Sashe 11
Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yau ta kasance juma'a, dan haka an tashesu da wuri. Sai dai shiru babu drivern su babu alamarsa. Sun san maybe ya fara zuwa ɗaukar su Abees kafin yazo nan, duk da kuwa a kulum su yake fara zuwa ya ɗauka kafin su ƙarasa makarantar su Abees ɗin saboda suna rigansu tashi. Tun suna kallon agogo har suka sare, ga mafi yawan ɗalibai duk sun wuce anzo an ɗaukesu. Makarantar su nada doka kuma ma tilas zuwa ake ɗaukar kowane ɗalibi bawai buɗe musu gate ake su fito ba kawai.
Sun gaji ga Ruky na ciwon mara, dan ita in zatai period ba ƙaramin jikata take ba. Ganin ta fara kuka hankalin Nimrah ya tashi. Ofishin Principal ta nufa amma ta tasar baya nan wai sun shiga meeting da malamai. Da gudu ta dawo wajen Ruky, ta sameta durƙushe azaba ta isheta, bata son suje clinic ɗin cikin makaranta dan an riga an tashi. Idannunta na cika da ƙwalla itama ta kamata ta miƙar. “Tashi muje wajen security ko zai taimaka ya barmu mu fita kawai, amma shima Baba Driver bai ƙyauta mana ba”. Da ƙyar da ƙyar Ruky ta iya miƙewa suka isa gate ɗin, cikin sa'a suna isowa sai ga motar Yaya Ammar na isowa. Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke, dai-dai Mu'azz na fitowa daga motar, ya ƙaraso inda suke da sassarfa yana faɗin, “Lafiya kuwa? Miya sami Ruƙayyan?”.
“Yaya ciwon mara, muyi sauri mu tafi kasan idan ya fara tsanani sai suma. Amma Yaya driver fa?”.
Sai da ya buɗe musu suka shiga yake bata amsa yana reverse. “Baba driver accident yayi, yanzu haka ma yana asibiti”.
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, badai da su Aheel ba?”.
“A'a bada su ba, shi kaɗai ne yaje ɗakko motar Ummie (Aunty Lailah suke cema Ummie, Shariffa Ammie) daga wajen wanki”.
“Ya rabbi, ya jikin nasa?”.
“Gaskiya yaji jiki sosai, dan har yanzu ma ba'a bari an gashi ba. Motar kuwa tama tashi aiki, dan babbar mota ce ta haye shi”.
Gaba ɗaya jikin Nimrah ya ƙara sanyi, ita kanta Ruky dake fama da kanta hankalinta ya sake tashi, a haka suka iso gida ciwon marar ya ƙara tsanani, dole ma sai Mu'azz ɗaukarta yayi. Gaba ɗaya hankalin ƴan gidan a tashe yake da hanlin da baba driver ke a ciki, dan mazan gidan duk suna can. Ganin hanlin da Ruky ke ciki kuma duk sai suka maida hankali a kanta. Babu bata lokaci aka kira family doctor ɗin su, da yake ya san matsalarta yana zuwa allurai yay mata....
Basu sami ganin Baba Driver ba sai ranar Lahadi da yamma. Gaba ɗaya gidan suka shirya suka je suka duba shi. Yaji jiki kam kwari da gaske, amma Alhamdullah yana samun dukkan kulawar data dace. Ga matarsa an ɗakko tana jiyyarsa. Komai na asibitin Kuma su Yaya Ja'afar ne suka biya.
Received at 6:57 PM
[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: Sannan ya kamata mu yarda ba laifinsu bane akan abinda ya faru baya, shima kansa wanda ake son azabtar da su ta dalilinsa mufa sani rayukanmu ya jajirce wajen karewa, ALLAH ne ya ƙaddara za'a tarwatsa mu a ƙauyukanmu har mu watse irin haka. Hasalima mutanen nan dake munana shi a garemu sune silar faruwar komai akan waɗan can abubuw......”
“Rabe! Kana nufin wuyanka yayi kaurin bijirema su Oga Dagger ko? Amma kasan minene hukuncin yin hakan a gareka ko? Karka manta kana cikin ƴantattun da aka bama damar zuwa su rayu a cikin mutane har suyi aure su hayyafa cikin ƴanci. Baku san wahala da azabar da mu dake cikin jeji kullum a ɓoye muke sha ba. Mutanen nan da kake ƙoƙarin karewa ance maka kaje kai musu wani abu ne? Information ɗin abinda ke gudana a rayuwarsu kawai akace ka dinga kawowa. Musamman ita wannan yarinyar Nimrah, amma taurin kai yasa ka zauna kana kawowa mutane ƙauli da ba'adi, gashi nan har sai da ka jama kanka zaman guri ɗaya, da da ƙarar kwana ma yanzu wani labarin ake ba naka ba. Ni dai yanzu ga saƙo, Oga Mole da Oga Dagger sunce gobe zasu turo sabon driver ka turashi ga mutanen nan ya maye gurbin ka, zaɓi ya rage naka kayi koka kuskure kai ne zakai kuka, dan a yanzu ba kai za'a hara ba ƴaƴanka ne ko matarka”...
Yana gama faɗa ya miƙa batare da ya saurari magiya da roƙon Baba Driver ba.....
