← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 47

Sashe 43

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     ★ Anan falo kam bayan wucewarsu Aunty Mamawo ta furzar da iska mai zafi tana kallon Hajiya Hasiba. Ta ce, “Aunty tunani ko damuwa bazata kaimu ko ina ba. Kawai muje wajen wani mutimina, shima yana ƙoƙari ya iya aiki, da rafanai yake aiki na tabbata zai mana nasa ƙoƙari kafin muje India ɗin. Dan dole gaskiya muyi wani motsi a wannan gaɓar, dan ina ji a jikina shirun Adeel bazai zama alkairi ba”.
         “Kina ganin zamu samu mafita kuma?”.
      “Tabbas Aunty, dan na yarda da aikin Malam Ƙolo sosai”.
    “To shike nan muje ai kawai mi zamu jira. Dan mutumin nan na tabbatar shima yana can ya bazama hanyar samun damar ganin Haysam, dan gaskiyarki kam shirunsa bazai zama alkairi ba.”
         “Wlhy ni wannan bai dameni ba Aunty, idan ma ya saka an kashe shi matsalarsu ce. Miye amfanin wani Haysam a rayuwar Nabeeha, banda soyayyar wahala da take masa ma. Garama ya kashesa ta samu wanda ya fisa koda ace zata bar Adeel ne, idan ma babu wata illar da ita First lady ɗin ta ambata ba shike nan ba. Dan ni ban yarda ma da matar ba kin san dai mutane da baƙar hassadar tsiya a wannan zamanin. Kowa yafi son ace shi shine kai kana ƙasanshi kana masa bauta bare ma manyan ƙasar nan”.
      “Mizai hana nayi hakan”.
  “Yanzu yanzu fa. Ko zaka kira abokinka ne Ammar?”.
      “Kodai kayi haƙuri zuwa anjima, kuma ba Ammar ya kamata a tambaya ba dan kar ya zargi wani abun tunda mun samu ya fara sakin jiki damu.”
           Ji Adeel yay kamar yace bai yarda ba, amma sai ya daure dan baya son Yohan yaga zalamarsa a fili da yawa, har ya kawo masa raini dan har yanzu bai san shi ɗin waye ba. Kuma baya son ya sani har ya gama abinda ya kawo shi ya bar ƙasar nan. Duk da yau da safe yaga saƙon Ummu ɗinsa ta Email akan tana son ganinsa da gaggawa, ya tabbatar koma miye take nemansa a kansa ba na wasa bane. Kuma dole ya amsa wannan kiran dan baya tsallake maganar iyayensa.....
      Bai sake magana ba sai ma barin wajen da yayi ya koma kan kujerar da take a balcony ɗin ya zauna zuciyarsa fal abubuwa. Dan gaba ɗaya yarinyar can ta rikita masa lissafi ko zancen abinda ya kawo shi ƙasar nan bai sake waiwaye ba. Kai su kansu su Hajiya Hasiba ɗin tunda suka iso bai bi takansu ba, sai ma da yaga Nabeeha yanzu ya tuna da al'amarinsu...........✍️KIƊA A RUWA 2

