← Book details Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Duk safe da yamma inna na ba xainab
abinci ta kawo mata wani lkcin zainab ta
dan tsaya taya ta hira wani lkcin kuma tace
sauri take duk da tafi tsayawa ma da
yamma, don da safe tana xuwa islamiyya,
intisaar ta sa zainab ta kawo mata novels na
turanci dayawa don ita bata fiye karanta
littafin Hausa ba kuma kallo ishenta yake
don wani lkcin sae ta yini bata kunna tvn
dakinta ba, karatun da take yi yana matukar
taimakonta don yana debe mata kewa
sosai, wani lkcin idan ta gaji da karatun ta
kan tafi garden tayi xamanta tana kallon
tsuntsaye, yau ma kmr kullum intisaar na
falo tana goge gogenta da ta saba, wajen
karfe karfe sha daya na safe ne don Zainab
duk ta bata mata lkci ta cika ta da surutu da
ta kawo mata abinci da safe bata barta tayi
aikinta ba don bata fi minti goma da barin
gidan ba intisaar ta fara gyare gyaren gidan
har lkcin kuma kayan barci ne jikinta,
muryar Aliyu taji bakin kofa yana waya duk
da bae shigo falon ba amma ya bude kofar,
gabanta yyi mugun faduwa ta mike a
tsorace tayi bayan kujera da gudu ta
durkushe a wajen tana xare ido, taji ya
karaso cikin falon tare da rufe kofar, bata
kara jin takunsa ba ko ina yyi tsit, ta rasa
inda ya shiga, a hankali xuciyarta na
bugawa ta dan leko daga bayan kujeran da
take ta gansa tsaye kmr mai naxari yanabin
ko ina na falon da kallo, ta maida kanta da
sauri tare da toshe bakinta gudun kar ta
fasa ihu jikinta ya dau rawa, can dai taji
yana hawa stairs har taji ya bude kofar
dakinsa ya shige, ta mike tsaye da sauri
jikinta na rawa tayi hanyar stairs da gudu
bata lura da ruwan dake cikin bucket da
take mopping ba tayi ball dashi ya kife a
wajen tsantsi ya kwasheta tun kan ta kai ga
fadawa kan centre table din dake gabanta
don kansa ta ga take shirin fadawa ta fasa
wani ihu, cikin ikon Allah bata wani buge
ba, amma taci wahala ledar da Aliyu ya ajiye
kan table dinma sae da ya fadi kasa, duk
kayan dake ciki su ka xube cikin ruwan da
ya malale ta ko ina a falon, intisaar duk ta
rude ta mike da sauri tana rike da cikinta ta
haye sama har tana tuntube ta bude dakinta
ta shige.Tana shiga daki taji ya bude kofar
dakinsa ya fito, takoma gefen gadonta da
sauri gabanta na faduwa ta rakube ta dinga
yarfe hannayenta tana hawaye, xuciyarta
kmr xae shige cikinta don tsoro, yau kam
tasan tata ta kare in ta shiga hannun Aliyu,
tayi kusan minti goma a hka amma bata ga
Aliyu ya banko kofar dakinta ba don ita
jiransa kawae take ya xo yaci ubanta kafin
hankalinta ya kwanta, ta mike tsaye da kyar
jikinta na rawa, taji an bude kofa
downstairs snn aka rufe, tayi kusa da
window dinta da sauri ta dan bude curtain
din tana lekan compound din,
.
tafiyar nn tasa yake ta kasaita yana sanye da
shadda fara yyi mugun masa kyau, har ya
isa kusa da motarsa dake ajiye a garage
don bae fiye fita da ita ba kuma da alamar
shigowarsa gidanaka wanke motar, taga
wani mutumi ya mika masa makullin motar
a ladabe snn ya juya ya bar gidan, ya bude
motar ya shiga ya tada ta maigadi ya bude
masa gate ya fice ta bi motar da kallo cike
da mamaki anya kuwa Aliyu ne wnn, sae a
lkcn ta tuna ashe ma ranar jumma'ah ce,
don da safe kananan kaya ta ga a jikinsa da
ta leko ta window don indae taji fitansa
daga gidan to sae ta lekosa ta taga tun kan
ya shiga mota, jikinta a sanyaye ta sauko
downstairs, barnar da tayi yana nn yanda
yake sae dae ya kwashe ledan magunguna
da allurorinsa da suka xube cikin ruwan, ta
dauki mop ta fara share ruwan da ya malale
ko ina na falon, ba karamin gajiya tayi ba da
aikin falon don sae kusan karfe uku komai
na falon ya dawo dae dae, ta dauko turare
ta feshe a falon snn taje tayi wanka a sama.
