← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 47

Sashe 45

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Yanda Imran yake a ruɗe ko damuwa da kallon lokaci baiyi ba ya dannama shugaban ƙasa kira. Cikin sa'a kuwa ba a jima ba aka amsa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin yay sallama. Daga can shugaban ƙasa da alamu ya nuna barci yake ya amsa, duk da dai a cikin murya mai nutsuwa ne.
        “Imran.”
     “Ranka ya daɗe ka gafarce ni na tashe ka a barci bazan iya haƙuri bane shiyyasa ko lokaci ban damu da dubawa ba na kira ka.”
       “Karka damu Imran nima barcin ya ɗauke ni ne kawai batare da na shirya masa ba. Nima ina son kiran naka a daren nan ai. Amma minene ya tada maka hankali haka?”.
Received at 2:38 PM      Shiru kaɗan ya biyo baya Imran ya gagara magana saboda abinda ya toshe masa maƙoshi. Shima sai Shugaban ƙasa bai iya yace komai ba yana dai saurarensa cikin shiru, irin shiru na masu fahimtar juna ba tare da doguwar magana ba. Tsohon minti guda Janar ya katse shi da faɗin,
      “Ka samu abin da ka je nema ne Imran?”
   Imran ya sauke numfashi karo na farko a hankali. Muryarsa da ɗaci ya furta, “Eh, ranka ya daɗe. Amma abin ya fi yadda muke zato nauyi.”
       “Faɗa min kawai”.
   “Akwai guba a jikinsa. Ba ta gaggawa ba, amma an tsara ta ne don ta lalata shi a hankali. Likitoci sun tabbatar da cewa a nan ba za a iya magance ta gaba ɗaya ba, koda akwai makarinta zai iya kasancewa a hannun wanda sukai aikin yake ko suna da alaƙa da wanda suka yin, dan dole mai makarin shike da gubar. Fitar mu nemata zai basu ƙofar sanin sirrinmu”.
      Shiru ne ya sake biyo bayan bayanin Imran ɗin. Dan Janar ya kasa koda motsin kirki tsabar yanda zancen ya buge shi shima. Imran ya san wannan shirun na Janar shiru ne na mutum da ke ƙoƙarin riƙe fushinsa  shima, dan dole Janar zai ji kamar yanda suka ji a lokacin da Doctor ke sanar musu.
      “A wajen akwai maganin? ta hanyar da muke buƙata?”.
    Janar ya faɗa cikin wata irin murya mai bayyana ɗaci da zafi.
      Amsa Imran ya bashi, “Akwai, ranka ya daɗe. Amma zai iya ɗaukar wata ɗaya zuwa biyu inji Doctor.”
       Muryar Janar ta sauya kaɗan zuwa matsayin shugaban ƙasa, cikin nauyin umarni ya furta. “Amincewar UBANGIJI kawai muke nema. Amma babu wanda zai ji wannan har Haysam.”
     “Mun riga mun kulle komai Sir.”
“Zan zo yanzu. Ina son na gansa.”
Imran bai yi mamaki ba, dan haka kai tsaye ya ce. “Muna maraba da zuwanka ranka ya daɗe.”
      “Uhhm”.
   Janar ya faɗa yana yanke kiran.........✍️
Received at 2:38 PMKIƊA A RUWA 2

43

........Shima Imran lumshe idanu kawai yayi a wajen yana jingina da kujera. Ya san wannan ganawa ba ta siyasa ba ce, ganawa ce ta gaskiya, ta amana, ta zumunci, ta yarda da bashi na tarihi. Ciki ya koma ya sanar ma Faro, dan haka suka nufi ɗakin da Dada yake duk da su a zatonsu har yanzu barci yake.....

    ★2:42am★

          Shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida suka iso cikin base ɗin. Fita ce ta sirri dan a cikin ɓadda kama ma yake. Dan haka daga shi sai dogarinsa ne a motar. Su Imran dake faman zaman jiran tsammani na zaune a falo dan tunda suka leƙa ɗakin Dada suka samu yana barci har lokacin basu zauna ba suka sake dawowa falon. Sai dai abinda basu sani ba likimo Dadan yay musu yana jin motsin shigiwarsu a lokacin, baya son su san yasan abinda suke ɓoyewar, dan haka yay likimo ɗin.
       Shigiwar Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ba tare da hayaniya ba ya sakasu miƙewa tsaye a tare. Basuyi mamakin ganinsa a shigar ɓadda kamar ba, kuma ba tare da yan rakiya ba sai dogarinsa kaɗai. Sai da ya zauna, dogarin nasa ya juya ya fita a falon sannan yay musu nunin su zauna suma.
      Kawuna suka jinjina cikin girmamawa, sannan suka zauna suna gaishe shi. Da kai kawai ya iya amsa musu. Daga haka shiru ya biyo baya na tsawon sakanni kaɗan, babu wanda ya yi magana kowa da abinda ke a ransa.. Janar ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Yana ina?”.
     Ƙofar ɗakin da Dada yake Faro ya nuna masa. “Ranka ya daɗe yana ciki yana barci”.
     “Muje in gansa”.
Ya faɗa yana miƙewa. Suma duk miƙewar sukai. Imran a gaba Janar a tsakkiya sai faro ƙarshe. A mamakinsu suna shiga da sallama suka samu Dada a zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe. Da ɗan sassarfa Imran da Faro suka ƙarasa garesa har suna haɗa baki wajen tambayar, “Ka tashi?”. Idanun sa dake lumshe ya buɗe a hankali ya sauke a kansu. Sai kuma ya jinjina kansa yana maida dubansa kan Janar. Yanda Janar ɗin ke kallonsa ko ƙyaftawa babu ya saka Dada sakin ƙaramin murmushi a karo na farko, sai kuma ya fara ƙoƙarin yaye blanket ɗin da yake ciki cikin nutsuwar sa. Karo na farko shugaban ƙasa ya matso gaban gafon, tsayawa yay a gabansa sosai yana mai dafe hannunsa da girgiza kai alamar kar ya sauka. Nan ma murmurshi ƙarami Dada yayi. Sai kawai Imran ya gyarama janar kujera a gaban gadon suka fice shi da Faro a ɗakin tare da rufe musu ƙofa...

