Sashe 23
Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ji tana cewa "wae store din kitchen din kike girka min gaba daya e intisaar, wnn ae sae yunwar ta galabaitar dani," da sauri har yana neman faduwa ya shige bayan kofar, intisaar bata san lkcn da ta kwashe da dariya ba har da xubewa kasa, Anty nafisa ta shigo kitchen din tana cewa "ohh dariya ma na baki, ai gskya ne," intisaar tace"na gama anty ynxu dama xan kawo maki," ta dauki farantin, Anty nafisa tace "to ina na mijin naki fa," intisaar ta girgixa kai tace "ae shi ba ko wani girki yake ci ba Anty," nafisa ta tabe baki tace "sae irin na uwarsa Aisha yake ci knn," intisaar ta dinga dariya, Anty nafisa ta karbe farantin tace "ni bani kar ki xubar min da abinci, ae gskya na fada," suka bar kitchen din a tare suka wuce sama, ae ba karamin farin cikin saukowar Antynafisar intisaar tayi ba, kuma tunda ya shige bayan kofa baya son ta gansa tasan bae da gskya ne. Ni kam koma wacece ke ci min gaba da lbri gskya bn yafe mata ba, Inteesar.... . Karfe biyar saura anty nafisa ta fara shirin wucewa gida, intisaar duk sae taji wani iri tayi jigum tana kallonta kmr kar ta tafi, Anty nafisa tayi dariya tace "kar ki damu daughter, xan dinga xuwa a kai a kai ina duba ki, tunda dae ke Allah bae sa kinyi sa'an miji ba," dae-dae nn Aliyu ya shigo dakin da sallamarsa, nafisa ta xuge handbag dinta ta sakale a hannu tana kallon intisaar din fuskarta atsuke tace "daughter ni na wuce sae wani lkcn," snnta yi hanyar kofar ba tare da ta kalle inda Aliyun yake ba, da sauri ya shige gabanta yana dariya yace "haba momy, ina kika taba jin uwa na fushi da danta," ta galla masa harara tace "da'alla wuce ka ban waje malam," ya karbe handbag din hannunta yace "ina! Ai yau nn xaki kwana momy," tun tana gintsewa har ta fara dariya ganin yanda Aliyu ya maida ta kakarsa, ta koma ta xauna tace "sae ka fito da kudin mota tunda Allah ya kawo ka," yace"tab, ni ban da kudin mota sae dae na kai ki a motata," dole anty nafisa ta tilastasa ya bata dubu biyar kudin mota snn ya maidata gida a motarsa, bayan fitansu intisaar duk sae taji ba ddi ta xauna ita daya a daki tana rera kuka. Ranar friday daya yyidae-dae da sati daya da xuwan Anty Nafisa gidan kuma hkn yyi dae dae da wata biyu da sati daya da kawo intisaar gidan Aliyu, tana daki da daddare ta gama shirin bacci wajajen karfe tara, Aliyu ya shigo dakin nata ya tsaya bakin kofa, ta juyo tana kallonsa, ransa a hade yace "ki shirya xamu fita," snn ya juya ya fice daga dakin, ta dde a tsaye bakin madubinta tana tunanin to ina xasu je da daddaren nn, can dae tayi tsaki tayi kwanciyarta a xuciyarta tace bbu inda xani, can bayan kmr minti sha biyar ya dawo dakin, ya daka mata wani raxannen nn tsawa "wat? . Ina wasa da ke ne ko kin fara hauka ne?" ta mike a tsorace don har ta manta rabon da yyi mata irin wnn tsawar tun suna gida, jikinta ya dau bari ganin bbu alamar wasa a tattare dashi ta mike tsaye muryarta na rawa tace "kayi hkuri, ni bn ji ka da kyau bne," "baki ji ni da kyau ba?" ya tambayeta yana mata wani irin kallo, ta girgixa masa kai, yyi kwafa ya fice, ba shiri ta dauko dogon rigarta na material ta saka snn ta dauki hijab dinta har kasa ta sa, ta feshe turare ta fito falon a sanyaye, yana tsaye ya dafa kujera yana jiranta, ya dauki makullinsa ya fita ta bi bayansa, suna fitowa ya rufe gidan yyi hanyar garage ya bude motar ya shiga, ta xaga ita ma ta bude ta shiga, ya ja motar suka fita daga gidan, sun yi nisa sosae, intisaar gabanta sae faduwa yake don bata san inda xae kaita ba gashi bata ga fuskar tambayrsa inda xasu ba, taga yyi park gefen titi, ya juyo yana kallonta fuskarsa a daure ya fara magana a hankali "kina jina," ta gyada masa kai a dan tsorace "wllh duk tambayar da xa a maki idan har kika nuna baki san komai a kan tambayar ba, xanyi gunduwa gunduwa dake, idan kuma kin yi tunanin am jokin dare me," gaban intisaar ya shiga faduwa sosai ta dinga gyada masa kai a tsorace...