Sashe 9
Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
musu ba don yasan warce ya so a rayuwarsa baxae taba samunta ba, wato intisaar. Hajiya kanta sae faman hararar haisam din take kmr ta makuresa amma yaki dago kan, yau dae xafi Alhaji da uwarsa sukayi niyyar tarawa umma, tunda gashi 'ya yanta biyu gaba daya auren hadi xa a yi masu, tab ae ita kam baxata yi tolerate din wannan ba. Intisaar sae tsunkulin maryam take yi tana 'yar dariya tana cewa "amaryar yayanmu," xainab ma hka ta dan dinga tsokanrta murya can kasa, ita dae bata ko daga kai ta kallesu ba, Abba ya kira Aliyu dake ta hararar inna da 'yar ta nafisa don yasan sune kan gaba akan wannan abun,ya dago kai fuskarsa a dan daure yace "na'am" abba yace"ya maganar aure fa?" ya dan yatsine fuska yace "ban shirya ba abba" abba ya tsura masa ido yana kallonsa kanayace "matarce bbu ko kudi?" ya tabe baki yace "duka" don bae ga dalilin wannan tambayr da abba yake masa gaban yan sa idon nan ba, har da inna yake nufi da momy, dama shi daya abba ya kira ya tambaya da xae ce masa yana da safeenah, amma ba gaban wannan group din da ya tara ba. Hajiya taji ddin yanda dan nata yaba uban nasa amsa har ta kasa boye hkn sae murmushi take, abba yyi murmushi yace "to yyi kyau," sannan ya juya yana kallon intisaar yace "ke inna tace akwae me nemanki ko?" gabanta yyi mugun faduwa ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, abba ya nisa yace "baxan iya bashi ke ba fatima, ke din tamu ce baxan bari ki fita daga gidan nan ba sae daeyyi hkuri, amma idan har yaga akwae wanda yake so a gidan nan xan iya bashi, don naga inna ta yaba da hnklinsasosae," kmr saukar aradu mgnr ta dinga xuwa ma intisaar ta kasa dago kanta sae jirin da take gani daga xaune, falon yyi tsit kowa na kallon abba, ita kanta xainab sae da tayi mutuwar xaune don maganar ta girgixa ta sosae, abba yyi shiru sannan yaci gaba da magana kmr hka, "ynxu abinda nke son kowa ya sani a nan shine, Ni da mahaifiyata munyishawara daga karshe muka kawo conclusion a kan cewa, na hada auren 'ya ta fateema da Aliyu, kuma ni din xan masa komai na auren tunda yace bae da kudi," final decision din da na ynke knan, don hka bna son wata magana kuma indae a kan wannan ne daga bakin kowa, ya fadi yana kallon su gaba daya. . .....Har daren ranar Intisaar bata daina kuka ba,ita kam tunda take bata taba shiga tashin hnkli irin na wnn rana ba, momy tayi lallashin har ta gaji ta kyaleta ganin kamar kara tunxurata take, ita gani take kmr momy ba sonta take ba tunda har taki cewa komae a falon, Zainab da maryam ma sun gaji da lallashin sun kyaleta, hka ma Anty Nafisa da ta hau ta da fada ganin lallashin nata da ake kmr xuga ta ake tayi ta kuka,ita kam ta rasa abinda ke mata ddi a duniya. Karfe tara da minti biyar na dare Haisam ya shigo falon nasu, momy na xaune ita da ihsaan suna cin abinci, ita ko tana kasan tiles a xaune ta kife kanta da kujera tun safe take a hkn, sllh kadae ke mikar da ita kuma da tayi xata dawo ta xauna taci gaba da aikin kukanta, dama tuni momy ta fita harkarta, don abincin ranar da ta xubo mata ma kin ci tayi, hkn ma yasa bata xubo mata na daren ba tunda abun nata kmr iskanci ne. Haisam ya gaida momy taamsa da fara'arta ta bar masu falon, ya dawo gaban intisaar ya durkusa yana kallonta kmr shima ya taya ta kukan, wani sabon kukan ta fashe da tana kallonsa gwaninban tausayi, ya xauna gaban nata hade da dago kanta cike da damuwa yace "haba intisaar, so kike ki janyo ma kanki wani ciwon ko," xubewa jikinsa tayi cikin kuka tace "ka taimakeni ya Haisam, ka ba ma Abba hkuri wllh bna son ya Aliyu, kasheni xae yi idan....." ya rufe mata baki hade da rungumota yace "ya isa hka kanwata, bbu abinda ya isa ya maki wanda Allah bai maki ba," a hankli ta fara kkrin hadiyekukan nata sae ajiyar xuciya da take yi, har lkcin yana rungume da ita, murya can kasa tace "ya Haisam," shima murya can kasa yace "kanwata" ta girgixa kai a hnkli tace"da ma kai ne" ya dagota yana kallonta yace "ni ne me?" wasu sababbin hawaye suka gangaro bisa kuncinta, ta maida kanta ga kafadarsa cikin rawar murya tace "dama kai ne Abba ya bani, Bayan sati biyu da faruwar lamarin, tana xaune ita dazainab da kursum a tsakar gida, su suna cin gyada suna hirar irin abubuwan da xasuyi a bikin fadila da ya rage saura sati biyu don abba ya maido dashi kusa a dalilin fitsarar da taje tayi ma inna wae sae tace ma abba ya janyemaganar aurenta da mai 'ya ya