← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 47

Sashe 47

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

       A yau Adeel ya sake dawowa ƙasar bayan tafiyar kwanaki da yayi amsa kiran mahaifiyarsa. Sai dai masaukinsa na hotel ɗin can ya fara sauka, dan kwana biyu kawai yake ganin zai yi ya sake komawa sai ya kammala uzirin daya taso masa sai ya dawo sannan yayi shirin da yake so. A bazata Hajiya Hasiba da suka samu labarin yaje gida batare da gaya musu ba a bakin First Lady taga kiran nasa a yau. Sai da gabanta ya faɗi, ta daure da ƙyar dai ta ɗaga dan voice call ne na WhatsApp yay mata. Tashi tai a falon dan duk suna zaune ne idan ka cire Mamawo da bata ƙasar ma. Nabeeha na charting da ƙawayenta ne. Su Amima na kallon Film, sai dai hankalin Nabeeha ya rabu ne gida biyu da tunanin hukuncin data gama yanke ma kanta na komawa gidan Abbansu itama kamar Ismat. Dan haka koda taji Momyn tana gaisuwa da yanayin girmamawa taji a ranta Adeel ne, dan duk da tana tare da manyan mutane girman da take bama Adeel da banne dana kowa. Kuma zata iya girme masa, sai dai bazata haifeshi ba a kwatance duk da tayi karatu kafin aure, ita ba'ai mata auren ƙarancin shekaru ba kamar yanda take basu labari........

((%))★((%))★((%))

      Har washe gari duk yanda Nimrah taso samun waya ta saka memoryn nan hakan ya gagara, ba kuma samun wayar ne mai wuya ba, keɓewa gefe ne ta gagara samu. Dan kowa yau na gida su Mammah ce ma ta ɗan fita tare da Uncle Bilal kuma zuwa sha biyu suka dawo. Gashi tana fashin salla. Ruky ce kawai ke shiga yi balle ta fake da wannan. Da dare kuma suna tare da Ruky, bata son fito mata da abinda ke faruwa saboda ance wani zai mutu. Koda Rukyn ta tambayeta ma littafan da Sayyid ya kawo kawai ta nuna mata cewar ta kaisu cikin littatafan su dake shirye a ƴar kanta, wajen yana a ƙasan hannun bene ne matsayin study table ɗinsu.. Ita kuma tana bata labarin yanda sukayi da su Uncle's jiya.
       Nimrah bata samu yanda take so ba sai da kowa ya tafi sallar magriba , ta tabbatar sai isha'i kuma. tana ganin Ruky ma ta kabbara salla ta zare jikinta tabar bedroom ɗin zuwa sama da wayar Mammah a hannu, dan tasan itace zata jima bata fargaba fiye da sauran. A sama a kwai ɗakin kusan ƙarshe da ƙofarsa ta ɗan juya ma nasu Yaya Ammar, shi ta shige. Babu kowa a ɗakin babu ma wanda ya taɓa zama cikinsa. Amma akwai kaya da aka ajiye sai dai komai na a leda a jingine kawai.Ƙaramin table ta jawo duk da akwai ƴar ƙura haka ta zauna ta saka wayar Mammah a plane mood dan karma a kira, ta zare memory ɗin ciki ta saka wanda tun jiya ke maƙale a jikinta. Tana tabbatar da ya hau ta wuce wajen videos kawai. Videos uku ne kacal a ciki, jikinka har rawa yake ta shiga na farko tai playing...........✍️     

Received at 4:00 PM
Chapter 47 · 0% Book details