← Book details Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 47

Sashe 24

Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

..........★A falo kam daga Imran har Uncle Nasiru sunji matuƙar daɗin ganin yanda jikin Mammah ya ƙara ƙyau. Da alama ta samu maganin da yafi wanda take samu anan gida. Dan wannan ne karon farko da suka fita Egypt ɗin dama. Kasancewar su Nimrah duk sun wuce islamiyya da ƙyar gidan shiru, dan ca sukai bazasu ba yau suna murnar dawowar Mammah. Sai da Yaya Ma'aruff ya fatattakesu sannan kowa ya wuce baki a sama. Sai Biebah kawai itama bata jima da dawowa daga school ba. Mu'azz yabi Imam gida.
Mammah ta kalla Biebah dake laƙai-laƙai ɗin cin abinci saboda bata jin daɗi yau da ciwon kai ta dawo makaranta ganin Mammah ɗin ne ma ya ɗan watsakkar da ita. Sai dai ganin baƙon dake gidan ya tsaya mata a zuciya kamar sauran ƴan uwanta. Dan yanzu haka ma Aunty Momy da Aunty Ummi da Ammar na ɗakinta suna sake tattaunawa.
“Biebah tashi kira Uncle ɗin ku”.
Idanu Biebah ta ɗago tana kallon Mammah, sai kuma ta amsa da to cikin sanyi tana tashi.
“Kina lafiya kuwa Biebah?”.
Cewar Imran.
Idanunta na cika da ƙwalla ta ce, “Yaya kaina ke ciwo”.
“Ayya Auta stress ne sannu. Jeki dawo kizo kisha magani kije ki ɗan kwanta kafin akkunayen gidan su dawo su hanaki”.
Kai ta jinjina masa. Shima Uncle Nasiru yay mata sannu. Nan ma amsawa tai ta wuce aikar Mammah...

Babu jimawa ta dawo tace yace gashi nan zuwa. Bata zauna cigaba da cin abincin ba ta ɗauka plate ɗin takai kitchen. Koda ta dawo da ruwa a hannunta ƙoƙarin wucewa tai ɗaki. Dai-dai nan Uncle Tasi'u ya shigo falon da sallama. Duk amsawa sukai suna kallonsa. Sai dai zaram Uncle Nasiru ya miƙe yana kallonsa. Shi ko Imran bai san shi ba a zahiri sai labari a sanda wancan abin ya faru, dan haka babu wani alamun mamaki ko damuwa a tare da shi. Sai ma sannu da zuwa da yake jera masa. Sai dai ya gagara amsawa dan hankalinsa shima gaba ɗaya yana kan Uncle Nasiru ɗin ne.
“Tasi'u!”.
Uncle Nasiru ya faɗa cikin matsanancin mamaki da al'ajabi. Karo na farko Tasi'u yay ƙasa da kansa, idanunsa na cika da ƙwalla. Fin sakan biyar kafin ya sake ɗagowa tare da takowa inda Uncle Nasiru yake ƙafafunsa nayi kamar suna rawa. Yana zuwa gaban Uncle Nasirun kawai sai ya zube akan gwiyawunsa. Imran ya zaro idanu waje sosai yana miƙewa, dan zuwa yanzu kam ya fahimci lallai akwai matsala, sannan baƙon yana tare da wani babban al'amari, yo dukda ba yaro bane babba da shi ya durƙusama Uncle Nasiru. Mammah ya kalla, ya ga ta duƙar da ƙai itama kamar mai kuka. Sai shima ya girgiza kansa. Muryarsa a raunane ya ce, “Mammah waye shi dan ALLAH? Naga kuna kama ba ɗan uwa bane ba shin?”.
Ɗagowa Mammah tayi ta kalla Imran tana ƙoƙarin maida hawayen da suka cika mata idanunta. Fuskarta da ɗan murmushi. Babu wani ko ɗar ta amsama Imran tambayarsa. Dan har cikin ranta kallon Imran take dai-dai da su Haysam. Jinsa take tamkar ɗan data ɗauki cikinsa ta haifa.
“Imran Tasi'u ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya. Baka san shi bane saboda wasu abubuwa da suka faru a baya. Amma sun riga sun wuce na yafe masa. Mun haɗu da shi a asibiti nd kwana huɗu kenan.”
Gaba ɗaya Imran sai yaji kamar ma yayi mutuwar tsaye. Ga kukan Uncle Tasi'u daya cika falon. Dan kuwa ya riƙe ƙafafun Uncle Nasiru ne yana raira kuka da kalmomin ban haƙuri kamar wani yaro. Yayin da shi Uncle Nasirun ya gagara sake iya cewa komai yana tsaye kawai shima idanun nasa sun kaɗe jazur.
Kukan Uncle Tasi'u ne ya sakko da su Aunty Ummi. Ko muce Biebah taje ta kirasu dan komai dake faruwa tana kallo daga inda take laɓe. Ammar daya gama kaiwa wuya cikin fushi ya ce, “Ni wlhy wannan drama ɗin ta isheni haka nan.”
Duk juyawa su Mammah sukai suna kallonsu, dan basu san da sakkowar tasu ba. Sai dai kan wani yay magana Aunty Ummi ta ce, “Ba kai kaɗai drama ɗin nan ta isa ba Ammar harda mu ma. Shiyyasa ma su Yaya Ja'afar suka bar gidan, dama kuma jiran zuwan Uncle Nasiru kawai mukeyi muma. Idan Mammah nada zuciyar kawaici da haƙuri mu bamu san wannan ba, babu yanda za'ai maciji ya saremu a bakin rami mu sake maida ƙafarmu da tunanin bazai sake na biyu ba. Ai ko hausawa sunce sanin hali yafi sanin kama.
Received atDan haka Uncle! Yaya kodai ku bashi shawarar ya koma inda ya fito, ko kuma ya nema masauki a wajen wannan gidan magana ta gaskiya”.
Tana gama faɗar haka ta juya zata bar falon tana hawaye. Take mata baya su Ammar sukai suma. Mammah zata dakatar da su Uncle Nasiru ya girgiza mata kai alamar ta barsu....
Dole Mammah tai shiru, shi kuma ya miƙe yana sake faɗin, “Tasi'u tashi muje can gidana, mu basu lokaci nan da kwana biyu.”
Daga shi har Mammah ɗin babu wanda yay jayayya, dan Uncle Nasiru yaya suke kallonsa uwa ɗaya uba ɗaya. Bayan wucewarsu shima Imran bai jima ba ya wuce gida abubuwa da yawa na masa kai-kawo a rai da zuciya......

(((★)))(((★)))(((★)))
★PRISON★
Chapter 24 · 0% Book details