← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 47

Sashe 13

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

........Shi ma'abocin ibada ne da ƙoƙarin ganin ya kiyaye dokokin UBANGIJI da kusantuwa da shi a lokacin da yake rayuwa kamar kowa. A yanzu daya ɓuya bisa faifan ƙaddararsa da jarabawa da makircin masu makirci hakan bai sauya komai ba. Sai himma da dagiya da hakan ya ƙara masa wajen sake kaɗaice UBANGIJI da bauta. Halin da yake ciki bai taɓa sakawa yaji kasawace ko tauyewa daga UBANGIJIN SA ba. Bai kuma taɓa jin nasara ce ga azzalumai ba. Bai taɓa mantawa da ƙasar da talakawan ƙasar ba. Yanda yakema kansa addu'a da zuri'arsa haka yake addu'a ga ƙasa baki ɗaya.
     Tabbas a siffa ta jikin ƙarfi da ALLAH ya bashi zuwa yanzu ya risina, sakamakon canjawar tsarin abincinsa zuwa zaɓin wanda ake ciyar da shi a yanzu. Shiyyasa ya zaɓi ɗaukar matakin yin azumi yau, gobe ya huta, azumi ibada ce mai girma, sannan kariya ce daga jarabawar ɗan adamtaka ta lafiya da halittun jiki da UBANGIJI ya ni'imata mu da su musamman akan abokan rayuwa. Nauyin jiki da raunanuwar ƙarfi bai sa ya gaza wajen ƙoƙarin cigaba da ƙarfafa ƙashi da tsoka da sauran ƙarfin daya rage masa ba, dan a cikin wannan nan dai tsukun ɗakin da yake ciki yakan gudanar da ibadarsa ya kuma motsa jiki da salo-salo irin nashi. Rashin ƙarfafa damuwa a zuciya, ya bashi kariya daga cututtukan zamani irin su hawan jini balle ciwon zuciyar da maƙiya ke fatar masa a kowane motsinsu. Ya riga ya amince UBANGIJI shine mai komai da kowa, idan kunga alkairi daga gareshi ne, saɓanin hakan daga shaiɗan ne ko halayenku ko jarabawar da zata sake ɗaukaka darajar ku zuwa wani mataki na duniya ko lahira. Yayi imani da hakan shiyyasa damuwa ta kasance abu na ƙarshe da zai iya cewa yana yi. A duk sanda ya tuna da ahalinsa musamman jajirtacciyar uwa irin Mammah, yakan mata addu'a da fatan samun nutsuwar zuciya daga shiga damuwar halin da yake a ciki. Hakama ƴan uwansa da suke masa kallon uban da matarsa daya tabbatar soyayyarsa mai ƙarfi ce a zuciyarta. Hatta ƴar amanarsa tana nan zaune daram a zuciyarsa, yana kuma mata addu'a da fatan rayuwa mai nasarori a yau da gobenta, sai dai daga ita har Nabeeha yana jiran wani lokaci ne da zai sawwaƙe musu suje suma su sake gina sabuwar rayuwar su.
       Bai yanke hukuncin fita a wannan wajen ba, dan bashi da wani tabbacin fitar. Sai dai yana fatan aikin daya ɓuya domin yinsa da hana Imran shiga cikin tarnaƙin su tabbata. Dan in har ALLAH ya bashi tsohon rayuwa a kurkukun nan, akwai matsayin da Imran zai kai a gidan soji da zai sa babu wanda ya isa hanashi zuwa ziyartarsa a-kai-a-kai. Idan kuma har UBANGIJI ya bashi damar cika shekarun da suka ɗiba masan ya tabbatar lokacin da zai fita koda bashi da ƙarfin jiki dana aiki, yana da zuciyar bin waɗan can azzaluman ɗaya bayan ɗaya ya hukunta su da hannunsa. Balle ma ko a yanzu ya gama shirya in har yay wasu shekaru a wajen nan sai ya nema hanyar dinga fita yana aiki yana dawowa koda a ƙarshe zai bayyana kansa a ƙarasa yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai koma kashe shi kai tsaye....
       Motsin buɗe ƙofar da akai ya saka tunaninsa katsewa, dan yana duk wannan tunanin ne tare da push-up daya sabama kansa yi sama da ɗaruruwa a kowane rana koda yana azumi. Dan haka har yanzu jikinsa a bubbuɗe yake sai dai raguwar ginanniyar tsoka da bata samun sinadarin da take buƙata kamar baya. Daga yanda yake push-up ɗin kawai ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla yaran sojin guda biyu ya janye yana cigaba da abinsa.
     Suma sake nutsuwa duk sukayi, dan su sun san badan zaki na keji ba basu isa ziyartar ko gefen dajin da yake farauta ba. A tare suka ƙame tare da yin salute ɗinsa, kafin na gefen damarsa ya furta, “Sir kana da vistor ne”.
      Cak ya ɗan tsaya na sakan, sai kuma ya cigaba da abinda yake batare da yace da su komai ba. Fin mintuna uku, dan har sai da ya cika adadin da yake buƙata kafin ya tashi da ƙyau tamkar ba shi ya gama push-up ɗin ba yaja ƙaramin towel dake jikin ƙarfen gadon kusa da sallaya ya fara goge hannunsa zuwa wuyansa. Sanye yake cikin uniform ɗin prison ɗin, amma hakan bai hana su kasancewa fes ba alamar baya barinsu da datti, sai dai sun koɗe sosai alamar tsufa da gajiya.
Receive[01-16, 11:37] +234 703 449 6321: A karo na farko ya furta, “Tsawon shekaru biyar kenan a tsarin jadawalin da doka ta sharɗanta a kaina No visitors, no communication. Miya canja hakan a yau daga dokar?”.
     Sake duƙar da kawuna sukai, kafin ɗayan yay magana cike da girmamawa. “Sir muma bamu sani ba. Umarni kawai aka bamu na zuwa da shi inda kake”.
      Idanu ya zuba musu sosai su duka biyun. Wani ɗan murmurshin gefen baki da shi kaɗai yasan yayi kayansa yayi. Ya ajiye towel ɗin a kan ƙarfen gadon ya taka a nutsensa cike kuma da tafiyar nan tasa ta nutsuwa, dattako zuwa gabansu bayan ya saka slippers a ƙafarsa.
       “Ku aikata aikin soja, Captains. Na fahimta.”
     A tare suka sara masa, zukatansu na sake jin rauni, ƙaunarsa da girmamawa.
    “Sir… I’m sorry.”
Suka sake faɗa a tare. Bai ce da su komai ba face miƙa musu hannayesa duk biyu. Dan doka ce fita da shi sai da handcuffs. Jikin sojan har ɗan rawa-rawa yake a ƙoƙarin ɗaura masa handcuffs ɗin, haka dai ya gama suka koma gefe suka bashi hanya. Shine ya fara fita sannan suka bi bayansa har ɗakin ganawar. Vistor ɗin nasa ya juya baya, dan haka bai fahimci ko wanene ba sai da ya zauna a kujerar da aka tanada domin shi.....

<<<>>><<<>>>
   ★EGYPT★
Chapter 13 · 0% Book details