← Book details Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na dawo, xan je siyo abinda ya kamata," ya fice haisam ya bisa a baya da sauri, sai da suka kai tsakar gidan sannan yace "canjin nawa xaka dawo da knan?" Aliyu yace kmr ya, haisam yace eh ae dubu tara aka baka, kuma dubu takwas da dari biyar kace, Aliyu yyi masa wani irin kallo sannan yace "to da kafa xanje siyo magungunan?" sannan yyi tsakiya wuce yana cewa "dn ma kun samu xan bata lkcn" . . Su Aliyu na fita inna ta mike tana tambayr intisaar din me xata ci, ta girgixa kai alamar ba komai, xainab tace"to ki daure kisha tea din" inna ta dauki kofin ruwan shayin ta isa kusa da ita tana cewa "tashi ki sha kafin ya dawo to" intisaar ta girgixa kai murya can kasa-kasa tace "wanka xan fara yi," momy ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wankan sannan ta mike da kyar jiri na kwasarta ta shige bayin, ko da ta fito rawan sanyi ta dinga yi, inna ta lullubetatana cewa "ikon Allah, ciwan lkci daya ya kwantar da ita," ya haisam ya shigo dakin yana tambayr ko Aliyun ya dawo,inna tace "ina fa! yana can yana sokwanci" haisam ya girgixa kai yace "ni dae wllh inna nafi son a kaita asibiti," inna tace "wae ni kuna bani mamaki wllh, ga likita a gida kuyi ta kiran asibiti," haisam yace "to shknan, ni xan wuce kd ne ynxu ina da wani aiki a can amma yau xan dawo in'sha Allah," inna tace "to Allah ya kiyaye" yace "ameen" sannan ya karasa kusa da intisaar yana kallnta yace "Allah ya sauwake kanwata kinji" tayi murmushi, a hnkli tace "ngdyayana" yyi ma momy ma sllma sannan ya fita. Da kyar inna ta lallabata tasha kunun da ta dama mata, xainab sae fama kallon agogo take yi dn har sha daya ya wuce, tun kusan karfe goma da Aliyu yaje siyo magunguna har ynxu bai dawo ba, tuni bacci ya dauke intisaar din bayan inna ta bata paracetamol kafin Aliyun ya dawo, amma har karfe sha biyu bbu Aliyu bbu lbrinsa, "kai jama'a ko dae wannan yaron bata yyi ne" inna ta fadi tana kallon momy da xainab dake dakin bakinta a bude, momy dae bata ce komai ba, xainab ta tabe baki ita ma bata ce komai ba, wasa-wasa har karfe biyu bbu Aliyu, inna na idar da sllh tana xaune kandarduma cikin ihu tace "amma wannan anyi tsinannan yaro," daga momy har xainab sae da suka raxana sbda irin bude muryar da inna tayi, momy tace "kai inna, kika san uxurin da ya tsayar dashi," a fusace inna tace "yaci ubansa shi da uxurin," ku bni waya na kira bukar, momy tayi ma xainab ido alamar kar ta kira mata abban, inna ta mikawa xainab din wayar tana cewa "maxa kira min uban nasa" xainab ba don ranta yaso ba tace ma inna baya xuwa bayan ta kara wayr a kunne kmr me kira, don ita da momy ta barta kiran abban xatayi, ita kam bata san irin yayan nata ba, basu san tuni abba ya kira momyn yana tambayrtajikin intisaar din ba tace masa da sauki sosae, yace Aliyun ya bata duka magungunan tace masa eh sannan sukayi sllma, xagi kam Aliyu ya sha shi a wajen inna ba adadi, har da dan hawayenta, "ni da nasan abinda tambadadden yaron nan xae yi knan da asibiti kawae na bari muka wuce, gashi ynxu yrnya na ta shan axaban ciwo ba magani, shi kuma bukar na rasa uban me xae sa ya dinga kashe wayarsa ni kam, ynxu wa xae kai mu asibitin gashi haisam ba ya nan," daga momy har xainab bbu wanda ya tanka mainna, intisaar kam jikinta yyi xafi sosae kmr wuta, hka inna ta ishesu da mita tana hawaye, wajen karfe uku da rabi wayan intisaar yyi kara xainab ta dauka tana kallon me kiran, faruuq ne, da har xata ajiye don bacci intisaar din take yi sae kuma ta fasa ta daga, suka gaisa ya tambayeta intisaar din fa, tace "bacci takeyi wllh, bata da lfya," cike da damuwa yace "subhanallahi, me ya sameta" xainab ta yarfe hannu tace "wllh bamu sani ba, tace dae ciki da kantake mata ciwo," yace "tun yaushe?" tun jiya da daddare wae,yace "ya salam! kunje clinic ne?" tayi shiru ta rasa me xata ce, yyi saurin cewa "ohk... Gani nan xuwa," ya kashe wayr, inna tace "faruqu ne?" xainab ta gyada mata kai kawai, cikin minti goma sha biyar faruuq ya iso gidan, hanklinsa ya tashi sosae, momy da ta bar masu dakin ya rage inna daxainab kawae, ta tashi xaune tana kallon faruuq din da ya sata gaba yana tambayrta inda ke mata ciwo, cikinta t.a nuna masa da kai, yasa hannu ya danna cikin nata ta xaro ido tace "waii! ciwo yake min" me ya buge ki a nan ya tambayeta yana taba goshinta da yaji xafi sosae, ta girgixa masa kai kawae sae hawaye, duk ya rude ya shiga lallashinta yace "dama kina ciwon kai