← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 47

Sashe 9

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..........“Ku fara da gaskiyar Ojo. Akwai wani abu da bai dace ba. Kuma akwai hannaye da yawa da suka fi mu ƙarfi har a cikin gida. Sai dai fuska biyun su tasa sun zame mana masu lulluɓin biri”.
    Shiru ya cika ɗakin. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Imran. Cikin kasa haƙuri ya furta, “Idan kuwa har akwai masu fuska biyu zan kasance mai tsoro da shakkar mu'amulantar kowa?”.
       “Wannan shine gaskiyar magana, amma a ciki akwai ɗaya tamkar da dubu. General Yusuf Shu'aibu Tafida. Col. Haydar Galadima (Faro), Brigadier General Abraham Yohana, yaranmu Dabo, Yusuf. Amma saura duk ka ajiye kowa. Akwai saƙo a ɗakina na ajiye maka, idan ka haɗa da wannan zai baka abinda nake buƙatar ka fahimta. Dan na tabbatar daga yau bazasu sake barinka ka ganni ba.”
     Da ƙyar Imran ya iya furta, “Janar ya shiga SIYASA...”
         Cak numfashin Zak-Shadow ya tsaya, hakama bugun zuciyarsa kafin su dawo a tare. “SIYASA?!”. Ya furta yana tsatstsare Imran da idanu.
      Kai tsaye Imran ya jinjina masa kai. Sai kawai Dada yayi murmurshi tare da wani ɗan lumshe idanu sannan ya sake buɗesu luuu akan Imran. “Na amince kayi aiki da shi Imran....”
     Cikin tsatstsareshi da idanun shima Imran ya ce, “Zak… kana nufin kaci karo da mutanen da kowa yaji tsoron ɗaga su?”.
     Wani ƙaramin murmushi mai zafi, mai ɗaci ya bayyana a gefen labban Dada. “Ni ba wanda nake tsoro, Imran. Amma gaskiya… ita ce abin da suka hana ni gani tsawon shekaru uku. Ni kaina kuma na yarda da hasashen General, ta irin hanyar da suke kai, kawai zamu bi mu gano su, mu kuma yaƙe su” ya ɗanyi shiru na sakan biyu. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Yau na baka wannan rubutun. Ka tafi da shi. Kada ka bari kowa ya gani a yanzu har Janar. Dan kai kaɗai nake son kayi waɗan nan binciken”
      Idanu kawai Imran ya kafeshi da su ya ma kasa magana. Wato idan Zak.. ɗinsa na wani abu a wasu lokutan yakan ga tamkar mai aljanu ko mai gani har hanji da yara kan faɗa. Kai har ɗan duba ma zai iya kiransa, amma yasan duk ba haka bane, tsabar kaifin basira ne kawai da iya sanin kan duniya da mutanen cikinta da ALLAH ya bashi.
    Shi ko Dada ganin kallon da Imran ɗin ke masa, sai kawai ya jingina da kujera a hankali ya lumshe idanunsa. A haka ya ce, “Ban san miya baka mamaki ba ka tsaya kana kallona bayan lokacin ka ƙayyadadde ne. Idan rana ta yi zaka gane me yasa naga mutuwa ta fi wannan shari’ar sauƙi.”
    Imran ya kasa magana yanzun ma, a haka har lokaci ya ƙare, masu tsaronsa suka buga ƙofa. Miƙewa kawai Dada yayi zai bar gurin, sai kuma ya tsaya ya kalle shi for the last time yasan kafin a sake ganin juna sai bayan shekaru. Dada ya lumshe ido tare da furta masa a hankali kamar sirrin da baya buƙatar iska ta ɗauka zuwa gaba a tsakanin su.
      “Ka zama hasken da nake bukata a waje. Ka cigaba da zama UBA kuma nagartaccen MIJI a cikin GIDA”. Daga haka yay gaba batare da ko waiwayen Imran ba. Shi ko Imran ya kasa motsi sai kai-kawo furucin ƙarshe na Zak-Shadow ɗin ke masa amsa kuwwa a cikin kai, dan magana ce a dunƙule ya bashi kuma mai ƙarfi.....

   (((★)))(((★)))(((★)))
         ★ 2021..... ★

       Duk wanda yasan gidan a shekarun baya takwas da suka shuɗe yanzu idan ya zo ba lallai ya gane ba. Domin kuwa gidan nan da Mammah da yaranta tara mai sassa biyu kacal a yanzu ya zama mai sassa da yawa sakamakon iyalanta da suka ƙara yawa. Kamar yanda Dada ya barma Imran wasiyyar dawo da ginin su Ma'aruff a cikin gida a wacan lokacin hakan ta tabbata, duk da kuwa shima Imran ɗin dole ya bar ragamar a hannun Uncle Nasiru sakamakon prison ɗin daya shiga na shekara uku.
     Duk da suna cikin ɗacin yanayi Uncle Nasiru yayi abinda ya dace harda kuɗin aljihunsa. Anyi bikin Ma'aruff da Ja'afar da amarensu Shariffa da Lailah, sai dai bikin baiyi armashi ba sakamon jarabawar da wannan ahali suke ciki a wancan lokaci na rasa jigon gidan da suke ma kallon Uba bawai yaya kawai ba. Amare sun tare a gidan Mammah kowace da ɓangarenta, kuma Alhamdullah dukansu masu tarbiyya ne da suka fito daga gidan tarbiyya. Dan kuwa akwai abubuwa da yawan gaske da suka bambanta su da surukar gidan ta farko Nabeeha.
Received at 4:11 PM
[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 7

