Sashe 42
Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Anan gidan Mammah bayan tafiyar su Nabeeha Malam Almu ya kawo ƙaninsa ciki dan su gaishe da Mammah su mata barka da dawowa. Da fara'a kuwa ta tarbe su. Tare da amsa musu gaisuwa da kulawa tana tambayar Malam Almu mai jiki. Kamar yanda yay ma malam Buba bayani itama haka yay mata duk su Yaya Ma'aruff na jinsa. Ya kuma nuna ƙaninsa Sanda ya musu bayani a kansa da aiki da ya fito nema idan ya samu. Sai dai bai nuna anan gidan ba kamar yanda suka shirya.
Cikin sa'a kuwa Mammah ta ce, “To ai bai kamata yay nesa da kai ba ko Malam Almu. Sai a bincika anan idan da wani aikin sai ya dinga yi, kaga sai kuyi zamanku ka samu abokin hirar dare tunda shi driver ba kwana yake ba yana tafiya gida da yamma”.
“Nagode Hajiya Mama, ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Sanda kayi godiya mana”.
Godiyar Sanda ya fara shima kamar yanda yaga malam Almu nayi, suka juya suna sake godiya gasu Yaya Ma'aruff suma. Sai da Mammah tace ya isa sannan sukai shiru. Daga haka ta ɗan yima Sanda tambayoyi yana bata amsa. Kai ta dinga jininawa cike da nazarin al'amarinsa, kafin ta sallamesu su koma bakin aikinsu...
Suna fita Yaya Ammar ya ce, “Mammah wai baƙya jin tsoron ɗauke-ɗauken nan kada wataran mu ɗauki abinda zai dame mu. Yanzu fa akan al'amarin Dada kowa zai iya shigowa jikinmu dan ya cutar damu. Shiyyasa kikaga ma Yaya Imran kullum yana kaffa-kaffa”.
“Hummm Ammar kenan, banda abinka bawa na iya gujema ƙaddararsa daman? Duk abinda kaga ya faru hukuncine na UBANGIJI. Jarabawa ba tawaya bace. Ba kuma faɗuwa bace ga bayi, sau tari kankarewar zunubi ce ko tsanin nasara daga wata ɗaukaka da UBANGIJI zai kai bawa kanta. Kar ku damu da makircin masu makirci, idan duk wanda ke zagaye da kai mugune mai fuska biyu, in har ka tsaida gaskiya, kai ka zauna da shi da kyakkyawar zuciya bisa umarnin ALLAH, wlhy ko shine ibilis akan sheɗanci da mugunta sai dai yayi ya barka. Dan shi bai isa canja komai daga ƙaddararka ba koda murmushi fuskarka ne, sai dai yayta wahalar banza da ɓata lokacinsa akan ka amma ko badaɗe ko ba jima saika cimma wannan nasarar. Ƙilama UBANGIJI yay masa tsahon ran da zai koma neman taimakon ka. Kudai kuyi addu'a kawai, idan ma da manufa mutum yazo mana, ALLAH zai hanashi nasarar cutar damu. Shima da yake can ALLAH zai kuɓutar da shi idan lokaci yayi, dan bana yanke ƙauna da rahamar UBANGIJI akan Muhammad zai fito ya dawo garemu. Ban taɓa jin na sare akan wannan fatan ba, duk da ina jin tsoron kar su cutar mana da shi. Amma ALLAH na tare ta shi, addu'a ta da taku na tare da shi. In sha ALLAHU indai gaskiyarsa ce ta kaisa wancan wajen komai tsahon lokaci zata ƙwatoshi daga hannun azzaluman makirai...”
“In sha ALLAHU Mammah”.
Suka faɗa a raunane, Biebah da Ammar kuwa sai da suka share hawaye. Su Ja'afar dai idanun sun canja launi amma babu hawayen. Su Nimrah dake laɓe suna sauraren su suma dai duk jikinsu yayi sanyi. Cikin Zuciya Nimrah ke jin tana son sanin inda Dadan yake? Miya faru da shi? Mi ake ɓoye musu game da shi?. A zahiri kam batace komai ba ta nufi komawa ɗakinsu, sauran duk suka bita dan dama tun shigowar maigadi Mammah tace su koma ɗaki abinsu. Shine suka laɓe, da farko dariyar shigar ƙanin Maigadi suka maƙe sukeyi, dan yayi wani shigar gayun ƙauye irin masu iyayin nan ne abin dariya......
••••••••••••••••••••••••••••••
★ONE WEEK LATER★
★10:15 AM★
SECRET MEDICAL BASE
Received at 4:37 PM “Colonel Imran… mun kammala dukkan gwaje-gwajen da muka yi masa.” Dr. Idris Ali, ya faɗa yana ɗan gyara gilashinsa.
Imran bai ce komai ba. Ɗaga masa kai yay alamar ya ci gaba.
Doctor ya jinjina kansa, kafin ya buɗe baki ya cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH jikinsa ya nuna ƙarfin juriya mai ban mamaki. Idan ba haka ba, da gubar da aka saka masa ta riga ta yi mummunan tasiri a lafiyarsa zuwa yanzu.”
