← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana komawa ɗakinsa ya zauna a gefen gadon sa yana kallon sojojin dake ƙoƙarin ɗaura tvn da suka kammala haɗawa a jikin bangon ɗakin. Baiyi musu magana ba, dan ko gaisuwar da sukai masa bai amsa ba a sanda ya shigo hannu kawai ya ɗaga musu. Suna kammalawa suka fice daga ɗakin tare da maida ƙofar suka rufe masa. Shima sai ya rufe idanu kamar yana barci amma ƙwaƙwalwarsa ce ta shiga aikin aunawa da lissafin abinda ya faru.
“Facemask Analysis. Camara jikin agogo”. Ya furta a saman lips yana wani ɗan gajeren murmushi har lokacin idanunsa a rufe. A zuciya ya cigaba da ayyana suffar mutumin dalla-dalla da irin ƙwaƙwalwar ma'aikacin daya san aikinsa. (Fuskar bogi, agogo, tsayayyun idanu na masu busashiyyar zuciya da shekarun girma na tantance gwagwarmayar rayuwa na tsawon lokaci. Yanayin motsin ƙwayoyin cikinsu na ƙwararren operatives. Hakan na nufin wani daga cikin manyansu ne. Ba sabon shiga ba. Barazanar da ya faɗa. Sun ce suna sarrafa shugabanni… hakan na nufin akwai infiltration a cikin gwamnati. Wannan na iya zama sashin da ke kai rahoton Board of Inquiry. Ya ambaci makusanta. Hakan na nufin da damar su Imran ya zo wurina shekaru biyar da suka wuce. Yanzu kuma sune suka saka aka dakatar da shi. In dai haka ne to akwai idanu dake zagaye da Imran cikin rundunar soji ko wajenta, lallai Imran zai iya shiga haɗari akoda yaushe dan ko zai mutu bazai bisu fuska da fuska ba.
Ya furzar da iska mai nauyi yana runtse idanu, dan Imran wani sashe ne na jikinsa da taɓashi tamkar ruguza jarumtarsa ne.
Abu na uku tambayar su (Me yasa suka barni da rai har yanzu? Nima wannan tambayar ta jima a raina. Tabbas da nine a matsayinsu, zan kashe wanda nake tsoro musamman in haɗarinsa zai zama babbar barazana ga ƙasata bawai a karan kaina ba. Amma su suna bukata na a raye. Me yasa?) yay shiru na tsawon lokaci, sai kuma ya tashi zaune da ƙyau ya ɗauki pen da takarda ya rubuta wannan tambayar.
_“They need me?. For what? To watch me? To use me? Or to fear me?”_
Pen ɗin ya kai saman lips ɗinsa da suka ɗan bushe dan yau yana azumi. Abu na huɗu (Wasan da suke cewa ya fara… hakan yana nufin wani babban shiri da suke da shi a wannan tsakanin kenan? Wani sabon hari ne?. Ko wata rawar juyin siyasa?. To amma ai basa buƙatar mutum kamar ni wajen gane kosu su waye?, ko ina matsalar?. Wannan kuskurensu ne ko ni ne ban fahimta dai-dai ba?) ya sake yin shiru alamar dogon nazari.
Tsohon lokaci yana kai kawo da tunaninsa, sai kuma ya kai dubansa kan television ɗin da aka saka a ɗakin. Karo na farko ya miƙe yana ajiye littafin hannunsa da pen ɗin, gaban tvn ya isa, sai da ya gama duba ko ina na jikinta ya tabbatar babu camara sannan ya ɗauka remote ya fara searching channels, tashoshin dake cikin decoder ɗin da aka haɗata da ita duk zaɓaɓɓune. Domin guda uku ne kacal ba'a komai a cikinsu kuma sai abinda ya shafi labarai. Labaran ma ba kowane labari ba. Dan a yanzu dai kusan harkokin siyasa ne da campaign da aka fara kusan wata uku kenan. Idanun ya janye a hankali cikin salon yin luuu da su ya maida gefe da sakin murmurshin nan nasa na ƙeta. Sai kuma ya maida remote ɗin ya ajiye inda ya ɗauka ya koma bakin gadon ta sake zama..
Received Gaɓar da tafi tsaya masa ce ta sake maimaita kanta a brain ɗinsa. (Sun ce suna sarrafa zuciyar manyan. Idan haka ne, bayanan da Imran ya kawo min game da janar mai ritaya… dole sai na sake nazari. Domin kuwa wani daga ciki yana iya zama mai sarrafa Janar a gefe, da wannan damar kuma kaɗai za'a iya cimma Imran. Dan tabbas tunda har suka faɗa ya fahimci cewa ziyara ta farko da ta biyu na Imran sun haifar da damuwa a ɓangaren kungiyar shaiɗanun nan, shiyyasa ma suka hana shi cigaba da zuwa.
Ya ɗan murmusa kaɗan, dan ya fahimci abu mafi mahimmanci har yanzu suna tsoronsa. Shiyyasa suka hana a ziyarcesa, suka hana yay communication da kowa, suka saka aka killaceshi inda baya ganin kowa sai masu tsaronsa dake kawo abinci dama duk abinda yake buƙata. Ya jima da gane a jikin masu tsaronsa akwai camara dake isar da saƙon shigarsu da fitarsu wajensa. Zuwan baƙon nan ma ba saƙon da yazo faɗa bane kawai maƙasudin zuwansa nan, suna son suga ko ya raunata a zuciya zuwa yanzu. Suna son su gane ko ya ragargaje da raunin kaɗaici. Suna son su tabbatar ko har yanzu yana da ƙarfi daga irin ƙarfin da suke tsoro. Gaba ɗaya ma sai yaji ya sake raina wayonsu. Dan da da gaske, suna da ƙarfin ikon da suke faɗa, ba zasu zo su gaya min ba. Babu mai saƙon barazana da ikon cikakke sai wanda yake jin tsoron wanda aka aika wa saƙo.
