici ne yazo wuyan Bilkisu ya tsaya tsaki taja mai karfi tare da miƙewa ta harari Hafsa ta yi waje kawai, ba tare da juyowa dan sauraron kiran me Hafsan ke mata ba"

A falo ta tarar da yaran suna kallo, kamar yadda tazo sun takure da alamu ma ba fahintar kallon sike ba, ta kuma jan ɗan karamin tsaki tausayin yaran ya cikata, sai dai mahaifiyar su ta mance da su, Faruk ne yace "Ummi har kin fito"

Murmushi ta yi "eh na fito, nabar su Jawahir su kaɗai," Aiman ya taso da gudu ni zan biki gaskiya, batai musu ba ta ce Abbadallah ya ɗebo masa kayan sa.

Amsar kayan ta yi, tare da riƙewa yaron hannu sukai farfajiya.

Hafsa bata shirya amsar gaskiya ba, ta zaɓi son zuciyar ta, fiye da zahirin rayuwa, ko Tariq Bilkisu bata kira ba dan yazo ɗaukan ta, titi ta nufa dan bata son ma Hafsan ta fito su tattanka, yadda take jin Haushin ta tas zasu yi rikici.

A ƙofar gate din gidan ta aka ajiye ta, bugu guda Mai gadi ya buɗe, kan ta shiga Aiman ya faɗa gidan da gudu Mai gadi yahau yi mata sannu da zuwa.

"Aunty Jawahir nine fa nazo" Aiman ya faɗa lokacin da ya shiga falon da gudu yana murna, Jawahir da ke faman danna waya ta miƙe tana dariya, Darling A welcome" ta faɗa tana ware hannu ya faɗa jikin ta suna dariya.

Walida ce ta harare su, kun cikani da ihu, ta faɗa da salon wasa, Aiman ya kalle ta lah ashe Aunty Walida kina nan shima da tsokanar, kuma harar sa ta yi, "to da ina zani Aimanu?" Turo baki ya yi ni ba sunana Aimanu ba ko yaya Jawahir.

Murmushi Jawahir ta yi kyale ta Darling A, wai dan kafi sona take kishin, gyaɗa kai ya yi irin ta yarin ta yana Murmushi.

********

Suna zaune baka jin sautin komai sai na Tv da fanka, Kursum ta dubi yayin nata "ni gaskiya nima ku kaimi gidan Ummi, mai yasa baku kirani na lokacin da zata tafi da Aiman."

Harar ta kawai Abdallah ya yi in da shi kuma Faruk ya ce "sai ki tashi ki bita ai, karki kuma mun magana" sanin halin duk su biyun yasa yarinyar sunkuyar da kanta zuwa abinda take kan tayi maganar tana murmushi.
Chapter 39 · 0% Book details