Sashe 14
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ohhh.. I’m so sorry.” Su dukka suka furta a tare suna nuna rashin jin dadinsu a fuskarsu sannan suka kalle ta. A take Hafsah taji tausayin yarinyar ya cika ta har sai da tayi kwalla. Da kyar ta kalle ta again tace. “Hi.”
Suna kallo Hajiya Deena ta kama hannun yarta. “Go with them habibty.” Da haka suka kama hannunta suka fita daga falon jikinsu yayi sanyi sosai. Har suka isa daki ba wanda ya sake magana inda suke ta tunanin ta inda zasu soma yi mata hira.
“Hi, sunana Asma AbdoulJalal. I was born blind. Ban san meye kala ba. And I’m happy.” Hafsah bata san sanda ta rungume ta ba sannan ta runtse nata idanuwan. Duhun da ya mamayeta ya saka ta fara hawaye. She couldn’t imagine life a makance. Bata san ta inda zata soma ba.
“Kowa sai ya dinga jin tausayi na, saboda ban san kalar komai ba. Not even Mamma.” Ta fada sadly amma da murmushi a fuskarta.
Duk sai suka zama bebaye suka kasa magana.
“Amma all the same, the world ia equally beautiful. Komai sai dai nayi imagining. The only thing i am missing is colors. Duhu kawai na sani so komai a duhu nake ganinsa. A duhu nake tunanin sa. Ance I’m beautiful haka ne?”
Da ido suke ta binta tana basu mamaki. Yadda take ta surutu freely. Su kuwa sai faman goge hawayen su suke. Cike da karfin hali Hafsah ta amsa mata.
“Kina da kyau. Ba kadan ba. Kina da mugun kyau. I don’t know how to describe it for you.”
Shiru Asma tayi wanda ya bawa Hafsah daman tashi ta tafi bandaki tana kukan rashin godewa Allah akan dukkan ni’imomin da ya mata. Rashin kula cewa idon ta da ya bar mata ma wata babbar kyauta ce da rahama sa a gareta….
"Aifa dole kaya su dinga koɗewa, haba ace sawa ɗaya sai an wanke kaya, su kaya ba wani na azo a gani ba" Inna da ta fito daga ɗaki riƙe da ɗan likidiri ta ce da Muktar wanda ke ta faman cuɗa kaya, ɗagowa ya yi yana murmushi daga sunkuyen wankin, "ai Inna kayan ne sam basa mun daɗi in nasu su da ɗauka ko yaya maiƙon jikina ya taɓa kayan na fiso kan in kuma sawa in wanke"
Murmushi inna ta yi, "ai iyawa ne bakai ba, in ka dawo ka cire kayan sai ka baza su a inuwa su sha iska kafin ka mayar adaka"
Murmushi ya yi ba tare da yace komai ba, inna tasan halin abin ta, tunda ya yi murmushin nan cewa bazai yi bane kawai ba zai ba anma bazai yi yadda ta ce ɗin ba, kwafa ta yi "ai shikenan kayan ka" ta faɗa kafin ta yi zaure har ta kai ta tsaya ni na shiga gidan Harira in ka gama kan kaje in da zaka ka daure ka shigo ka duba Malam ɗazu Fiddausi da ta shigo siyan taliya take cemun jinin nasa ya yi tsanani"
"Tom shikenan a masa sannu kanin zo" Inna bata ce komai ba ta fice daga gidan tabarshi yana shanya.
Sai da ya gama komai sannan ya fito, yana ƙoƙarin ɗaure ƙofar gidan da wayar kebir yaji muryar juwairiyya na faɗin yaya kar ka kulle, sakin ƙofar ya yi tare da juyawa Juwairiyyar ya gani ɗauke da katuwar Kula tare da Hajara wadda ke sanye da uniform ɗauke itama da ƙatuwar kular kamar kullum in ta taso saga makaranta sai ta fara zuwa ta ɗauko kula inda Juwairiyya ko Ummi ke zama da abinci kafim ta tawo gida, bai ce musu komai ba ya tsallaka kwatar da ta raba tsakiyar layin nasu ya shiga gidan su Harira da sallamar sa.
daga zaure suka haɗa ido da Bahayura wadda ke gefen tabarmar da su Inna ke kai tana gurza kuɓewa murmushi ta sakar masa, lah yaya shigo mana ta faɗa lokacin da ta jawo turmi miƙo masa ta yi zauna daga bakin zauren ya zauna dan tsakar gidan ya tushe, a nutse ya gaida su ya musu ya mai jiki kafin Bahayura ta gai she da shi, "yaya ya aikin?, Jiya nazo ai baka nan"
"Aiki Alhamdulillah, eh jiya naje lesson da nakewa yara da na dawo na biya ta majalisar mu sai dare na shiga gida"
" Haba nifa in ce har gidan su Yaya Salisu naje bakanan"
Murmushi ya yi " towo Allah yasa ba bashin ki naci na manta da shi ba" sai da kowa ya yi dariya kafin Umman su Bahayuran ta ce " ai ko bashin ne ta ƙyaleka ka sarara.
Aje kuɓewar ta yi kafin ta miƙe ta mika hannu saman kusa da jakun kunan su ke rataye daga ɗan inda rufi ya zubo, takardu ta ciro " ka gani Badawi ne ya kawo min tana nufin saurayin ta wai form ne na school of hygiene, ya sai mun to daga ni har shi muna tsoron mu cike ba dai dai ba" cike da annashuwa ya amsa " amma Badawi ba ƙaramin kyautawa ya yi ba gaskiya miko biro in cike miki yanzu in ya so ko gobe sai in miƙa miki in jiyo mai da me zakuyi."
