Sashe 1
Kida A Ruwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
[01-16, 11:53 DARMA😍🍬 *_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 2_*
_Chapter 1_
__________________
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D1ZOZr50SfwCQUbhMB0eVC CEO Maryam Tofa 07010346400 inshaAllah zakiyi dariya kayanmu nada sauki da inganci kedai kiyi joining group din don ganewa idonki kaya masu kyau da aminci. Akwai GHT Supplements masu inganci.Allah yasa damu da alkhairi.
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........*_Yau da gobe ita ke canja WANE zuwa WANE bisa yarda da HUKUNCIN UBANGIJI. Ƙaddara ƘAWA ce, kamar yanda JARABAWA ke zama aminiyar numfashi da gangar JIKIN ƊAN ADAM. Idan JIYA tazo da nasara, ba lallai GOBE tazo da nasarar ba. Sai dai hakan baya nufin baza'a sake yin NASARAR ba. Kalubale shike zama tubalin da ke gina mutum har ya zama mai ƙarfi a bayan ƘADDARIRINSA. Sai dai hakan baya tabbata sai idan ka koyi haƙuri. Duk wanda ya koyi haƙuri tabbas zai mallaki rabin nasarar rayuwa. Dan hakuri shi ne ginshiƙin da ke taimakon duk wani buri ya zama gaskiya..._*
Zaku fahimci abinda nake nufi ne kawai idan kuka kasance da littafin *KIƊA A RUWA__MAI* *TADA HANKALIN DODO* _kashi na biyu. Da zai fara zuwa muku_
*_Akwai Audio da zamu fara ɗorawa shima in sha ALLAHU saboda masu ciwon ido da basa iya karatu dama marasa juriyar bibiyar dogayen labaran mu. Shima Audio ɗin zai zo a AREWAPEN, da TELEGRAM akan farashi mai rahusa._*
<<<<<<%>>>>>>
★2016★
Shekaru uku da wasu watanni kenan da kama Zak-Shadow. Abubuwa da yawa sun faru marasa daɗi harma da masu daɗin ta wani fannin. Sai dai rinjayen marasa daɗin ya danne masu daɗin ta yanda har idanu basa ganinsu. Misalta kalar tashin hankalin da su Mammah suka shiga a wancan lokacin ɓata baki ne. Babu irin shigi da ficin da Imran baiyi ba amma ko damar ganin Zak-Shadow an hana musu har na tsawon watanni. Daga baya shima Imran ɗin suka kama shi.
A farko manyan sojoji da yawa sun tsaya akan case ɗin da son ganin abubuwa sun dai-daita Zak-Shadow da Imran sun fito, sai dai daga baya sai suka fara janye jikinsu baya aka bar General Yusuf kawai da gwagwarmaya. Dan har cikin ransa ƙauna ɗaya tak yake ma Zak-Shadow da Imran. Faɗi tashin COAS yasa aka fara shirin miƙa case ɗin kotu, a lokacin Zak-Shadow nada watanni tara a rufe, kuma har lokacin ba'a taɓa barin kowa ya gansa ba sai masu tsaronsa sai shi COAS ɗin kawai.
Kasancewar al'amarin shiri ne na musamman da kowa ya rasa bakin zarensa a zaman farko na kotun aka yanke hukunci. Sun yanke ma Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi hukunci zaman gidan yari na shekara ashirin da biyar, shi kuma Imran Abbas shekara biyar. Ya rabbi wannan al'amari ba zuri'ar Mammah da gidan su Imran kawai ya girgiza ba, ƙasa gaba ɗaya ce ta girgiza, dan a take matasa masu kishin ƙasa da wasu kungiyoyi suka fara zanga-zangar lumana akan basu amince da hukuncin da aka yankema Zak-Shadow da Imran ba. Wannan zanga-zanga taso kawo hargitsi daga baya, hargitsin kuma ba kowa ne ya haddasa shi ba sai ƙungiyar duhu da suka fuskanci ana neman warware musu nasararsu. An saka matakan tsaro masu tsauri daya tilasta matasan komawa gida aka koma ka-ce-na-ce a media kawai, tare da addu'ar neman ɗauki ga UBANGIJI, Sai gargaɗi ga ƴan siyasa akan ALLAH ya kaimu zaɓe na gaba, dan duk mai hankali ya kalli abinda ya farun da idon basira yasan lallai hukuncin nan na siyasa ne kawai...
A ɓangaren Mammah ba'a magana. A wannan karon duk dauriyarta da iya danne abu sai da ta kwanta jiyya, kusan watanta biyu kafin ALLAH ya bata lafiya, sai dai ciwon hawan jini ya riga yayi tasiri a gareta. Hakama ƙannensa da sukafi kowa ɗaga hankalinsu, sai da takai har su Ma'aruff suka ce sun fasa aurensu da ake gaf da yi, amma Mammah tace bata yarda ba bata amince ba. Dan haka tana samun lafiya aka hau shirye-shiryen bikinsu, dama gininsu tun kafin a kama Imran ya dawo da shi anan cikin gidan, bayan an kama shi kuma Uncle Nasiru ya tsaya akai aka cigaba bisa shawarar Mammah. Satin Mammah ɗaya da baro asibiti, da yay daidai da sati biyu ciff da yankema su Dada hukunci akai bikin Ma'aruff da Ja'afar, sai dai bikin baiyi wani armashi ba, dan aure kawai aka ɗaura amare suka tare. Idan ka cire yara irinsu Nimrah dake shagalinsu kowa ƙarfin hali kawai yake, har dai akai aka tashi lafiya...
