← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 47

Sashe 8

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Ranar ta yi zafi sosai kasancewar ya tareta ne a lokacin zafin nata. Domin kuwa ƙarfe ɗaya ne a lokacin. Dan daga massalaci ma ya wuce special Military Corrections Facility.... ɗin. Wani nauyi ya lulluɓe zuciyar Imran tun daga lokacin da ya taka ƙasa ya ƙarasa gaɓar ƙofar babban prison ɗin. A karo na biyu cikin satittika biyu yana zuwa wurin da rabin zuciyarsa ke tsare.
      Ya shigar da sunansa kamar zuwan farko, aka tabbatar da izinin shigarsa bisa doka. Daga haka aka rakashi zuwa ɗakin ganawar kamar na wancan lokacin. Wurin nan buɗaɗɗe da babu shamakin gilashi a tsakaninsu kamar saura, kujera biyu, teburi a tsakiya. Cikin mintuna kaɗan aka kawo Dada. Hannayensa daure da handcuffs, fuskarsa ɗin nan a ɗaure kamar yanda kowa ya santa, sai dai a yanzu babu zafafawa kuma ba murmushi. Amma idanunsa sun kasa ɓoye gajiyar shekaru uku da wahalar ƙuncin rashin aikin daya zamewa jiki da zuciya sabo.
       Imran ya zuba masa ido batare da yace komai ba. Shi ma Dada bai yi magana ba har sai yada ya zauna. Sai wani ɗan shiru mai zurfi ya cika ɗakin. A hankali Dada ya zubama Imran ɗin juyayyun idanunsa, kamar yanda shima Imran ɗin ke kallonsa.
     “Ni karka cinye ni”.
   Dada ya faɗa yana hararar Imran. Murmurshi Imran yayi a karo na farko. Shima sai ya furta, “Da zaka haɗiyun ma ai da na huta. Kaga sai mu fice abinmu batare da kowa yaji ya gani ba mu koma gida kaga yanda Mammah ta ƙara ƙyawu. Nimrah da Ruƙayya dasu Asma'u da Khalifanka suka girma. Ma'aruff da Ja'afar suka zama magidanta harda ƙyawawan yara masu kama da kai da duk suka ci sunanka da sunana. Ammar da Bilal suka sake girma. Mu'azz ma ya fara zama ɗan saurayi. Ummi da Momy da Mimi sun sake haihuwa, Biebah ta sake zama budurwa ƴar jami'a. Nabeeha na cikin kewa da son ganinka.”
      Wani sassanyan murmushi Dada yayi yana mai girgiza kansa da sake tsatstsare Imran ɗin da idanunsa. “Shike nan ka faɗa kaji daɗi, ALLAH ya albarkaci rayuwarsu gaba ɗaya. Ya sanya farin ciki da kwanciyar hankali a ciki. Ina fatan Mammah bata da wata damuwa?”.
          Shima cikin murmurshi Imran ya ce, “Alhamdullahi Mammah na cikin ƙoshin lafiya. Duk da dai an shiga ruɗani a farkon ƙaddarar, amma zuwa yanzu zuciya ta amsa da hannu biyu kuma ALLAH ya saka nustuwa da farin ciki. Sai dai addu'a ba'a gajiya ba. Dan kwanan nan ma suka dawo daga Umrah su dukansu dan har Nimrah da Ruƙayya ba'a bari ba. Kasan yanzu sune autocin Mammah, suna zuba shagwaɓar su yanda suke so da rashin ji. Dan a wata biyu kawai da tawa dawowar an gayyaceni makarantarsu karo na huɗu kenan akan rashin jin su. Mammah kuma da anyi magana ta tare ko ina ta hana ai musu faɗa. Koda yake suma su Ja'afar ɗin babu mai son musu faɗan, sai Hafsa ce ma ke ɗan lallasasu idan sunje gidan shiyaysa basa son zuwa can su kwana”.
        A mamakin Imran murmushi mai faɗi Dada yayi a yanzu fiye dana farko har haƙoransa na bayyana. Ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Ai nasan za'a rina. Dan tun a ranar farko na fahimci kam hali yazo ɗaya. Shike nan dai Mammah ta cika min burina na ƙwace Ruƙayya.”
      Imran ya ɗan murmusa shima da faɗin, “Ta cika maka kam ita da Nimrah, dan Nimrah ta taka rawar gani wajen janye hankalinta da ƙyau”.
       “ALLAH ya raya su”.
Ya faɗa a taƙaice.
   Imran ya lumshe ido, muryarsa a raunane ya ce, “Amin ya rabbi. Gani na dawo Zak.... Ina bukatar ka bani dama dan fahimtar abin da bakace ba a ranar farko.”
        Dada ya ja dogon numfashi. Ya jingina da kujera kamar mai yaki da wani abu a zuciya. “Babu abin da zan iya faɗa da baki ba tare da ya cutar dani ko ya cutar da ku ba”.
     Imran ya jinjina kai. “Na fahimta, amma ka sani nazo jin duk abinda zaka iya rubutawa… Sannan a wannan gaɓar faɗar tafi amfani, dan nima ina tafe da muhimmiyar magana. Idan ba yau ba, yaushe?”
        “Haka ne”. Cewar Dada yana zaro wasu murɗaɗɗun takardu daga ƙarƙashin rigarsa ta prison. Kai tsaye ya miƙa takardar ga Imran kamar yana mika zuciyarsa. “Ka sakata a jikinka dan nasan bazasu bari ka fita da ita ba. Na rubuta wannan cikin shekaru uku. Babu kuma wanda ya kamata ya gani sai kai.”
      Hannu Imran ya miƙa masa shima, bai karɓa nan take ba saboda nauyin da kalmar “Sai kai” ta yi masa. Idanun Dada suna cike da gajiya amma akwai hasken wanda ya tsaya tsayin daka, wanda bai fasa ba, baya jin kuma zai fasa ɗin koda na daƙiƙa guda ne, duk da cin zarafi, yaƙi, da shekaru uku na shiru sukazo masa da shi. Ba wanda suka killacesa anan yake kallo ba ƘASAR da masu tasowa a GOBEN ƘASAR kawai yake hange da kallo. Shiyyasa ya yarda zai sadaukar wajen ginawa tare da duk mai zuciya irin tasa, domin ƴaƴa da jikoki su amfana a bayan rayuwarsu.
       Imran ya karɓi takardar cikin sauke ajiyar numfashi. Kallonta yake cike da nauyi saboda sirrikan dake cikinta. Yana buɗewa ya ga layuka marasa yawa amma masu nauyi:
Sunaye. Abubuwan da suka faru. Kurakurai. Shakku. Hujjoji.
Da kalma guda ta ƙarshe. Sai kawai ya nannaɗeta kamar yanda ya bashi ya ɗaga rigarsa ya sakata a cikin ɗammararsa ta soja.
       Imran ya haɗiye wani abu mai zafi da ya tsaya masa a makoshi. Cikin ɗacin murya ya ce, “Zak… me kake so mu fara? Ina kake so mu fara kalla ko tunkara?”.
     Dada ya ɗaga kai ya kalle shi kai tsaye. Wannan kallo Imran bai taba mantawa da shi ba tun lokacin da suka yi fice-ficen yaki tare. Muryar jarumta ta shiga kunensa da izza da tabbacin MAZAN SUNA NAN A MAZANSU NA FAMA. GWARAZA KUMA BARADAI Masu tsayayyar zuciya da tsayayyar KALAMA..........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*

*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 6
Chapter 8 · 0% Book details