41

........Da ƙyar Daddy Imran ya iya fisgo kalma ɗaya wajen furta,
“Wace irin guba ce?”.
“Slow-acting toxin. An tsara ta ne don ta lalata jiki a hankali ba kashewa nan take ba. Hakan na nuna wanda ya aikata ya so yaga yana rayuwa cikin rauni ne.”
Shiru ɗakin yay dan kowa da kalar da raɗaɗin da zuciyarsa ke masa akan jin wannan baƙon al'amari mai rikita lissafi. Suna cikin farin cikin babu wani damuwa a tare da Dada a kwaje-kwajen farko, ashe tashin hankalin na gaba. Da ƙyar Faro ya yanke shirun nasu.
“Doctor yanzu minene mafita? Tana da makari ne?”.
Doctor ya ɗan gyaɗa kansa. “Tabbas za'a iya samun makarinta, abin da ya rage mana shi ne inda zamu same sa, musamman a ƙasar nan tamu kuma da bana jin zamu samu ɗin kai tsaye, idan ma mun samu hankalinmu bazai kwanta ba ga duk wanda zai bamun. Dan duk wanda ya samar da gubar dama dole shine mai makarinta. A yanzu kuma mu kowa ba abin yarda bane a wajenmu. Musamman tunda bamu san wanda ya aikata masa haka ba. Sai dai mubi wata hanyar sirri da cikakken tsaron da zamu fitar da ita gaba ɗaya.”
Imran ya ɗago kansa ya zuba masa idanunsa da suka juye jazur. Kai tsaye ya furta, “Waje ke nan?”
“Tabbad Sir! Asibiti na musamman a waje ya kamata mu kaishi. Zaman wata ɗaya zuwa biyu. Idan aka yi hakan da wuri zamu tsare rayuwarsa da cikakkiyar lafiya.”
Komai Imran bai sake cewa ba, sai ma ya tashi tsaye a hankali, sai dai nauyin abin da yake ji ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa da kuzarin jikinsa. Ɗan juyowa yay ya kalla Doctor ɗin, cike da gargaɗi ya furta, “Babu wanda zai san wannan bayan mu ukun nan.”
Dr. Idris ya gyaɗa kai da girmamawa. “Mun riga mun ɗauki rantsuwar sirri ai Sir.”
Imran ya juyo ga Faro, idanuwansu suka haɗu a waje guda. “Zan sanar da shugaban ƙasa yanzu.”
Faro ya ɗan murmusa da gyaɗa kansa, sai dai murmushin da ke ɓoye fushi. “Ka sanar da shi. Amma ka faɗa masa gaskiya ɗaya: Zak-Shadow bai fito daga prison don ya mutu a asibiti ba.”
Imran ya gyaɗa kansa yana ɗaukar wayarsa, harya fara tafiya ya tsaya a ƙofar ɗakin, a taƙaice ya furta “Ba zai mutu ba in sha ALLAHU.” daga haka ya fice ya bar Faro da Doctor Idris na cigaba da tattaunawa.

Dada da basu san duk ya gama jin abinda basa son yajin ba ya bar jikin ƙofar yana murmurshi. Drip da ake faman saka masa a kwanakin nan dama doctor ɗin ya saka masa bayan sallar isha'i, shine ya saka shi barci har su Imran ɗin suka shigo gidan bai sani ba. Yanzu ma ya farka ne sai yaga ruwan ya ƙare ya cire da kansa, ruwa da yake buƙata na sha daya duba babu a ɗakin ya saka shi ƙoƙarin fitowa duba Dr Idris ɗin, dan koda yaushe Doctor na tare da shi a gidan. Barin wajen yay ya koma ya zauna a bakin gado. A zuciyarsa yana faman maimaita kalmar poising ɗin, sai dai fuskarsa da murmurshi, dan ya jima da fahimtar hakan a tare da shi, musamman a watannin nan da suka gabata. Har ma yana tunanin yaushe hakan ta faru? Tun yana a prison ɗin, dolene a ɗayan biyu gubar ta shigesa. Mafi ƙarfi a zuciyarsa shine television da aka kawo ɗakinsa watannin da suka wuce, ko kuma ta hanyar securitys ɗinsa......

