← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 47

Sashe 10

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da baya. Jinin sarauta dan kuwa daula babba suke da ita a yankin larabawa. Sannan zuri'arsu zuri'a ce mai ɗunbin dukiya da kaso huɗu na arziƙin Dubai yana da alaƙa da shi. Adeel irin gagararrun yaran nan ne da giyar mulki data kuɗi ke ɗawainiya da su. Dan kuwa iya shegen da yake zubawa a cikin Dubai ba'a magana.
     Harkar business ce ta haɗashi da Hajiya Hasiba, a dalilin First Lady da suke aminta. Sunyi wani zaman meeting Hajiya Hasiba ta kasance kujerarta kusa data Adeel a meeting room ɗin, irin ta ajiye wayarta a table sai aka irin kirata ɗin nan, bata ɗaga ba kasancewar suna a halin meeting har kiran ya tsinke, dai-dai screen ɗin wayar na komawa yanda yake ƙyaƙyƙyawan hoton Nabeeha dake a fuskar wayar Hajiya Hasiba ya bayyana. Sai ko karaf a idon sa. Cak ya tsaya da bayanin da yake ya zubama wayar ido, abokan meeting ɗin nasa sukaji shiru duk sai suka ɗago suna kallonsa, cike da basarwa ya ɗauke idanunsa ya cigaba da jawabinsa, amma bini-bini idonsa nakan screen ɗin wayar Hajiya Hasiba har aka tashi.
      Hajiya Hasiba ta lura da kallon da Adeel kema wayarta, amma sai bata kawo komai a ranta ba har suka wuce. Mizai faru da daddare kawai sai ga Firt lady ta kirata wai Adeel nason magana da ita, idan ba damuwa kuma so yake su haɗu. Mamaki ya kama Hajiya Hasiba, ta tambayi ko lafiya? First Lady ta bata amsa da cewar wai akan wani hoto ne da ya gani a fuskar wayarta sanda suke meeting. Sosai Hajiya Hasiba ta zaro idanu tana dafe baki, kafin ta ce, “Kai ranki ya daɗe ɗiyarki ce fa Nabeeha, kin san dai tana da aure kin kuma san waye mijinta da fitinarsa”.
     Cikin nuna rashin damuwa First Lady tai murmurshi da faɗin, “Yo ALLAH na tuba sai me Hajiya Hasiba, aure nawa ne a wannan zamanin da shi gara babu. Ke dai kawai ai sha'ani. Mijinta kuwa girman kansa na banza ba ko sisi, kin san waye kuwa Adeel? Hummm na baki dama daga nan zuwa minti talatin ki bincika sai ki yanke hukunci. Ni dai na isar da saƙo yace zai turo mota a ɗaukeki a kaiki inda yake ”. Daga haka ta yanke wayarta.
     Shiru Hajiya Hasiba tai na tsawon lokaci, dan babu abinda ke zuwa mata a zuciya da brain sai fuskar Zak-Shadow. Amma dai ta daure ta fara binciken waye Adeel kamar yanda First Lady ta bata shawara. Tun a ambaton farko kanta ya nema bugawa, jin nasabar gidansu kawai, jin ɗan waye daga zuri'ar daya fito. Data bincika arziƙin zuri'ar tashi kawai bama shi wadda ya mallaka ba bata san ta rikito a kujera ba tsabar rawar jiki. Har lokacin da za'a ɗauketa yayi bata iya ta dawo a hayyacinta ba saboda matsanancin mamaki. Ai babu ɓata lokaci ta shirya a gurguje tabi ɗan aiken. Ai ko kanta da zuciyarta sun nema fashewa saboda inda aka kaita matsayin wajen hutawarsa. Wani mahaukacin azababben garden ne da in ka kirashi da suna aljannar duniya bakai ƙarya ba. Ga masu hidima zagaye da wajen da wasu mugayen masu tsaro ya subahanallah. Ita dai haka aka kaita har inda yake jiki na ɓari.
     Kallo ɗaya yay mata ya maida kansa ga laptop ɗin gabansa, a haka cike da isa ya nuna mata wajen zama. Sai ta dinga jin kamar ba Adeel ɗin juya bane da sukai zaman meeting, koda yake ko'a jiyan dama yanda yake magana da isa da ƙasaita kasan akwai girma da izza. Amma a yau ɗin ba'a magana. Ya share fin mintuna goma sannan ya gyara zamansa, babu wani tauna harshe ko girmamawa kai tsaye yana kallonta ya furta, “Yarinyar dana gani kan wayarki nake buƙata, ina fatan ba hotonki bane dan naga kuna kama sosai, tsufa kawai zaki nuna mata”.
     Kan Hajiya Hasiba a ƙasa tana murmurshi ta ce, “A'a bani bace. First born ɗina ce, sunanta Nabeeha”.
      “Nice...”
   Ya faɗa cike da iskanci yana ajiye kofin hannunsa. Sai da ya ƙara busar iska ya cigaba da faɗin, “Za'a iya kawo min ita a yau? Zan bada ko nawa ake buƙata, daga biliyan 1 zuwa sama”.
Received at 2:42 PMReactions:
[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 9