har uku tunda ita ce ta xugasa ya hadasu dama, kowa dai yasan umma ce ta sa taxuwa tayi ma innar hka, inna ko ta kwashe abinda ya faru da wanda ma bai faru ba duk ta tsara mar abba tana matsarkwalla, har da ce masa da bulalarta taxo wae xata mata duka, kuma daga Aisha har shafa bbu wanda ya hanata suna kallonta, abba yasa Haisam ya xane ta snn ya maida bikin kusa. intisaar tayi xurfi cikin tunanin da tke yi, xainab ta kwashi bawon gyadar da suka gama ci ta watsa mata su, ba shirita dawo daga duniyar tunanin da ta shiga, ta hade rae tace "meye hka xainab," xainabta dawo gefenta taxauna tana kallonta tace "haba intisaar ke baki da aiki ynxusae tunane tunane, dubi fa yanda duk kika bi kika lalace," intisaar tayi narai-narai da ido kmr xata yi kuka amma ta kasa cewa komai, xainab tace "ynxu tsakaninki da Allah meye matsalarki ki gya min," nan da nan ta fara hawaye tana kallon Zainab din tace "ya faruuq," xainab tayi tsaki tace "yyi pick din cal din naki ne," ta girgixa mata kai a hnklitace "A'a, he ix nt still respondn," xainab ta tabe baki "to tunda ke kuma shashasha ce 'yar wahala ae sae ki ta kiransa, nan a gabanki ya haisam yyi ta kiransa ranar kinga ya daga, mutumin da har office ma ya bi sa, sae dae ace masa baya nn, alhalin kuma yana nn din, kwanakin baya kusan kullum sae inna ta kirasa kinga yana daga wayar, mutumin daya gujeki lokaci daya idan ba ma wauta ba meye na damuwa dashi," cikin kuka intisaar tace "haba xainab ba dole ya guje ni ba, ai tunani xae yi na yaudaresa ne, kuma ko..." xainab ta buga tsaki tace"gskya ne, sae ki tayi ai," snn ta bar ta wajen tayi gaba, kursum ma ta mike tace"duk kin bi kin daga ma mutane hankali akan wanda bai ma damu da ke ba, idan har sonki yake da gskya, ai baxae guje ki lkci daya ba, kuma idan shi dan mutunci ne bai ci ace ya ma ya Haisam abinda yyi masa ba" ita ma tana kai wa nn tayi gaba, ta kife kanta kan gwiwowinta, kuka take kamar ranta xae fita, ita kam ta ga rayuwa, ynxu bbu wanda xae fahimce abinda take ji a ranta, momy damatuni ta dawo daga rakiyarta, ga wani irin sabon tsana da hajiya ke mata a gidan don ji take kmr ta kasheta ta huta, hkn yasa bata da ikon ko lekowa compound, ynxu ma bata gidan shine dalilin fitowar ta tsakar gidan dasu xainab. Budewar gate din da taji ne yasa tadago kanta a tsorace don tayi tunanin su hajiya ne suka dawo, wani irin muguwar faduwar gaba yaxo mata ta dalilin hada idoda suka yii da ya Aliyu, tuni jikinta ya fara bari tayi saurin mikewa tsaye, tana kakkabe jikinta duk na karfin hali. Sae da taga ya wuce ta snn murya na rawa tace"ina yini," shima don gudun kar yace bata gaishesa bane, ta ga ya juyo yana dawowata inda take kuma, salati ta shiga yi a xuciyarta gabanta na ci gaba da bugu, shi knn ta ja ma kanta, da ta sani da bata gaishesa ba ma, gab da ita ya tsaya yana kallonta, ta kasa dago kai ta kallesa don tsoro,"kika ce me?" ya tambayeta cikin daga murya, ta fara kame-kame. "aa.. Dama ni em gaisheka nayi dama," ya fixgota hade da dago kanta yana kallonta, ta tsura masa ido ganin yanda ya rame sae idanuwa, lips din nn nasa yyi wani irin pink sae sheki suke. Wasu sababbin hawaye sukagangaro bisa kuncin ta. . Abba na barin wajen, Aliyu ya fito yyi hanyar gate yana hararan inna da har ynxu ke tsaye tsakar gidan tana kuka, inna ta bisa da gudu ta datse gate din tana cewa gidan uban wa xaka? Sae kuma ta shiga kwada ma Abba kira"Bukar maxa ka fito gashi nn xae gudu wllh," Abun dariya abun takaici, su fadila da kursum dake leke ta taga suka dinga dariya har da faduwa, nn da nn Aliyu ya saita murya ya marairaice mata yana rokan ta ta bude gate ya fita ynxu xae dawo, inna taki sae faman kwala ma Abba kira take tana cewa xae gudu, Haisam ya fito yyi bangarensu intisaar, ba a dau lkci ba suka fito tare da momy suka shigafalon Abba, duk wnn abun da ake akan idonsu hajiya dake leke ta taga ne, wayar Aliyun yyi ring ya duba ya ga Abba ne, ya maida aljihu, yace "don Allah inna ki bani waje na wuce, kati xan je siya," inna ta galla masa harara tace "ae wllh bbu inda xaka sae bukar ya ci min ubanka yau," dariya ta kubce masa, ya ko dinga yi har da buga kafa, karar da wayarsa ta sake yi ne yasa yyi saurin juyawa yyi bangaren innar, inna tace "gidan uban wa xaka, kar ka kuskura ka dosa falona," ko kallonta bai yi ba yyi saurin shan kwana, sae ga Abba ya fito fuskar nn tasa bbu alamar wasa xae yi bangarensu Aliyun inna tace "yyi bangarena maxa ka bisa"