"Anma yaya da ka kyautamin walllahi don ni yace in kai da kaina gashi na kashe kuɗin motar da yaban."
Tsaf ya cike mata kafin ya mike "bari in leƙa in gaida malam ɗin," sosai ya tausayawa yadda Malam ke jin jiki, a kasalance ya bar gidan kasancewar yau lahadi ranar da suke ɗaukan karatu yasa da ya fito daga gidan littattafan sa ya ɗauka kafin ya wuce masallaci.
Ko da ya dawo dakyar ya samu bacci ya yi awon gaba da shi sabida tunane tunane haka kawai ya rasa mai yasa da ya zauna sai Hafsa da ƴar hirar rakin su mara tsayi ke dawo masa wani zubin takaicin kan sa ya kamashi wani zubun ya saki murmushi, bai san mai yake ji kan yarinyar ba kuma zai iya cewa maine ba yasan dai ba sabo bane ba kuma so bane cikin tunanin da son gano mai ne ya samu bacci ya yi gaba dashi.
Washe gari da wur wuri kamar kulluum ya shirya bayan ya cika gidan da ruwa, fitowar da ya yi daga kama ruwa ya tarar an zuba masa abincin karin sa yau a langane har ya ɗauka ba tare da dubawa sai kuma ya buɗe kosai da faanke ne, "an gama toya wainar nan kuwa?" ya tamaba.
Umma ta ce "towo yau kai ke tambayar waina ina kafison fanke?" Murmushi yayi abokin aikina ne rannan da kika zubamin yaji daɗin ta shine nace bari yau in kai masa.
"Hajara ɗibar masa a ta gidan Malam Hassan in ya so sai ki zuba musu wata" Inna ta faɗa da ɗan ƙarfi.
"Ta ɗari biyu zaki zuba" shima ya faɗa
Koda ta miƙo msa amsa ya yi ya sa a langar da ke hannun sa kafin ya zaro ɗari biyun ya miƙa mata, juyawa ta yi ta ce da Inna " kinga ya bada kuɗin"
Da hanzari inna ta ce " wanne kuɗi bashi abinsa kaji ka mene dan an baka ta ɗari biyu ka bawa wani?" "A'a inna abin fa siyarwa ne, sai na dawo" ya faɗa tare da saka kai ya fice ba tare da ya amshi kuɗin ba.
******
Yau tana tashi ta hau zuba kayan ta a ƴar ƙaramar akwatun ta, itakam wannan hutun semester ɗin ba zata iya yin sa guri guda ba takaicin first papar ɗin su sai ya ishe ta sai da ta ɗebi duk abinda tasan zata buƙata kafim ta shiga wanka tsaf ta shirya kafin shida ta kammala komai ta fito riƙe da jakar ta sam batayi niyar faɗawa Momy zata wani gurin ba, tafi so sai taje ta bugo mata waya wannan yasa take so kafin Mom ɗim ta fito falo takai kayan cikin but ɗin mota.
Cak ta tsaya lokacin da taji Muryar Mum ɗin "ke Hafsa ina zaki da wannan fagon kayan?," Daurewa ta yi tare da tattara kwarin gwiwar ta guri guda kafin ta jiyo fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarya " Momy yanzu nake son in kai kayan sai in zo in fada miki daga Flourish gidan Gwaggo zan dinga wucewa acan zan hutun"
"Ba inda zaki da wannan damunar zaki tafi wannan gidan ga uban sauro da raɓa"
"Allah Mum ba raɓa, sauron ma ni ba jin sa nake ba" Hafsa ta fada a shagwaɓe.
"Nadai faɗa miki ba in da zaki, kin san ba iya aikin gidan nan zan ba ni kaɗai in kin tafi"
"Please Mum ki tallafa ki barni in tafi, walllahi ina missing ɗin gwaggo"
Harar ta Mum ta yi bayan ta zauna " ai kin san dai duk yadda kike missing din su ba kamar ni da suka haifa ba, ba inda zaki"
Abba da ya fito ne ya ce "Hajiya Hansatu kai kayan ki mota" cike da murna ta fice sannan ya juyo kan Mum wai dan Allah Hadiza mai ke damun ki ne, kibar yara suyi zumunci mene ciki dan taje tayi sati biyu.
Yatsina fuska Mum ta yi " ni karka min sharri Abban Farida ina ga satin da ya wuce taje gidan, ni bance kar taje ba kwana ne, uban sauron da ke gidan nan taje zazzaɓi ya rufe ta kadai san dai Hafsa ba lafiya ta cika ba."
Dariya Abba ya yi " kema dai kinsan duk yadda Gwaggo zatai ba zata bari sauro ko wani abin ya cutar da Hafsa ba ki kyale ta taje" shiru kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Kalil ne ya fito yana sosa ido hango Abba da ya yi ne yasa shi rugowa da gudu yana murna Abba ya rungume shi "a'a Khalilullahi an tashi?" Gyaɗa kai ya yi " Good morning Abba, ta shi na yi da wuri Aunty Hafsa ta ce in ban tashi da kaina ba yau ba zata bani cake ba"
Dariya Abba ya yi "Morning my boy, wato kwadayi ya tashe ka kawai maza jeka ta shirya ka, kuyi sauri kar mu makara"