.......Cikin matuƙar bala'i da ihu matar ta ce, “Babbar bala'i kai, wlhy bazan yarda ba, dolene ma yaran nan suje police station dan sai nayi shari'a da su.....”
     Da sauri matashin malamin nan ya katseta da faɗin, “A'a ranki ya daɗe kada ai haka. Mudai bari a zauna dasu aji miya haɗasu, duk da nasan Naja'atu da Ruƙayya fitinannun yara ne amma basa faɗa sai da dalili...”
         “Oh yanzu na fahimta, to kodai kaine ka sakasu su aikata ma saboda kana nemansu? Dan ba abin mamaki bane idan muka dubi yanda malamai suka koma fasiƙanci da ɗalibansu a makarantu”.
      “Innalillahi wa'ina ilaihiraji'un, Hajiya wane irin magana ce wannan? Dan na faɗi abinda yake gaskiya kuma sai ki aibantani da yaran da suke tamkar ƴaƴanki. Amma dai.....”
       “Teacher Khalil ya isa haka. Ka fahimta kawai ranta ne ya ɓaci. Yanzu dai ka kira gidan su yaran sannan azo min da su nan yanzu nan”.
     Sosai ran wanda aka kira da Teacher Khalil yake a ɓace da zancen matar, sai dai bai sake cewa komai ba ransa na ƙuna ya shiga neman layin wanda yasan Yaya ne gasu Ruƙayya, amma fin kira goma bai shiga ba. Ganin ba samu zaiba principal yace ya sake kiran wata number mana, canja kiran yay zuwa ɗayar number da yake da ita, cikin sa'a kuwa ta shiga. Koda aka ɗaga cikin nutsuwarsa yay bayanin daya dace, a ƙarshe ya sanar da ana buƙatar ganin wani nasu babba daga haka ya ajiye wayar ya fita a office ɗin....

Mintina kaɗan Teacher Khalil ya dawo, sai da ya shigo sosai matasan ƴammata biyu suka bayyana. Ta gaba fara ce tas kuma ƙyaƙyawa, siririya daga ganin fuskata kasan zatai rashin ji. Wadda ke biye da ita ma da zasu iya zama kai ɗaya black beauty ce masha ALLAH, itama dai daga ganin fuskar nan kasan zatai tsiwa. Su duka sanye suke da uniform skirt peach color da farar riga long sleeve shirt, sunyi zanzaro da skirt ɗin, sai ɗan ƙaramin baby hijjaf fari shima da iyakarsa matashin ƙirjinsu da ake kiran kamar su da suna ƙwailoli. Daga ƙasa safa ce doguwa data zo har gwiwar ƙafa saboda skirt ɗin nasu kaɗan ya zartar gwiwar sai takalman sandal baƙaƙe na ƴan makarnta. Ga shi dai uniform ne ana saka shi badan ado ba, amma yayi musu matuƙar ƙyau da zaunawa a madaidaicin jikinsu ɗas kamar ka lashesu. Ga wani ƙamshin turare mai sanyin daɗi na fita a jikin nasu da gogaggun uniform ɗin su da suka sha karin guga kamar batun safe suka sakasu ba.
     A makarantar ba'a dukan ɗalibai sam, dan makaranta ce ta kuɗi kuma ta ƴaƴan manyan ƙasa. Duk wanda aka gani a school ɗin lallai ubansa yaci ya ƙoshi ne. Shiyyasa daga ƴaƴan masu mulki saina jami'an gwamnati dana manyan ƴan kasuwa. Dan makarantar ma ta baƙin haure ce ƴan ƙasar waje ba ƴan ƙasa ba. Rabi da kwatar malaman cikinta duk masu jajayen kunne ne, sauran tsiraru irinsu Teacher Khalil ne kawai ƴan ƙasa baƙaƙen fata, sai kuma shi kansa principal ɗin shima dai ɗan ƙasa ne.
      Da farko idanu principal ya zuba ƙyawawan ƴammatan biyu, yayinda matar nan ke zuba musu uwar harara kamar idannunta zasu zubo. Hakama ƴarta dake lafe a jikinta tun shigowar yammatan dake sa'ointa ta sake mannema uwarta tana harararsu. Suko sun wani tamke fuskoki suna cika suna batsewa. Haɗa ido baƙar tayi da yarinyar, tako watsa mata uwar harara da nunata da yatsu biyu alamar saita tsokale idon...
     Wani irin takaici ya sake mamaye zuciyar uwar, dan ta kasa gane ita zata tsokalewa ido ko ƴar tata tunda itama hararar take. Baki ta buɗe zatai magana principal ya katseta sakamakon ambaton sunan yaran da yayi.
       “Ruƙayya Imran Abbas”.
  A cinkushe farar tace, “Yes Sir!”.
Ya sake maida idonsa ga baƙar ya ce, “Naja'atu Muhammad”.
Itama cikin tura baki tace, “Yes Sir”.
      “Ku miyasa bakwa jin magana ne, yara kamar ibilis ne malamin ku kullum cikin kawo ƙararku ake. Yanzu ku duba yanda kuka fasa mata kai, inda abin yazo da ƙaddara fa...?”
Received at 4:11 PMReactions:[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 8
Chapter 9 · 0% Book details