Karfe biyar xainab ta kawo mata abinci tace
ba dde wa xatayi ba don sauri take amma
bari ta bata waya su gaisa da inna don
kullum cikin mita take an hanata xuwa
wajen jikokinta kuma an ki barin ta ta
kirasu su gaisa, intisaar ta karbi wayan da
murnarta suka gaisa da inna kmr xatayi
kuka wae kullum ta kira Aliyu ya bata sae
yace tana bacci, intisaar tayi yake tace eh
hka ne inna, sun dde suna hira da inna
daga bisani xainab ta kwace wayarta ganin
suna nema su cinye mata kati tace "ke ma ai
sae ki ce da mijinki ya siyo maki waya tunda
baki taho da taki na da ba," intisaar dae
bata tanka mataba sae murna take yau taji
muryar innarta, xainab tace "daxu fa ya
Aliyu ya xo gida," intisaar bata ce mata
komai ba hkn yasa ta mike tace kinga sae
da safe, intisaar tace Allah ya kai mu, gobe
kice ma inna dan wake xata min, xainab tayi
mata bnxa ta fice abinta
.
Ranar dae har tayi bacci bata ji shigowar
Aliyu ba, washegari asabar ma bata ji fitarsa
ba hkn yasa ta gane bae kwana gidan ba
knn, karfe biyar da rabi zainab ta kawo
mata abincindare, tuwon shinkafa ce da
miyar ganye sae farfesun kifi, intisaar ta
tabe baki tace "to ynxu ni canayi ma inna
ina cin kifi," xainab tace " iyye samun waje,
ba laifinki bne, kuma ni da kaina xan xuga
inna nace tunda kinyi sati kawae ki fara
girki," intisaar tayi dariya tace "ke kin isa ki
shiga tsakanina da innata, ae ta dinga kawo
min girki knn har sae nayi shekara," xainab
tace gskya ne matar yayanmu, snn ta hada
mata wani tsumi da inna ta bata ta kawo
mata tace "gashi nn inna tace ki sha wnn,"
intisaar ta yatsine fuska tace "na meye,"
xainab tace "yana sa mutum yyi fresh, yyi
kyau," ganin yanda xainab tayi serious
kuma taga har da madara ta xuba ciki yasa
intisaar ta yarda ta jawo ta fara sha, xainab
ta danyi murmushin intisaar wawiya ce, snn
ta bata turarrukan da inna ta bata takawo
mata kusan kala uku, tayi mata sllama tayi
gaba abinta. Karfe takwas intisaar ta gama
kallon tasharta ta Mbc bollywood ta kashe
kayan kallon snn ta kwashi kwanukan da ta
ci abinci tayi kitchen dasu xata wanke, ta
gama wanke wanken tana dan goge
kitchen din da ruwa taji shigowar motar
Aliyu, gabanta yyi mugun faduwa ta kife
kwanukan da ta wanke da sauri har tana
xubar da ruwa kitchen din don har wani
bari jikinta yake don tsoro, ta kashe tap ta
fito ta rufe kofar kitchen din ta haye sama
da gudunta ta shige daki ko me ya dawo da
shi da wuriyau don tasan ba lkcn
dawowarsa bne ynxu. Tana jiya bude
dakinsa ya shiga, ta kashe wutan dakinta
snn ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta
fara shafe shafenta gaban madubi, ta dauki
turaren da xainab ta kawo mata ta shafa
kamshin turaren yyi mugun tafiya da
imaninta, dama ga ta gwanar son kamshi, ta
lumshe idonta ta bude cike da jin ddi, ta
tsura ma kanta ido a madubi tana kallo, ta yi
murmushinta mai kyau snn ta mike ta dauki
wani kayan barcin ta pink colour mai
hannun singlet tsayin iya cinyarta sae
wando da shima da kadan ya wuce cinyar
ta saka, tana ji Aliyu ya bude kofar dakinsa
ya fito ya sauka downstairs, ta san coffee
kila xai je hadawa a kitchen,
Chapter 16 · 0% Book details