..........“Sir kawai fa dan na taka ita Ruƙayya ɗin ne ban kula ba, kafin na bata haƙuri sai ta hankaɗe ni ta ƙwace wayata ta jefar a ƙasa ta fashe, ni kuma na zuba mata ruwa a jiki ƴan class suka yi dariya. Itafa Nimrah ɗin ma bata ajin ta fita, kawai tana shigowa ba tambayar ba'asi ta hau dukana itama Ruƙayyan na tayata, ni kuma naji wahala na cijesu kawai suka gwara kaina da bango wai aljanunsu ya tashi...”
        “Da dai kin fito kin faɗi gaskiya yarinya da yafi miki”. Cewar Ruƙayya tana hararta. Uwarta zatai magana principal yay saurin tarar numfashinta. Idanunsa akan su Ruƙayyan ya ce, “Ke haka akai?”.
      “Sir ta ɓoye asalin zancen”.
   “To miya faru?”.
“Yarinyar nan ƴar iska ce Sir, a bayan desk ɗinmu suke ita da ƴar iskar ƙawarta, kullum sai suna damunmu da kallon Film ɗin iskanci a waya, mun musu magana akan idan suna kallon rashin tarbiyyarsu a waya suna saka Bluetooth amma sun ƙi dainawa. Kawai yau suna kunnawa na juya na ƙwace wayar na fasa banza, shine tazo zata min hauka ni da Ninah muka sauke mata nata ƙaramin hau ɗin”.
     Rawa jikin yarinyar ya fara, ta fara rantsuwa ita sharri su Ruky sukai mata. Uwarta ma bala'i ta fara wai za'a ma ƴarta sharri bazata yarda ba. Kodai principal ya bari ƴan sanda su tafi dasu Nimrah ɗin ko kuwa tai ƙarar makarantar gaba ɗaya. Cikin takaici Ammar ya ce, “Hajjaju ya kike Abu kamar baƙya ganewa ne, shin anan akwai wai mai tsoron zuwa police station ɗin ne anan akace miki. Yaran nan sun faɗi abinda ya faru har sukai rikici da ƴarki, maimakon ma ki damu da abinda take aikatawa kina neman juye wa mutane shirme. To muma bazamu yarda ba, dan bazata ɓata mana tarbiyyar yara ba, banda ma rashin kula har yara na kallon banza da wofi a waya iyaye basu sani ba, kuma miye na zuwa da waya makaranta? Gasu nan ko waya basu da ita yaran nan kuma basu taɓa damuwa ba duk da sun kai ƴammatan daya dace ace an barsu da ita, idan anyi maganar ku daina bama yara waya ko ku dinga kula dasu idan kun basu musamman masu tashen sabuwar balaga irin su kuga kamar an raina ƙoƙarinku ne. Ba haka bane, a irin wannan gaɓar waɗan nan abubuwa suke kwaɗaituwa a zukatansu, dan haka muma bazamu yarda ba, yaranmu masu tarbiyya ne, bakuma za'a ɓata mana su anan ba, kuma yanda sukai mata sun min dai-dai....”
    Hayaniya sosai ta kaure a office ɗin tsakanin Hajiya da Ammar, sai da ƙyar aka fitar da Ammar itama Hajiyar principal yace taje zasuyi bincike akai. Dan haka an bama yaran suspension na sati ɗaya su duka ukun har sai an tabbatar da gaskiyar mai laifi. Suko ƴan sandan data kira suka sallamesu. Suma ƴan sandan sanin makarantar ta jiga-jigai ce basu ja da nisa ba suka wuce.
       Yaya Ma'aruff dake hararar su Nimrah ya ce, “Sai ku wuce muje masu kunnen ƙashi. Hankalinku ya kwanta ai ko. Banda ma fitina ku kuma haifeta da zaku hukuntata? Ba kusan hanyar kai report bane, jibeku da kawuna kamar kullun magani”.
     Babu wanda a cikinsu bai cika baki da iska ba. A haka suka fito suka shiga mota shima Yaya Ammar na zuba musu tashi hararar.....