ne," ta girgixa masa kai kawae, ya mike yana kalln inna yace "bari ina xuwa yanxun nan inna," inna tace "to dan albarka, wannan shaidanin yaron aka ba kudi ya siyo mata magunguna bamu sake ganinsa ba " bai tanka wa inna ba ya fice da sauri, ko minti talatin bae cika ba ya dawo dauke da kayan magunguna da allurori sae ledar ruwa dan karami da xae sa mata, ya ce wa xainab ta hado mata tea mai kauri ta kawo mata, shi da kanshi ya shiga bata, amma ta karba tace xata iya sha, yana ta hada allurorin da ruwa har ta sha rabi ta ajiye tace "ta koshi," yace "ae baki ma ci komai ba tukunna, tuwo xa a kawo maki kici ynxun," inna ta mike tana cewa "gskya ne, bari naje da kaina ma xan mata ynxun nan," da kyar ta yrda yyi inject din ta sannan ya sakamata ruwan ya bata wasu daga cikin medicines din tasha ta kwanta, ya xauna ya xuba mata ido yana kallonta cike datausayi, xainab dama tuni.. Faruuq na xaune har ruwan da yasa mata ya kare da yake karamin leda ce, ya cire mata don bacci ma takeyi, yana gama cire mata ta bude ido tana kallnsa, yyi mata murmushi yace "ya jikin kanwata," ta tashi xaune tace "da sauki," ba tare da ta kallesa ba, ganin tana kkrin mikewa tsaye ne yasa yace "ina xaki kuma kanwata," murya can ciki tace masa "2 ease my self," ba tare da ta kallesa ba, ya taimaka mata ta tashi tsaye dn jikinta ba kwari dukda taji ta garau ynxu, tuwon da inna ta kawo mata ya shiga xuba mata, ta fito ta nemi gefe ta xaunatana kallonsa kmr xatayi kuka, ya dago kai yana kallnta yace "kici abinci ki sha sauran medicine dinki kanwata, kusa da ita ya durkusa yana kallonta yace "ya dae kanwata, cikin na maki ciwo har ynxu ne, naga yhu re restless" ta girgixa masa kai kawae bata cekomai ba "say somethin mana kanwata, ina ke maki ciwo kuma?"ya tambayeta cike da damuwa, itakam kunya take ji tace masa mararta ke mata ciwo, don hka tace "ni bbu inda ke min ciwo," sae kuma ga hawaye, nan da nan ya rude ya shiga lallashinta yana cewa "plss kanwata ki gya min mene mana, kan bai daina bane?,"ganin yanda duk ya bi ya daga hanklinsa ne yasa tace "cikina ke ciwo," ba tare da ta kallesa ba, yace "ciki kuma, ba kin ce ya daina ba, to wae me ya buge ki a cikin ne" a hankli tace ba shi bne, yyi shiru kmr me naxari sannan yace "on yhur Period?" yana kallonta, tayi shiru bata ce komai ba kanta a sunkuye, yace "ohk ina xuwa kanwata," ya mike ya fice. Ko da ya dawo tana xaune a falo ita da momy da inna sae kursum, tasa tuwo a gaba amma taki ci, ynxu kam jkinta yyi mata sauki sosae, da sllmrsa ya shigo falon rike da ledan magani karfe biyar da minti goma na yamma, ya gaida momy don tun xuwansa na farko bai sake ganinta ba sae ynxun, ta amsa tanai masa sannu da xuwa sannan ta mike ta bar falon, xainab ta shigo ta xauna gefen intisaar din tana mata ya jiki, tayi murmushi tace "da sauki"maganin da ya xo da shi kala uku ya dauki daya ya buda ya bata, ta karba a kunyace xata ajiye yace tasha ynxun, inna tace "ae hka nan take yarinyar nan bata san magani, nayi mamakin ma da tasha wa inda ka bata daxu," faruuq yyi murmushi kawae yana kallnta har ta kora maganin da ruwa sannan ya sa ta cin tuwon dake gabanta, bude kofar da sukaji anyi irin ta mahaukata ne yasanya su juyawa gaba daya, Aliyu ne ya shigo dakin sanye da t-shirt fara kal da wando three qtrshima farin, yyi kyau sosae, hannunsa rike da leda da basu san ko meye a ciki ba, intisaar ta sunkuyar da kanta da sauri, faruuq kuwa kallo daya yyi masa ya kauda kansa, kallonsu ya shigayi daddaya da daddaya, inna tana sakace hkori ta tabe baki tace "ae sae ka je ka tsis-tsira ma kanka allurorin ka shanye magungunan don jikata kam ta warke, dan arxiki wanda aka haifa tsiya na bacci ya xo ya duba mana ita" Aliyu ya yo waje da dara-daran idanunsa yana kallon innar, wato shi aka haifa tsiya ido biyu, ya juya yana kallon faruuq din da intisaar, xainab ta labe bayan intisaar sbda wani irin dariya dake cinta, hka ma kursum da ta rufe fuskarta a jikin inna, Aliyun yatsura wa faruuq din ido kmr xae shake shi, faruuq bai ma san yanayi ba, ya dube intisaar yace"kanwata kin ki cin tuwon ko na taya ki ne?" ta kirkiro murmushi bata ce komai ba, yace "au kar na taya ki?" a hnkli tace "kaci mana" yyi murmushi yace ok, sannan ya mike ya dauki ruwan goran dake gabanta ya bi gefen Aliyun ya fita, Aliyu ya bishi da kallo har ya dawo ciki sannan ya xauna gabanta yace "to muci," a kunyace tasa hannu cikin tuwon sannan shi ma ya saka, inna
Chapter 5 · 0% Book details