Sashe 44
Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gidan Mammah kam yau su Nimrah gidan Daddy Imran suka tafi zasu kwana. Harda Feddo da Bintu kuma suka shirya weekend ɗin nasu. Uncle Bilal ne ya kaisu da kansa, dan dama su ƴan gatansa ne. Tunda suka iso suka cika gidan da hayaniyarsu da karaɗi, aka fara faɗan ƙa'ida tsakanin Ruky, Nimrah da auta da suke kira Lolo. Dan shine sakon Ruky, dan haka yake ganin itama Nimrah sakon tashi ce. Wani lokacin kuma suke jansa tsiyar, dan ko yau suna shigowa ɗakinsa suka wuce suka kwaso masa chocolates na makaranta suka hau ci. Shi ko yana dawowa daga Islamiyya aka fara, sai da Ammie ta shiga tsakani. Sun gama da Lolo suka koma kan Aunty Ma'u. Wai sai ta faɗa musu miye tsakaninta da Uncle Billa. Cike da baƙar magana tace su shaƙeta ta sanar musu to. Da yake shaƙiyay ne suka sakata a gaba wai ai sun sani, Fiddo harda cewa ai taga wani bangle a ɗakin Uncle Billa an saka sunan Aunty Asma'u ɗin.
Received at 2:37 PMReactions: Duk abinda suke Ammie na jinsu, itama kuma hirar tasu ta fara kai hankalinta akan al'amarin Asma'u ɗin da Bilal, dan kwan biyun nan ta fahimci ko yaushe Asma'u na maƙale da waya, idan ta tambayeta sai tace wai assignment take yi. Ashe ita ta maida assignment ɗin. Kai yaran yanzu sai a barsu dai kawai. Tai murmushi mai yalwa, dan har cikin ranta wannan haɗin ya mata. Wlhy idan duk ƴaƴan data haifa zasu kasance matane ace yaran gidan Mammah suka auresu zatafi kowa farin ciki, dan jinin Mammah jinin alkairi ne. Abotar Imran da Haysam babban rahama ce kuma alkairi ga zuri'arsu guda biyu. Addu'ar fatan alkaici tayi ta cigaba da sabgarta.........✍️
Received atKIƊA A RUWA 2
42
........Bayan la'asar su Nimrah suna a garden suna basket ball su duka huɗu sai Yaya Khalifa, Yaya Mu'azz da Yaya Imam da suka zo gidan babu jimawa, sai Auta Lolo. An raba team ɗin biyu, amma Nimrah da Ruky sunƙi yarda a rabasu, dan haka sai ƙwange sukema su Mu'azz da rinto.
A yanzu ma ana tsaka da gardama Nimrah da Ruky sun dage kuma akan rinto ne Khalifa ya hararesu da faɗin, “Kufa matsalar ku rinton jaraba, shiyyasa sam bana son haɗa sabga da Ninah da Ruky munafukan yara ne ALLAH”.
“Ashe ka gane Broth, wlhy haka suke”. Cewar Mu'azz shima yana hararsu. Baki Ruky da Nimrah suka taɓe, Nimrah zatai magana sallamar maigadi ta dakatar da su. Imam ne ya amsa masa duk suka juyawa suna kallonsa. Kai tsaye inda Nimrah take ya isa, ya miƙa mata ƙaramar ledar hannunsa yana faɗin, “Saƙo ne wani ya kawo wai a baki. Yace malamin ku ne na islamiyya Kamal”.
Tsit wajen yay ana kallan kallo, sai Bintu ce da tai dariya da faɗin, “Humm guy ɗin nan fa ya dage wlhy”.