       Janar yakai zaune, har lokacin hannunsa na riƙe dana Dada tamkar mai gudun ya ɓace masa, murya ƙasa amma da nauyin fitar sauti ya furta, “Na yi maka laifi. Haysam”.
        Dada ya ɗan murmusa, murmurshi irin na dattako da kamewar nutsuwa, sai kwarjininsa ya sake bayyana da cikar kamala. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya furta, “Ranka ya daɗe, bazaka taɓa zama mai laifi ba a wajena. Duk abinda ka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce, sai dai idan tazo a mummunar ƙaddarar saɓama UBANGIJI wannan kam daga mu ne da jagorancin shaiɗan. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ina kuma tayaka murnar tare da addu'ar baka ikon sauke nauyi da haƙƙokin al'umma. ALLAH yasa baka cikin shugabannin da zasuyi dana sanin samuwar mulki a garesu a ranar rarrabe ayyuka”.
      “Amin ya rabbi Haysam na gode sosai. Sai dai ka sani shi gudanar da wannan mulkin namu ne a tare, dan kana da muhimmanci a cikinsa wajen sauke nauyin haƙƙin al'ummar ƙasar nan. Shiyyasa nake jin kaicon kaina na kasa kare ka da nayi a shekarun baya.”
     Dada ya sauke numfashi, kafin cikin nutsuwa irin tasa ya furta, “ALLAH ya fi kowa iko. Shi ne Alƙali mafi adalci. Wannan rubutacciyar ƙaddara ce tun daga alkalamin farko. Sir ka daina damun kanka”
       Kai Janar ya jinjina yana sauke numfashi mai nauyi, tabbas ya yarda ilimin addini duniya ne, wanda ya samu wannan ilimin yay kuma aiki da shi ya more, dan kasancewar Haysam a yau ya tabbatar masa da hakan. Sake duban Dada yayi cikin katsewar tunani ya cigaba da faɗin, “Na zo ne ba a matsayin shugaban ƙasa kawai ba. Na zo a matsayin soja… a matsayin mutumin kuma da ke bin ka bashi.”. Ya ɗan dakata, yana kallon idanuwan Dada kai tsaye. “Akwai guba a jikinka Haysam.”
Received at 3:59 PM      Dada bai nuna mamaki ba, sai ma murmurshi da ya saki da ɗan taɓe baki kaɗan ya ce, “Na fahimta tun kafin likitoci su faɗa.”
     Shugaban ƙasa ya ɗan zuba masa ido da jinjina baiwar da ALLAH yay masa, irin su Haysam wata ajiyar ALLAH ce a cikin al'umma da sai mai hankali ke fahimta, kaɗan ya ɗan murmusa shima cikin baƙin ciki da ɗacin murya ya furta. “Har yanzu kai ne Zak-Shadow ɗin da na sani Haysam. ALLAH ya cigaba da ɗaga darajarka da baka kariya, UBANGIJI ya cigaba da ɗora nasararka akan maƙiyanka?”. Ya ɗan yi shiru na sakan biyu har Dada ya samu damar motsa lips ɗinsa kaɗan wajen amsawa da amin.
        “Ba zan iya barinka a nan ba. Za ka tafi waje. A ɓoye. Ba suna, ba matsayi, ba labari kamar yanda muka fara ka ƙarasa jiyyarka a can”.
      Dada ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya furta, “Zan je. Amma ba dan tsirana kawai ba. Sai dai ina kewar Mammah da son ganin su”.
     “Na sani Haysam. Amma kayi haƙuri bana son kowa naka ya ganka a cikin wannan halin, in sha ALLAHU wata biyu tamkar gobe ne indai da rayuwa. Mammanka zatafi farin ciki da son ganin Haysam. Saɓanin hakan raunana mata zuciya zaiyi daga ita har ƴan uwanka. Ka duba halin da Imran ke ciki a yanzu haka kawai ya isa misali”.
      Cike da gamsuwa Dada ya jinjinama shugaban ƙasa kai. Kafin cikin ɗan furzar da iska ya furta, “Zan dawo in sha ALLAHU. Ba a matsayin wanda aka yima afuwa kawai ba. A matsayin wanda ya dawo ya gyara abin da ya samu karaya daga BURINSA.”
      Da ƙarfi Shugaban ƙasa ya sauke ajiyar zuciya yana miƙa masa hannu. Kama hannun nasa Dada yayi sukai musabaha irin ta amintattun sojoji masu kishin ƙasa da tsayayyar zuciya, musabaha ta tarihi, ta alƙawari da cikakkaiyar JARUMTA.
      Janar dake murmurshi ya furta, “Ina ji a jikina Haysam, da izinin UBANGIJI a ranar da ka dawo ƙasar nan zata fara canjawa da canji irin na masu son a shinfiɗa gaskiya. Da taku irin na masu girgiza zukatan ɓoyayyun munafukai. Daren gobe in sha ALLAHU zaku wuce”.
       “ALLAH ya kaimu”.
   Dada ya faɗa......

=================
Chapter 45 · 0% Book details