← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 47

Sashe 26

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

★ Sai sha biyu su Nimrah suka tashi da ƙyar, shima sai da Mammah tazo da kanta ta tashesu. Dan suna yin sallar asuba suka koma gado. Aiko sai shagwaɓa suke mata wai ta barsu sai ƙarfe ɗaya sannan.
“Shike nan kun fasa zuwa gidan sunan kenan? Ai da nasan haka ne sai na tadaku kun wuce Tahafiz. Ga ƴan Bauchi can tun sha ɗaya suka iso ku kuna nan kuna barci”.
Tuni duk suka watsakke, cike da farin cikin jin zuwan ƴan Bauchi. Zasu nufi ƙofa a guje Mammah ta dakatar da su. “Kai kuji min ƙazaman banza. Haka zakuje musu da kayan barci? Ba brush kamar wasu ƙazamai. Maza ku koma ku gyara jikinku, wata taje ɗakin Biebah yanda zakuyi sauri”.
Received Cike da farin ciki sukace to. Mammah ta fito tana murmurshi. Koda ta dawo falon wajen su Gwaggo Alawiyya ta samu su Ma'aruff sun iso gidan. Dan tun ɗazun ta sanar musu sukace zasu zo yanzu. Sai ko gasu da ledoji niƙi-niƙi na kayan ciye-ciye. Fuskokinsu washe da murmushin ganin gwagwgwannin nasu. Badiyya na sinƙe-sinƙen kai ganin yanda suma basu nuna mata komai ba kamar Mammah sai ta ware aka fara gaisuwa da tambayar yara. Yaya Ja'afar ya ce, “Haba Gwaggo, kwa taho ku kaɗai duk babu yara? Bayan kun san ba ganin juna ake ba tsahon lokaci sai irin haka ta faru”.
“Makaranta tasa haka Ja'afar, amma in sha ALLAHU idan anyi hutu sai su zo. Tunda kudai kun tattaramu kun watsar, yaushe rabonku da Bauchi balle Maiduguri?”.
“Dama idan sunje Bauchin ba ganinsu muke ba Adda Khadijah, iyakarsu gidan Yaya Jamilu da Adda Alawiyya. Dan nidai sau biyu suka taɓa zuwa min lokacin rasuwar Inno surukata, da ciwon Ahmadi”.
“Munyi laifi Gwaggo Nanah, amma kiyi haƙuri zamu gyara in sha ALLAHU. Wani lokacin abubuwan ne ke yawa. Mafi yawan lokuta kuma zuwa Bauchin kasuwa ke kaimu. Ki tambayi Aunty Badiyya sau da yawa shima Uncle Jamilu a kasuwa muke samunsa ba gida muke zuwa ba. Itama Gwaggo Alawiyya takan jima bata gammu ba. Maiduguri ne dai kam ma zamuce muna shiga dan ziyara kai tsaye”.
“To na gamsu, amma dan ALLAH a gyara, mun san mu masu kuskurene a gareku, amma kuyi mana afuwa kunji, Yaya Abdul-rasheed mutum ne mai son zumunci da Adda A'isha da Adda Yakura, na tabbatar kuma akwai wanan jinin alkairin nasu a tare daku, kar ku biyema aikin son zuciyar wasunmu ku watsar damu gaba ɗaya. Suma lokaci zai yi da zasu yi nadamar abinda suka shuka. Dan har ma wasu sun fara, Yaya Babba a tsakanin nan babu abinda yake sai tafka asarori kala-kala, ga yara cike da gida, mata har huɗu. Yaya Haruna ne ma za'ace da ɗan sauran damshi-damshi. Shi ko Yaya Garzali ma yaje ya tare saudia aikatau ƙiri-ƙiri ko takan matan baya bi sai ya gadama.”
Sosai zancen ya girgiza su. Sai dai basu ce komai ba face ALLAH ya ƙyauta. A haka Ammar ya shigo shima da Mu'azz. Nan fa falon ya sake lacamewa da farin ciki. Sai kuma gasu Nimrah na fitowa cikin kwalliya tsaff suna baza ƙamshin turaren da suka satarma Aunty Biebah na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Cike da farin ciki suka rungume Gwaggo Alawiyya da Gwaggo Khadijah dan su suka sani sukam. Abin birgewa bazaka taɓa cewa ba jininsu bane su. Sun gaida su Gwaggo Nanah suma. Suka amsa musu da kulawa duk da basu san alaƙarsu da gidan ba. Garama Fiddo ƴar Aunty Mommy data kwana a gidan itama, tunda sun jajje Bauchin ita.
Gwaggo Khadijah ta ce, “Oh ni Dije Maman Ma'aruff ƴan matan nawa duk sun miƙe. Kaga yara kamar wasa sun ƙosa. A wannan sai aure”.
Caraf Mu'azz ya ce, “Tab ɗin wazai kwasa Granny? Wannan gayyar ciwon kan da basu iya komai ba sai dambe da neman masifa da ƴaƴan mutane”.
Baki duk suka tura gaba. Gwaggo Khadijah ta ce, “Kunga ƙyaleshi ƴan uku Ko nace ƴan huɗu dan banbu Bintu ne. Ai ana yin auren duk zaku daina ko. Kuma dai ai kowa da ƙuruciyarsa, shima idan za'a faɗi abinda yayi ai sai kowa ya gudu”.
Dariya suka shiga yima Mu'azz suna masa gwalo, shiko yana hararsu da musu alamar zai kama su. Su Yaya Ma'aruff dai na murmurshi ne, Yaya Ammar kam dining ya nufa yana faɗin shifa yunwa yake ji, mi aka dafa ne?. Miƙewa su Nimrah sukai suma suna faɗin yunwar suke ji. Daga haka suka koma kan dinning ɗin harda su Mu'azz aka bar su Yaya Ja'afar suna hira da su Gwaggo Khadijah.....

<<%>><<%>><<%>>

Da yamma shagalin suna aka sha sosai a gidan Aunty Mimi, duk da kuwa haihuwa ce ta huɗu tayi. Babu ƙarya su Nimrah sun cashe da rawa iya iyawarsu. Kasancewar hall aka kama iyakar kuma mata ne kawai a wajen dan ko su Mu'azz basu shiga ba sai abin ya ƙayatar. Ƙarfe shida aka tashi saboda sallar magriba. Nan fa motoci suka fara ɗibar mutane zuwa gidajensu. Su Nimrah dai yau a gidan Aunty Mimi zasu kwana. Dan haka sukabi ƙanin mijinta da yazo kwasar yaranta dana family ɗin mijinta.
ReceivedDuk da dai da farko ca sukai su bazasu shiga cikin yaran ba, sai da Aunty Shariffa ta fara musu faɗa da tabbatar musu zako ta kaɗa kansu zuwa gida sannan suka nutsu saboda suna son zuwa can ɗin su ƙarasa weekend ɗin su. Ga Bintu kuma ta ƙaru sun zama su huɗu yanzu.
Haneef dake matuƙar son Ruƙayya na sharewa yana faman murmushi yace su jira shi ya kai yaran ya dawo to. Feedo ce ta amsa masa da “To Uncle”. Su Ruky kam aka wani ɗauke kai gefe. Murmurshin shaƙiyanci Nimrah tayi, tare da ɗagama Bintu gira ɗaya cike da gulma. Aiko suka kwashe da dariya. Ruky da tasan da ita suke ta balla musu harara da jan tsaki zata bar wajen Nimrah ta riƙota........✍️
Received at 6:38 PM[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: KIƊA A RUWA 2

27
Chapter 26 · 0% Book details