← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 47

Sashe 7

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

.........“Bai tare musu komai ba, gaskiyarsa da rashin tsoro yasa suka kasance su a tsoracen. Sannan an tasirantar da siyasa ne a cikin al'amarin a yanzu.”
          “Shima abinda ya gaya min kenan, da nace masa zaluncine yasa suka rufemu. Yace ba zalunci bane siyasa ce kawai”.
     “Ƙwarai da gaske maganarsa gaskiya ce, wasan ya canja daga yanda ya fara ya koma siyasa saboda an janyo hankalin wasu masu zuciyar kwaɗayi a cikinsu da kuɗi, sannan duk masu son ayi gaskiya an daƙilesu. Kaga dai sunyi duk yanda zasuyi sun hana wasu a cikin adalan shugabanin komawa tenure ɗinsu ta biyu, sun ƙalama ministoci da yawa sharrin da sai da suka bar ƙasar. Yanzu sun ɗora wanda suke so akai gashi har sun shiga shekara ta uku akan mulki, sun samu damar yin yanda suke so. Duk da lafawar hare-haren nan dakaga an samu akwai manufar da suke son cimmawa ne kawai, sannan sun sami abinda suke so wato cigaba da haƙar ma'adanai.”
        “ALLAH zai mana maganinsu Sir”.
     “In sha ALLAHU Imran, sai dai muma dolene mu tashi tsaye sannan ne zamu samu taimakon UBANGIJI. Dan tabbas in dai ba wani motsi mai girma mukai ba akwai babbar matsala da zata iya faruwa anan gaba. Ciki kuwa harda halaka Haysam dana samu tabbacin suna shirin yi.”
     Cikin matsanancin tashin hankali Imran ke kallon General. Shima sai ya jinjina masa kan nasa. “In sha ALLAHU bazasu samu dama ba. Shiyasa ma na yanke wani hukunci. Wanda ta hanyarsa ne kawai naga mafita a fitowar Haysam daga prison”.
        Imran ya ture plate ɗin abincinsa gefe, cikin bugun zuciya da rawar murya ya ce, “Sir wane irin hukunci ne wannan? Wlhy komai wahalarsa da haɗarinsa zan kasance tare dakai muyi domin kuɓutar da Haysam, dan raina fansa akan Haysam Abdul-rasheed Shehu”.
           Cikin jinjina kai da sauke ajiyar zuciya General ya ce, “In sha ALLAHU wannan abotar taku sai kunci moriyarta mai tsaho a duniya sannan ku kasance a aljanna tare. Imran a yanzu kaf hanyoyin fitar da Haysam na bisu amma duk an rufe su ta hanyar makirci da ƙarfin ikon masu mulki. Dan haka nai nazari nima da gane hanya ɗaya muma ta rage mana. Wato irin hanyar da sukabi suka rufe kaf ƙofofin muma dole ne mubi tanan mu buɗe ƙofifin. Dan tabbas Haysam shine ƙashin bayan karya waɗan nan mutanen da shirye-shiryen su. Badan wasu bazasu iya bane, badan babu kamar Haysam bane, badan babu masu irin gaskiyarsa da jarumtarsa bane. Akwaisu da yawa cikin matasan sojojinmu dama sa'anninku ɗin, kai harma wanda suka fishi duk za'a samu. Kawai Haysam shine ya fara musu illa, yay musu sani na haƙiƙa, sannan yake firgitasu da basu tsoro tunda har suka tattara duk karfinsu wajen son ganin sun danne shi. Dan haka ina son shi daya fara wannan aikin ya ƙarasa shi dan su san ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA...... Sannan da gaske shi ɗin KIƊA A RUWA NE MAI TADA HANKALIN SU. Dan haka Imran zan shiga SIYASA..”
         “SIYASA! Sir?!”.
    “Ƙwarai kuwa Imran SIYASA. Dan yanzu haka na fara shiga jikinsu, har wasu a cikinsu sun ɗorani a shawarar fitowa ɗan majalisan tarayya. Na kuma yarda na amince musu, sannan zan musu duk yanda suke so dan babbar kujerar mai gaba ɗaya nake hari nan da shekaru huɗu masu zagayowa bayan an gama tenure mai zuwa bayan wannan”.
       “Turƙashi”. Cewar Imran yana zuba tagumi da hannu biyu. Murmurshi Genaral yayi mai faɗi, cike da dattako ya ce, “Yaƙin namu ne mu duka. Wannan shine hikimata ta cewa kada ka ajiye aikinka. Dan a yanzu haka kaima suna shirye-shiryen ƙara maka girma. Acewarsu zasu fara jan ra'ayinka dan zafafa zuciyar Haysam da ɗarsa masa cewar baka tare da shi. Su kuma samu sirrikansa....”
      “ALLAH ya kiyaye, bana buƙatar ƙarin girmansu....”
    Ƙaramar dariya Genaral yayi, cikin katse Imran ya ce, “Kwantar min da hankalinka mazan fama. A yanzu da bamu da zaɓin daya wuce maida kammu sakarkaru. Ta haka ne kawai zamu kamo bakin zaren, mu kuma tantance su waye ainahin munafukan. Su waye masu gaskiyar? Sannan mu cimma burin mu kuma. Amma na baka dama kaje kai tunani mai zurfi. Sannan zan sake shiga da fita dan ka sake ganawa da Haysam a karo na biyu, ka nema shawara a wajensa kuma. Imran idan wani zai iya gane zuciyar Haysam daga cikin duhun prison, kai ne. Ka koma. This time, ka saurare shi da idon zuciya, ka kuma gaya masa shirin mu da manufar mu. Na tabbatar zai bamu goyon baya shima.”

     Wannan maganar ta General Yusuf ita ta kulle ma Imran baki tun jiya. Haka kuma ya cigaba da yawo da ita tsakanin safiya zuwa marece na kowane rana. Har ALLAH yasa a karo na biyu ya sake samun damar ziyartar Zak-Shadow a karo na biyu bisa tsayawar Janar ɗin......

<<•>><<•>>•<<>>
       A PRISON GATE...
Chapter 7 · 0% Book details