%★%★%★%★%

A ɓangaren su Hajiya Hasiba kam abinda suka jiyo ga bokan Mamawo ya matukar rikitasu, amma sai Hajiya Hasiba tace ita dai su sake zuwa wajen wani mana. Ko suje India ɗin kona kwana biyu ne.
Mamawo ta yarda da shawarar, amma tace su fara fuskantar Adeel. Itama Hajiya Hasiba bata musa batun ba, sai dai sun nema ganin Adeel ɗin shi kuma ya toshe hakan. Dan yama ɓoyema ganinsu gaba ɗaya dan haka dole sukai hakuri dan zuciyarsu na kitsa musu ko wani abu yake shiryawa. Ga First lady ta takurama Hajiya Hasiba akan harkokin bikin ƴarta, dole ta haƙura da batun India ɗin ta maida hankali a kanta. Har takai ma bata fahimci Ismat bata gida ba sai bayan kwana biyu. Sai dai tana taɓota tace tana gidan Aunty Jiddah zatai kwana biyu sai ta saki batun ta. Dan bata kawo a ranta wani abu Ismat ɗin ke shiryawa na komawa gidan babansu ba.
Received at 2:37 PM Ita ko Nabeeha tunda suka baro gidan Mammah a waccan ranar al'amarin Nimrah ta ɗauka ta saka a zuciyarta dan girman yarinyar ya tayar mata da hankali matuƙa. Tun tana ɗaukarsa ƙaramin abu har yake neman zame mata ciwo a kwanakin gaba ɗaya bata jin daɗin ranta dama jikinta duka. Babu abinda take saƙawa sai yanda zatai da Nimrah. Wannan ya ɗauke hankalinta itama bata shiga sabgar kowa da komai na gidan.
Su kuma su Amima holewarsu suke hankali kwance da yawon tsiya ita da Rayhana kullum. Dan uwarsu ta tsaya musu.....

<<%>><<%>><<%>>

“Waye shi wannan?”.
“Wani yaro ne malamin islamiyyar su. Gaba ɗaya alamominsa sun nuna sonta yake yi. Dan haka da shi ya dace muyi amfani wajen yi mana wannan aikin. Saboda gidan tako ina zagaye yake da ƙyamarorin zamanin nan. Sannan kamar yanda na sanar maka ranar da gaske sun mantar da ita asalinta, su kaɗai take ma kallon iyaye a yanzu.”
“Da gaske mutanen nan shu'umai ne fa Mole, wannan halayyar a jininsu take ba Zak-Shadow ɗin bane kawai shege”.
“Zan tabbatar musu mun fisu shu'umci, ba laifinsu bane kuma. Laifin Hafsatu ne data ɗaukar min yarinya ta bashi. Kuma ta godema ALLAH data mutu, dan da ace tana raye har yanzu, sai na ɗanɗana mata fiye da abinda take tsammani na azaba a tafin hannunta duk da son da nake mata”..
“Mole manta kawai, wauta ce irin ta mata da zigar ubanta. Ba gashi sun kuma ɗanɗana daga hukuncinmu ba yanzu sai labarinsu. Yanzu shi wannan yaron mai gemu kamar jelar tsatso ya za'ai yazo hannun mu? Dan su Oga sun ce muyi faka-faka babu ɓata lokaci muna buƙar yarinyar mu Nimrah tai mana aikin nan da gaggawa ta dawo hannumu.”
“Karka damu wannan duk mai sauƙi ne. Dan tana nan da halin nan nata dana santa da shi har yanzu. Na tabbatar idan taga videon nan kodan son da takema uwarta zata dawo hankalinta. Ballema idanunta ya sake buɗewa yanzu tayi karatu. Kamar yanda kace babu ɓata lokaci kawai saƙon nan na farko ya dace ya fara riskarta, dan yaran ya sanar min watannin baya ya aika mata ƙyautar litattafai, kaga sai muyi amfani da wannan damar nake ga ko.”
“Hakan yayi, zan saka a cikin satin nan a sace min yaron. Amma fa kaima sai ka sake kula gaskiya. Dan Imran ɗin nan na tabbatar shegen kansa ne zuwa yanzu. Duk da dai a zahiri baya wani abu da zai tada mana hankali, ina jin tsoron shiru-shirun sa”.
“Ni ko kaga bana wani tunani mai girma a kansa, saboda uban ƴan taurin kan can shi ne ƙarfinsa, rashin sa a kusa da shi kuma duk ya sake rage masa kuzari.”
“Kai ma kayi magana ta gaskiya. Amma duk da haka kada mu sakankance. Bari naje dan asuba ta gabato. Sai na jika”.
Sunyi sallama Dagger ya bar gidan, dan gida ne dama na haya mai mutane da yawa Mole yazo ya kama ɗaki. A yanda yake kuma baka isa kace yana da wata suffa ta mutanen banza ba. Tsabar iya taku ma jama'ar gidan da sunan Malam suke kiransa......

<<<<<✷⁠‿⁠✷>>>>>
Chapter 43 · 0% Book details