Yay ƙwafa, saboda wannan tunanin ya ƙara masa ƙarfin gwiwa, da fushi, da nunin ya sake tashi tsaye da shirye-shiryesa. Dole kuma ya aikama Imran saƙo batare da jinkiri ba...........✍️
[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: KIƊA A RUWA 2

26

..........KWANA UKU da dawowar Mammah suka karɓi baƙuncin ƴan Bauchi da sukazo sunan Aunty Mommy. Gwaggo Khadijah, Gwaggo Alawiyya, da Gwaggo Nanah. Sai matar Uncle Jamilu da wannan ne karonta na farko da tazo. Dan tun abinda taima su Mammah ɗin a wancan shekarun take jin matsanancin kunyar zuwa inda suke. Sai dai har cikin ranta taji nadama. Musamman da ayanzu su Mammah ɗin ne riƙe da rayuwarsu tunda su Ja'afar ne suka buɗema Uncle Jamilu babban shago kayan sakawa a can Bauchin ƙyauta, da shi suke ci suke sha. Sannan kuma suka ɗauki nauyin karatun yaransu a makaranta mai ƙyau. Gwaggo Nanah kam ta fita zakka a cikin ƴaƴan Inna, tana iya ƙoƙarinta dama tun ma suna cikin wahalar rayuwa kamar yanda Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya keyi. Sai dai tsoron ƴan uwanta su Yaya Babba ke hanata zuwa inda su Mammah suke. Wannan karon kuwa itama sun mata halin nasu, dan mijinta ya gudu ba'a san inda yake ba shekara biyu kenan duk sun ƙi taimaka mata, ga wahala tana ciki ita da yara. Babu mai taimaka mata sai Uncle Jamilu da su Gwaggo Khadijah ɗin. Shiyyasa ta yanke shawarar zuwa sunan nan danta sanar ma Mammah halin da take ciki ko zata samu wani taimako. Kuɗin mota ma Uncle Jamilu ne ya biya mata.
Ba ƙaramin daɗi Mammah taji da ganinsu ba. Musamman Gwaggo Nanah da matar Uncle Jamilu Badiyya da suketa ɗari-ɗari suna jinjina hukuncin UBANGIJI da ganin gidan da Mammah ke ciki a yau da zuri'arta. Lallai duniya budurwar wawa, wanda yace shine kuwa ba shi ɗin bane ba.
Tuni Mammah ta saka su Kulu masu aiki suka gyaro musu ɗakunan baƙi, dan sunyi isowar wuri lokacin sha ɗaya na safe, sunce tafiyar asuba sukayi dan mota suka ɗakko kai tsaye. Mammah dake ta farin ciki ta ce, “Ku fara yin wanka da ruwa mai zafi sai kuzo ku karya. Bara kiga nasa a kakkaɓo min yaran nan duk suna gado jiya sun raba dare ne suna shargallen su”.
Gwaggo Khadijah tai ƴar dariya da faɗin, “Aike da gayyar nan taki Maman Ma'aruff sai ALLAH. Kinga barsu suyi barcinsu, muda ba yau zamu koma ba. Anjima ma wata hidimar ce ta bikin suna a kansu”.
“Kamar ko kin san harda fati suka shirya wai. Biebah ce kawai ta iya bin su Lailah gidan maijegon, yanzu babu jimawa suka fice suma dan jiya sai goma suka dawo”.
Yanzu kam Gwaggo Alawiyya ce ta ce, “Kai waɗan nan yara ALLAH dai ya saka musu da alkairi. Wlhy samun surukai irinsu sai an tona Addah.”
“Ai su Shariffa sun wuce surukai ƴaƴane Alawiyya. Babu abinda zan cigaba da musu sai addu'a da fatan suma ALLAH ya basu masu yi musu”.
Gwaggo Nanah dake jinjina kai ta ce, “Wlhy ki musu ki ƙara muma muyi musu, ga gidan Yaya Babba can su Haire su da surukai ba arziƙi. Jiya matar Haƙilu kamar zatai dambe da Haire akan ɗanta, ke bakiji wannan tujara ba abin kaico”.
Murmurshi Mammah tayi, saboda a saki zancen ta ce, “ALLAH ya ƙyauta to, ai zamanin ne ya zama abin tsoro sai addu'a kawai. Kunga kuyi wankan kuzo ku karya hirar tafi armashi”.
Godiya suka yi ta juya ta fita. Dukan su suna jin ƙaunarta a ransu, Badiyya kam kunyarta take ji sosai shiyyasa tunda suka gaisa tai shiru kanta a ƙasa. Sarai Mammah ta fahimceta, dan haka ta ƙuduri aniyar cire mata abinda ke ranta gaba ɗaya, dan ita babban fatanta ta haɗe kan zuri'ar Abdul-rasheed ba rabuwar kansu ba....
Chapter 25 · 0% Book details