      ★ Koda suka iso gida ko kallon inda suke su Yaya Ma'aruff basuyi ba suka shige ciki abinsu. Kallon juna Nimrah da Ruƙayya sukayi, cikin marairaicewa Ruky ta ce, “Wlhy yau akwai matsala Trouble Queen....”
    “Babba ma kuwa”.
Aka faɗa daga bayansu, a tare duk suka juya, Mu'azz ne daya zama matashin saurayi ɗan shekara goma sha takwas, dan kuwa ya kammala Secondary ɗinsa ma yana shirin shiga jami'a. Yanzu kam Nimrah ce tace, “Ya Mu'azz kaji tsoron ALLAH”.
         “Oh, to da tsoron ku nake ji. Ba kunce ku baƙwa jin magana ba. To Daddy ma na nan zuwa dan Uncle J ya kirashi shima”. Wani mugun ƙwalalo idanu waje sukayi a tare, shi ko ya kwashe da dariya yana barin wajen. Da sauri sukabi bayansa, amma yaƙi tsayawa har suka shigo falon. Cak kuwa suka tsaya, ganin kowa yana nan har su Aunty Lailah. Yaya Ja'afar ne ya fara zuba musu harara da faɗin, “Sannunku ƴan wrestling ko ƴan boxing ma zance ban sani ba nikam”.
Received at 2:42 PMReactions:[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 11

.........Kwanaki kusan biyar su Nimrah na cin ƙaniyarsu da aiki, sun jikatu matuƙa sunyi laushi, kuka da roƙo babu kalar da basuyi ba, hakama kawunansu sun bama Daddy Imran haƙuri amma yace idan suka bar aikin nan Boarding fa babu fashi. Da ga ƙarshe dai suka zagaye suka kira Aunty Ummie a waya suna mata kuka suka sanar mata. Dama kwana biyu bata leƙo gidan ba saboda aiki. Aunty Mommy kuwa basa ƙasar ita da mijinta sai a satin nan zasu dawo. Ita ko Aunty Mimi ciki gareta tsoho haihuwa ko yau ko gobe shiyyasa Mammah ta hanata zuwa gidan.
     Alhamdullahi zuwan Aunty Ummi da suke kira da Big Mah-mah ne ya cecesu a hannun Daddy Imran. Dan bayan an sako massalacin juma'a yazo gidan gaida Mammah ta tareshi da daɗin baki da ban haƙuri har ya haƙura masu aiki su dawo gobe. Amma duk da haka da sharaɗin daga yanzu kullum dasu za'a dinga shiga kitchen yin girki. Da wannan ALLAH ya ƙwacesu. Masu aiki suka dawo, su kuma suka samu sauƙi. A cikin satin ma suka koma zuwa islamiyya dan suspension ɗin ta ya ƙare, sai kuma karatun da akayi basa nan ya sakasu a gaba. Sati ya zagayo suka koma boko ma, amma duk da haka sai da akai zama da Hajiya ta kafa sharaɗin babu su ba yarinyar ta, dole kuma a raba musu wajen zama sannan case ɗin ya mutu. Dan an dai gane ƴarta na kalle-kallen banza a waya da gaske kamar yanda su Nimrah ɗin suka faɗa......

        >>>>><<<<<<
Chapter 10 · 0% Book details