← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

       “Mammah dan ALLAH ki daina kukan nan ya isa haka”.
    Ammar ya faɗa cikin tashin hankali muryarsa na rawa idanunsa shima cike da hawaye. Sai kuma ya dubi mutumin da shima ke sharar hawaye ya ce, “Bawan ALLAH ka min bayani dan ALLAH. Minene alaƙarka da Mammah ta? Ku taimaka ku sanar min kada zuciyata ta fashe, dan kukan Mammah ba ƙaramin azabtarwa bace mai ƙuna a zuciyata”.
        Hawaye mutumin ya sake sharewa da handkachiff harda ɗan fyatar majina. Kafin ya kalla Ammar cikin rawar muryar alamun tahowar wani sabon kukan ya ce, “Ɗana ka kwantar da hankalinka, duk da ban san wanne a cikin ƴaƴan nawa ba ina ji a raina ko Bilalu ko Abdul-rasheed (Ammar) ne kai. Dan kune dai ƙananu da zan iya gani a wannan shekarun ba Haysam ko su Ja'afar da Ma'aruff ba”.
    Kafin Ammar yay magana cikin zafi Mammah ta ce, “Har kana iya cigaba da riƙe zuri'ata a cikin ƙwaƙwalwarka amma ka gagara waiwayen inda nake Tasi'u....?”
        “Wlhy Adda A'isha kunya ce ta hanani, tsananin kunyarki nake ji da tsoro da nadamar son zuciyata. Ina ganin bazaki sake kallo na ba a rayuwarki, bazaki sake son ji koda daga wani ne kina da ɗan uwa irina ba. Adda A'isha ni azzalumi ne butulu da ban cancanci gafara daga gareki ba balle marigayi Yaya Abdul-rasheed, dan kuwa mun kasance butulu da ga ni har Bashir da danginsa......”
        “Bashir bai kasance butulu a gareni ba, dan kuwa na tabbatar idan shine a raye komai girman laifin da yake ganin ya min bazai ɓoyema ganina a tsaho waɗan nan shekarun ba. Haba Tasi'u, kun maida ni mara kowa a duniya, mara gata, mara dangi gaba ɗaya. Badan Yaya Nasiru ba da nace ban san daɗin zuri'a ba a duniya. Da ƴaƴan Kawu kamar sun waiwayemu munata zumunci har bikin su Haysam duk dasu a kayi suma yanzu sun sake ɗauke min wuta gaba ɗaya saboda ƙaddarar rayuwa da muka sake shiga. Shike nan kowa ya juya bayansa a garemu dangina dana Abdul-rasheed idan ka cire Jamilu da su Khadijah saboda kawai sune ciki ɗaya da Abdul-rasheed. Wlhy idan kowa zai barni banyi tunanin harda kai ba da muke ciki ɗaya Tasi'u, kada ka manta nice na fita a cikin Inna ka kwanta, sannan nice na gama sha daga jikinta ka amsa. Miyasa zaka gujeni tsawon shekaru ashirin da shida, a talatin kaɗan ne babu rabona da kai fa Tasi'u. Miyasa? Miyasa haka?”.
        “Wlhy kunya ce kamar yanda na sanar miki Adda, dan ALLAH ki yafeni ki gafarce ni na tuba”.
    Yay maganar yana sauka ƙasa ya durƙusa a gabanta tare da riƙe ƙafafunta duk da kuwa shekarun dattijantaka sun bayyana a gare shi shima. Bata hanashi ba, sai kuka da take itama. Ga Ammar dake rungume da ita shima tuni kukan yake, dan a duniya basa ƙaumar ganin hawaye Dada da Mammah na ɗiga. Tsohon lokaci suna a haka kafin Mammah ta fara tsagaita nata kukan ta kama dattijon tana miƙarwa da faɗin, “Shike nan ya isa. Na yafe maka  ka share hawayenka. ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya. Ya jiƙan Inna da Baba da Abdul-rasheed da Bashir.
Received at 3:00 PMReac
[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: Amma dan ALLAH karka sake yin nesa da ni kaji”.
       Tashi yay ya koma kan kujerar yana share hawayen nasa da faɗin, “In sha ALLAHU har abada bazan sake nesa dake ba Adda, na baya ma kunya ce da nadama ta sakani dole. Amma wlhy a kullum cikin begen son ganinki nake keda zuri'arki”.
       “ALLAH ya rufa mana asiri”.
  Mammah ta faɗa tana shafa kan Ammar alamar lallashi. Ɗakin ya sake ɗaukar shiru na wasu mintuna kafin ta kallesa ta ce, “Mi kake yi a Egypt? Ko nan kake aiki?”.
        “A'a nazo ganin likita ne kawai. Yanzu ina Paris. Sai dai kusan shekara ma biyar kenan na koma ƙasarmu, kawai dai ina zaune a kudanci ne sakamakon tsoro da fargabar tunkarar ki.
     Murmurshi Mammah tayi mai ƙayatarwa da faɗin, “Ja'iri ashe kana shakkata?”.
         “Adda wlhy ina yi dan kece madadin Inna a wajena. Ya bayan rabuwa ya iyalai?”.
      “To sai godiyar ALLAH, Iyalai kuma duk gasu nan sun girma sun zama magidanta. Duk da dai Bilal da Ammar da Biebah basu kai da yin aure ba. Amma Alhamdullah duk komai ya dai-daita babu abinda zamuce da UBANGIJI sai godiya”.
        “Alhamdullahi naji daɗi sosai wlhy Adda. Kice yanzu gida ya cika da ƴan jikoki na”.
      “A ya cika kam. Dan a ƙalla yanzu kana da jika goma sha bakwai zuwa sha tara nan gaba kaɗan, dan yanzu haka yau ɗin nan Mimi ma ta sake haihuwa ta huɗu. Matan Ma'aruff da Ja'afar ma duk suna da ciki a yanzu haka na uku-uku duk da ƙarami ne.”
       “Kai Masha ALLAH lallai zuri'a ta haɗu. Ina yaron kirki Haysam?”.
    Shiru Mammah tayi na sakanni, sai kuma tai murmurshi gajere da faɗin..........✍️
Received at 3:00 PMReac[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: 16

..........“Yana lafiya shima Alhamdullah. Kai fa ina fatan dai ƙanwata ta koma ko ka sake sabon aure?”.
    Kansa ya ɗan shafa yana murmurshi, sai kuma ya ce, “Ta koma bayan taga na koma da kuɗin gidan nan, dan har mun sake haihuwar yara biyu ma. Amma ta rasu shekara kusan bakwai data wuce. Sai yaran yanzu kawai.” ya ƙare maganar idanunsa na tara ƙwalla. A take tausayinsa ya sake kamata. Ta shiga jajantawa da masa ta'aziyya. Shima Ammar yay masa ta'azziya. Dan har yanzu bai san ainahin wanene shi ba, tunda sanda wacan abun ya faru suna yara sosai musamman shi da Mimi ma da basu wuce shida zuwa bakwai ba maybe, sai dai ya fahimci ɗan uwan Mammah ne na jini koda kamanni da yanayin tattaunawar tasu.
     Cikin share sabbin hawaye Tasi'u yake amsa musu. Mammah dai ta babbashi haƙuri daga haka ta koma jansa da hira harya saki jiki shima yana jan Ammar a jikinsa......

%><%><%><%><%>
Chapter 14 · 0% Book details