Kafin wani ya bata amsa Lolo ya amshi ledar, maigadi ya juya abinda yabar wajen. Dai-dai Lolo na fiddo littatafan cikin ledar. Yanzu kam dariya Feedo, Ruky, Bintu suka kwashe da shi. Yayinda Nimrah taja tsaki. Aunty Asma'u kuma ta tambayesu waye ya kawo?. Labari su Feedo suka bata, har su Mu'azz duk na saurarensu, sai dai abin mamaki duk fuskokinsu sun canja, dan cikin faɗa Khalifa ya ce, “Zamu ci uwar guy ɗin nan kuwa, ƙannenmu da aka tura makaranta ne abin bibiyarsu da soyayya? Dan ubansa aure akace za'ai musu?”.
Cikin ɓacin rai Imam ya ce, “Dolene muje har makaranta muja masa gargaɗi kam, wannan ai rashin hankali ne”.
Mu'azz kam daya kume bai iya ya tanka ba, dan fuuu yabar garden ɗin ma. Khalifa da Imam suka take masa baya. Daga haka wasan ya watse. Ammie dake falo sai ganinsu tai suna shigowa ɗai-ɗai. Bata ce da su komai ba dan tana waya da Daddy Imran ne....
Washe gari daga Nimrah har ƙawayenta babu wanda ya sake bin batun litattafan Sayyadi Kamal kamar wancan karo da suka ma barsu a gidan Aunty Mimi. Dan tunda suka tashi ma suka taya masu aiki gyaran gidan da haɗa breakfast. Bayan sun karya kuma sukai shiri wucewa gidan Baffa dan Hajiyar Daddy Imran ta dawo daga ƙauye jiya da yamma. Tunda Aunty Asma'u ta sanar musu sukace yau can zasu yini. Duk da Ammie na son su zauna babu yanda ta iya. Dole ta haɗa lafiyyayen farfesu da kunun aya da kunun gyaɗa tace su kaima Baffah da Hajiyar (Iyayen Imran kenan). Nimrah ce ƙarshen fitowa a ɗakin. Ta kammala rolling veil ɗin abayarta kalar maroon da adon milk da taji stone tana maida kayan kwalliyarsu a make-up kit ɗinsu idanunta suka sauka akan books ɗin Sayyidi Kamal dake zube a side drawer inda tun jiya Bintu ta zube su. Samun kanta tai da ƙarasawa inda suke ta ɗaukesu su duka uku yau dai tana kallo. Zuuu taɗan buɗesu a tare, sai ga wata ƴar ƙaramar takarda ta faɗo a ɗaya daga cikinsu. Takardar tabi da kallo, ganin rubutun jikinta ta kai duƙe ta ɗauka.
_Ba litattafan bane muhimmanci a gareki yau kamar saƙon farko, ainahin saƙon yana a littafi mai jan bango shafi na hamsin da uku da shafi na tamanin, ki tabbatar ke kaɗai kikaga abinda ke ciki batare da kowa ba har aminiyarki, saboda muhimmancin abinda ke ciki da zai amfaneki ke kaɗai. Idan kuma kika bari wani ya gani bayan ke to tabbas zai mutu._
Takardar ta ɗan jujjuya cike da mamaki zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri saboda kalaman ƙarshe, dai-dai nan akai knocking ƙofar ana kiran sunanta. Dan haka ta maida takardar kawai cikin littafin farko tana amsawa da haɗiye abinda ke shirin hargitsa mata brain, sai kuma ta buɗe handbag ɗinta ta saka duka books ɗin a ciki dan basu da wani girma sosai. Haka ta fito zuciyarta na kai-kawo akan abinda ta karanta. Amma da yake tana da wayo sai ta danne ta yanda kowa bazai fahimta ba.
Received at 2:38 Yau kam Yaya Khalifa ne ya kwashe su zuwa can gidan Baffan. Cike da farin ciki suka zagaye nutsatstsiyar tsohuwar mai cike da kwarjinin ibada da lafiyar data haɗu da jin daɗin rayuwa. Hajjo tsohuwa mai ran ƙarfe kenan, mahaifiya gasu Imran da a yanzu ta zama uwa harga su Mammah, sannan kaka gasu Nimrah. Dan dattakonta yasa itama bata san raba ɗaya biyu ba, ta zama ginshiƙin dunƙule familyn nan uku da basu da alaƙar jini a yanzu sunfi ma waɗanda keda alaƙar jinin gina ƙyaƙyƙyawan zuminci...