Kasancewar ba wani taro akai sosai ba gidan shiru babu hayaniya, su Gwaggo Khadijah ne dama kawai sai wasu tsiraru daga mutanen Kano suka zo. Tun bayan sallar isha'i aka maida amare sashensu, dan tunda aka kawosu anan sashen Mammah aka ajiye su sai yau da biki ya tashi. Ganin har ƙarfe goma babu Ma'aruff babu Ja'afar Mammah tai kiran Bilal tana tambayarsa su.
Amsa ya bata da, “Mammah gasu nan fa a ɗakinsu. Da alama kuma basu da niyyar tafiya sashensu. Wanka ma da ƙyar na samu sukayi suka canja kaya”.
Murmurshi Mammah tayi tana ɗan girgiza kai cikin danne damuwa, “Kaga basu wayar”.
Da to ya amsa mata, yana nufar ɗakin su Yaya Ma'aruff ɗin dake jikin nasu shi da Ammar. Sai da yay knocking ƙofar suka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama. Mammah dake saurarensa tace, “Saka wayar a amsa kuwwa”.
Sakawar yay kamar yanda ta bashi umarni, ya sanar mata ya saka. Kai tsaye ta furta, “Ma'aruff! Ja'afar!”.
A tare suka amsa mata, dan suna zaune ne a bakin gado su duka, “Yanzu kuna ganin abinda kuke shirin yi dai-dai ne kenan?. Karku manta yanzu suna da hakki a kanku, ɗaya kuka tauye sai ALLAH ya tambaye ku. Abinda kukeyi bashi zai dawo da Imran da Muhammad cikinmu ba, miyasa bazamu karɓi ƙaddara muyi haƙuri bane. Addu'a itace maganin komai. Dan haka ina baku umarnin tashi ku wuce Bilal da Ammar su raka ku sai da safe...”
Ma'aruff da idonsa ya kaɗe murya a cinkushe ya ce, “Amma Mammah.....”
“Bana son jin komai, ku tashi ku wuce kawai. Bilal kaje kai da Ammar ku rakasu.”
“To Mammah”.
Bilal ya amsa yana share hawayen da suka cika masa ido. Dan Ja'afar ma kuka yake. Haka shima Ma'aruff ɗin gefe ya kauda kansa ya share nashi. Babu abinda ke cizon zukatansu sai tuna yanda suka shirya wannan ranar da ɗokin zuwanta tare da Dadansu da Yaya Imran, amma sai gashi yau anyi komai babu su, kuma suna raye, suna a gari ɗaya amma ƙaddara tai musu shamaki. Ba yanda suka iya dole sukabi umarnin Mammah, dama sunyi wanka, suka shirya cikin kayan barci iri ɗaya dan basa wani buƙatar wasu kaya saɓanin waɗan nan.
Ammar da gaba ɗaya baida isashiyar lafiya tunda aka yanke hukuncin nan nasu Dada da ƙyar ya iya binsu saboda umarnin Mammah. Ma'aruff shine babba, shi suka fara takawa har falon sashensa daya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu abinda ke tashi sai ƙamshin sabbin kaya dana turare da sabon fenti. A ƙofar bedroom ɗin da yake da tabbacin Lailah na ciki yay knocking, bai jira amsarta ba ya buɗe kaɗan ya leƙa. Hangota can a kan katafaren gadon da aka saka mata ya sashi ɗan sauke numfashi, kafin ya buɗe ƙofar gaba ɗaya yana sallama. Bai damu data amsa ba, ya juyo yana kallon su Ja'afar da ke tsaye.
Nuni yay musu su shigo, dan haka suma duk sukai sallama ya amsa sannan suka shiga. A bakin gadon ya zauna kusa da ita, su kuma suka zauna a sofa ɗin ɗakin su duka. Duk da sun girmeta, matsayin ƙanwa take ma a garesu, dan uwa ɗaya uba ɗaya take da Imran, itace autarsu ma. Amma a tare matsayin matar Yayansu a yau suka fara gaisheta.
Da sauri ta girgiza kanta tana share hawaye batare data buɗe fuskarta ba. Dan itama dai irin ciwon dake zuciyarsu shine a tata zuciyar. Cikin rawar murya ta gaishesu batare da ta amsa gaisuwar da su sukai mata ba. Dan kai tsaye ta ce, “Yaya ina yininku”.
Amsa mata sukai da kulawa, kafin Ja'afar yay mata gajeruwar nasiha da addu'a. Shima Bilal yay mata a taƙaice. Ammar dai kasa cewa komai yayi sai addu'a da fatan zaman lafiya. Cikin abinda bai fi mintuna goma ba suka kammala suka fito zuwa sashen Ja'afar...
A sashen Ja'afar ɗin ma dai shine yay musu jagora har bedroom ɗin Shariffat. Itama dai komai na funichars ɗinta irin na Lailah ne, kala ce kowa wadda yake so aka saka masa. Ga ƙanshin turare na tashi kamar dai sashen Lailah ɗin. Ita kam a kwance suka sameta, sai da Ja'afar ɗin yay sallama sannan ta tashi zaune, fuskarta na lulluɓe itama cikin lifaya. Suna zama ta fara gaishesu. Suka amsa mata da kulawa. Yanzu kam Bilal ne yay mata nasiha ita, Ammar yay addu'a. Anan ma basu wuce mintun goman ba sukai musu sallama suka fito...