Cikin wani irin bugawar kai Faro ya ɗan matsa gaba, murya ƙasa-ƙasa da alamar tashin hankali a ciki ya furta, “Guba kuma Doctor?”.
Dr. Idris ya ɗan numfasa, kamar yana neman kalmar da zai musu bayani da ita da bazata ɗaga musu hankali ba fiye da kima. “Eh. Poisoning ne… dan abinda sakamakon bincikenmu ya nuna mana kwanaki uku kenan shiyyasa ma muka sake masa sabon gwaje-gwaje akan hakan, kusan wannan dalilin ne ya hanamu faɗa muku komai a ranar wednesday data gabata mukace ku saurare mu. Sai dai ku kwantar da hankalinku poising ɗin bai jima da fara shigarsa ba, da dai ya jima a inda yake ne zai cigaba da shiga kamar yanda koma su waye suka tsara, sanan zai dinga tasiri a jikin nasa ne a hankali har sai ya gama yima jikinsa illa ne zai bayyana. Dan haka ko a yanzu babu wani damuwa mai girma. Sai dai idan aka bar shi haka a jikinsa, akwai haɗari sosai anan gaba”.
Imran da gaba ɗaya yake jin jinin jikinsa na tsiyayewa tamkar an ɓula ledar ruwa da tsinin allura ya rumtse idanu yana matse hannunsa.........✍️
Received
[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: KIƊA A RUWA 2
40
.........Gaba ɗaya ran Hajiya Hasiba a dagule yake. Koda su Nabeeha suka koma gida da nasu ɓacin ran sun sameta tana faman kai-kawo a falo. Aunty Mamawo zaune itama ta rabga tagumi. Ismat ce kawai tai ƙarfin halin tambayar su ko lafiya? Amima da Rayhana kam da ƙorafin abinda ya faru suka fara. Nabeeha dai ranta a ɓace yake, dan haka bata tankama kowa ba ta wuce upstairs abinta. Dan a wannan gaɓar ta gama yarda dole ta nemawa kanta mafita. Mafitar kuma ɗaya ce jal shine komawa gidan su Haysam. Dan a can ne kawai zata samu damar maganin wannan shegiyar mayyar yarinyar da ganinta ya gama birkita mata dukkan lissafinta, sannan ta samu mafakar gujema Adeel da bata san manufarsa ta biyosu ƙasar nan ba.
Tsakanin Aunty Mamawo da Hajiya Hasiba babu wanda ya kula tambayar Ismat, sai ma umarnin su wuce ciki da Mamawo ta basu. Hakan ya sake tabbatar musu babu lafiya. Wucewar sukai, dan sun san halinta da masifarta bata musu ta wasa. Shiyyasa ma suka fi son Hajiya Hasiba dan tafita sauƙin kai. Koda suka hauro saman ma kowa inda yafi masa ya nufa, dan kowa da abinda ke ransa da zuciyarsa. Ismat dai a wannan gaɓar ta gama yanke shawarar komawa gidan mahaifinsu. Dan tayi alƙawarin bazata sake komawa Dubai zama ba sai inda ziyara itama tare da mijinta Yaya Ja'afar in sha ALLAHU. Dan a wannan karon yaƙi zatai ɗan gaske babu gudu babu ja da baya. Ta share ƙananun hawayen da suka cika mata ido, wani irin wutar sonsa na sake ruruwa mata a zuciya, saboda ganinsa ba ƙaramin tayar mata hankali yayi ba. Ya ƙara ƙyau da cikar jiki da buɗewa irin ta magidantan dake samun dukkan gata a wajen iyalansu. Tunda yay auren nan bata yarda taga matarsa ba saboda bata buƙatar hakan, amma a yau tana jin kwaɗayin ganin Shariffa ɗin duk da ta santa dama can.
Akwatin kayan da tazo dasu daga Dubai ta buɗe, kasancewar ƙaton gaske ne dama kuma ta haɗo komai nata mai muhimmanci daga can sai ta sake tattare na nan gidan ma ta loda a ciki, ganin ya cika da yawa ta sake ɗaukar wani ƙarami ta zuba sauran abinda ya rage ta rufesu. Bakin gado takai zaune ta ɗauki wayarta ta fara kiran Aunty Jiddah. Gidanta take son fara zuwa, dan tai mata rakkiya gidan Abban.
Da mamaki Aunty Jiddah data ɗaga wayar ta ce, “Yaushe ke kuma a gari haka?”.
“Aunty mun jima da zuwa. Kina gida ne dan ALLAH?”.
“A'a ina gidan Aunty Fateema, zata aurar da ƴarta Aminatu muna shirye-shirye dan za'a fara gobe idan ALLAH ya kaimu.”
“ALLAH ya sanya alkairi, yaushe zaki koma?”.
“Amin ya rabbi. Lafiya kuwa?”.
“Aunty zan zo ne, ni dai yaushe zaki koma?”.
“Ki tafi kawai ai yara na nan, Shafa'atu ƙanwarsa ma na gidan tazo weekend”.
“Okay tom. Ki gaida Aunty Fateeman, in sha ALLAHU dani za'ai kamun gobe”.
Daga haka ta yanke wayar tabar Jiddah da mamakinta....