★>><<<<★>>>><<★
★DUBAI★
Ganin yanda Nabeeha ke faman haɗa kaya ya bama Ismat data kawo mata breakfast har ɗaki tsoro. Duk yanda taso daurewa saita kasa. Cikin damuwa ta ajiye tray ɗin da take ɗauke da shi ta nufeta. Hannunta ta riƙe cikin rauni da damuwa ta ce, “Aunty wai mi kike yi haka ne? Ina zaki kike haɗa kaya?”.
Hannun nata ta fisge, kukan da take faman riƙewa tun daren jiya saboda taurin zuciya a karo na farko ta fashe da shi..........✍️
Received[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 12
.........“Ismat zan koma ƙasata, wlhy na gaji da wannan rayuwar, bazan iya ɗaukar huɗubar Momy ba, gara na koma gidan mijina nai zaman jiran dawowarsa ko nan da shekara hamsin ne ma ba ashirin da biyar ba”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ismat ta sauke, dan koba komai itama an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi dama. Ta kama hannun Nabeeha suka koma bakin makeken gadon ɗakin da yaji shinfiɗu na alfarma, dan duk da haɗuwar gidan da komai na cikinsa ɗakinta na musamman ne. Gyara irin na ƴar gata Adeel yasa akai mata. Hannayenta duka a cikin na Ismat ta ce, “Aunty wlhy koni ina bayanki ki koma gidanki, dan ita Momy idannunta sun rufe da son kuɗi bata duba abinda muke so koya dace damu. Ita kawai tafi kallon abinda zata samu. Gamu dai a cikin ƙaton gida a kuma ƙasa irin ta Dubai da kowa ke buƙatar yazo, amma wlhy Aunty Jiddah ta fimu kwanciyar hankali, tana rayuwar auren ta ga yaranta abin sha'awa, shiyyasa wlhy nima na fara ji a raina zanyi na nata na koma gidan Abba na bashi haƙuri na samu miji nayi aure. Dan in har muka cigaba da rayuwa da Momy anan wataran sai mun lalace, dan waɗan nan shaggun mutanen babu abinda suka iya sai son mata kamar su babu matan a cikin nasu ƙabilar”.
“Ismat wlhy ni duk bama wannan ba, babban abinda ke bani mamaki da Momy itafa kawai na kashe aurena saboda wannan mutum yace mata aurena yake son yi, haba miyasa ba zatai tunanin daya dace ba, dukiya irin ta mutumin nan, da nasaba ta gidan mulki, mulkin ma mai ƙarfin gaske ne zai zauna wani auren baƙar fata ƴar Africa saboda rainin hankali da ɗaukar mutane jakai. Kiga yanda suke wulaƙanta matan African fa kamar wasu dabbobi dan ko bayi na baya sun fi matan da ake kawo musu suna iskanci da su a yanzu mutunci da daraja. Wlhy Ismat ina son mijina, duk da ina jin takaicin auren shegiyar yarinyar nan har yanzu a zuciyata....”
“Na sani Aunty, ki share wani batun yarinya kawai muyi tafiyar mu, dan uwarta mune zamu miki maganinta, da ƙafarta zata bar gidan batare da kowa ma ya sani ba ta koma ƙauyen su, idan tace ita ƴar hau ce mu ƴan hau-hau ne to”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske Nabeeha ta saki, tana mai jin nutsuwa da gamsuwa da zancen autar tasu. A gefe zuciyarta na jin matsanancin kewar mijinta da buƙatar son kasancewa da shi da akoda yaushe take yaƙi da kanta a kai, sauƙi-sauƙin ma da take samu kullum cikin mafarkinsa da yanda yake tafiyar da ita a shimfiɗa take, shiyyasa take samun sassauci da jinsa kamar a kusa da ita har yanzu.....
Da baya-baya Hajiya Hasiba tabar bakin ƙofar ranta a matuƙar ɓace da tattaunawar yaran nata. Ƙayataccen ɗakinta ta shiga, ta zauna a bakin makeken nata gadon hannunta dafe da kanta. Jitake kan nata na wani mugun sara mata, sai dai abinda ke mata kai-kawo na takaicin yaran nata na son danne ciwon. Lallai lokaci yayi da zata nunama su Nabeeha ita ba sankaran uwa bace sha-sha-sha kamar yanda suke tunani. Taya zata bari ma Nasiru yaci nasara a kanta, bayan ya rabata da Jiddah ya rabata da Nabeeha da Ismat da suka rage mata kuma. Ta jima da fahimtar soyayyar da Ismat kema Ja'afar, sai dai bata damu ba ganin yanda shi Ja'afar ɗin yaƙi kulawa, amma yanzu ta fahimci Ismat na zuga Nabeeha ne su koma gidan ubansu saboda son da take ma Ja'afar, kenan da sunje sun kwantar ma da ubansu kai itama sai ya aura mata shi, shekenan ita kuma A'isha ta haifama ƴaƴa ko? To kuwa zasuci ubansu.
Da wannan tunanin tai ƙwafa, tare da miƙewa zuwa gaban wadrobe ɗinta, ta ɗibo duk passport ɗinsu dake wurinta, cire na Nabeeha da Ismat tayi ta canja musu waje, daga haka ta hau shirin fita. Dan tana buƙatar ganawa da Adeel yanzu nan basai gobe ba.....
§§§§§§§§§§§§§§§§
★EGYPT ★