“Oh ni Bilkisu, yaran nan ina zakuje da girman jiki? Ba'a kauda uwarku Biebah ba balle yayunku amma neman dannesu kuke da girman jikin ku, anya bazance a haɗeku rana ɗaya da Habibah da su Asma'u ba”.
A tare suka gwalalo mata idanu, cike da shagwaɓa har suna haɗa baki wajen faɗin a'a gaskiya su auren su sai sannan da shekara goma.
“Shekara goma? Kuji min shaƙiyan yara, sannan kuma in sha ALLAHU ai sai dai lissafin auren ƴaƴanku. Ni yanzu kunga tunda gaku ku duka huɗun yau ba lalaci da surutu zaku yimin ba. Tashi zakuyi kumin kwalemar ɗaki a fitar da komai a canja min jere na, dama su Asma'u zance suzo suyi, amma tunda gaku shike nan sun huta”.
A tare suka amsa mata da to. Sai kuma Nimrah da duk bata da kuzari ta ce, “Granny ina Baffa wai?”.
“Naja'atu sun fita shi da baban ku Ammar, dan kamar ma suna can gidan kakanku Nasiru. Amma nasan anjima kaɗan zasu dawo”.
Kai Nimrah ta jinjina, har sun miƙe Hajjo dake binta da kallo ta kira sunanta, juyowa tai, sai kuma ta tako inda Hajjon take. Sai da ta kama hannunta ta zaunar kusa da ita sannan taima su Fiddo da suka tsaya suna kallonsu alamar suje su. Basuyi musu ba suka wuce hanyar bedroom ɗinta. Ita kuma ta maida hankalinta ga Nimrah.
“Naja'atu mike damun ki? Ko baki da lafiya ne?”.
Sai da gaban Nimrah ya faɗi, dan bata taɓa zaton wani zai gane halin da take ciki ba. Amma sai tai ma Hajjo murmushi da girgiza kanta. “Ba komai Granny, mi kika gani?”.
Hajjo dake kallonta cike da nazari ta ce, “Ban yarda ba Naja'atu, nafa san halin kowa a cikinku, ko yaya kuka canja kuma ina ganewa.”
Har Nimrah ta buɗe baki zatai mata bayanin abinda ta gani a takardar nan sai kuma ta tuna kalaman ƙarshe na cewar duk wanda ta bari ya sani zai mutu, da sauri ta canja zancen tana kwantar da kanta jikin Hajjo ɗin. “Granny da gaske ba komai. Kawai dai yau na tashi ne duk zuciyata wani iri ba daɗi, kuma gabana nata faɗuwa”.
Ajiyar zuciya Hajjo ta saki a hankali, sai kuma ta shafa kan Nimrah ɗin cike da lallashi da so da ƙauna ta ce, “Ki yawaita ambaton Hasbunalahu wani'imal wakil da talatin ANNABI kinji. In sha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Barsu ma suyi aikin muyi hirar mu”.
“Granny zan taya su ina son nima nayi. Amma kin zo mana da farar mu?”.
“Buhu guda ma kuwa, tana nan a store dama in baku zo yau ba zan bayar a kai muku, damma na manta ne da A'isha tazo ɗazun ita da Bilalu ban basu ba”.
Farin ciki sosai ya bayyana a fuskar Nimrah, sai kawai ta nufi ɗakin Hajjo tana ƙwalama su Ruky kira. Da kallo Hajjo ta bita tana murmushi, dan har cikin ranta take ƙauna da tausayin Nimrah.......
<•><•><•><•><•><•><•>
★ SECRET MEDICAL BASE ★