← Book details Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sama da kankara yau, wae ya Aliyu ne har da bata kudi ta hau mota," tayi dariya sosae bayan ta fita, lallai intisaar ta gama mata da yaya jiya. Yinin ranar Aliyu bae fita ba yana gefen intisaar, duk wani motsi da xata yi a kan idonsa, dukda xxabin ya bar jikinta amma ta kasa sukuni don sae juye juye take, yasan ciwo ne ke cin ta, karfe biyar da wani abu ya fita siyo mata chips ganin taki cin duk abincin da xainab ta kawo mata (ko ya akayiyasan intisaar na son chips oho ma Haiydar) yana fita kuwa xainab ta shigo gidan da abincin dare, ta kasa shiga dakunan ganin level ya canxa a gidan, hkn yasa ta dinga rafka sllma amma shiru, ta sauka kasa ta samu maigadi ta tambayesa ko mutanen gidan na ciki, yace oga dae ya fita daxun nn, ta koma cikin gidan tayi hanyar dakin intisaar ta bude a hnkli bata ga kowa a ciki ba, hkn yasa tayi hnyar dakin yayan nata, xaune taga intisaar kan gado, ta kife kanta bisa gwiwwowinta, ta karasa dakin ta xauna gefen gadon tana kallonta, a hnkli intisaar ta dago kai tana kallon xainab din da idonta da ya gama rinewa alamar ta ci kuka, xainab ta girgixa mata kai ganin kukan take son fashewa da kuma ta rungumeta, ta ko fashe da kukan sosae cikin shassheka tace "xainab ya Aliyu mugune, ya cuceni,ya..." da sauri xainab ta rufe mata baki tace "sshii.. Ya isa hka, wnn sirrinki ne tsakaninki da mijinki," kuka sosae intisaar ta dinga yi xainab na lallashinta, suka ji an bude kofar Aliyu ya shigo dakin "wat," ya daka ma xainab tsawa yace "uban me ya kawo ki nn kuma," ta mike tsaye da sauri, ya daka mata tsawa ba da ke nke ba, ta xunburo baki tace "abincin dare na kawo maku," ya nuna mata kofa "xoki fita," . tayi hnyr kofar ba tare da ta kallesa ba tace inna tace ta fara girki daga gobe," yace"taji," snn xainab ta fice.. Cikin kwanaki biyun nn intisaar ta sami kulawa a wajen Aliyu sosae, don ynxu kam jikinta yyi sauki sosai, kuma duk wnn abinda yake mata baya bari su hada ido, ita kuwa dari dari take dashi don bata yrda Aliyun da ta sani bne wnn ga wani mugun tsanarsa da take ji a xuciyarta, sae dae kuma har lkcn bata iya takawa, yyi yyi ta bari ya dubata amma kememe taki, hkn yasa ya kira wata Dr Maryam warce suka yi karatu tare ta xo dubata, ya fita ya bar masu dakin, ita ma dae da kyar intisaar ta yarda ta dubatan. Bayan kmrminti talatin ta fito tana ma Aliyun wani irin kallo, yyi murmushi yace "ya akayi Dr," ta girgixa kai tace"amma wllh ka bn mamaki Dr, kai da kanka, kai da xaku dinga ba wasu shawarwari shine..." yyi dariya ya katse ta da sauri "gskya ne maryam, but tel me d truth don Allah, is it dat critical" ta galla masa harara tace "wnn kuma ya rage naka, though it's nt, idan na fita ynxu xan turo maid dita da drugs da injections da prescription dinsu sae ka mata, snn kadinga sa tana shiga ruwan xafi da dettol sosae, i will b on my way," yace "ok, bill dina fa Dr," ta hararesa tace " ae ba kai nayi ma wa ba, kanwata nayi ma, xan lekota xuwa jibi," yyi dariya yace "to ngd maryam," ta tabe baki tace "mugu kawae," snn ta fice, sunyi soyayya sosae da maryam suna sch, kuma lkci daya ya gujeta duk da irin son da take masa, shi kuma yana da dalilinsa nayin hkn. Ya haye sama ya shiga bedroom dinsa ya xauna gefenta yana kallonta, tana kwance idonta a lumsheduk da ba bacci take ba, shima kuma yasan ba barcin take ba. Cikin kwanaki ukun da intisaar tayi dakin Aliyu ta sami kulawa sosae daga gareshi don komai shi yake taimaka mata tayi, harta abinci shi da kansa yake bata, duk da tana yi tana dan noke masa, kullum da yamma sae Dr maryam taxo dubata har dae ta warware sosae tana iya yin komai da kanta, yana ganin ta warke kuwa ya fita harkarta ya daina tarairayarta kuma, snn yaki barin ta ta bar dakin nasa, tsakaninta da shi sae dae ya siyo mata abincin ya ajiye mata gabanta in ta so taci idan bata so ba ta barshi, ko kadan hkn baya damunta, ita dae 24hrs tana kallo abinta a dakin, shi kuma yana kan laptop dinsa, ta rasa dalilin da ya hanasa xuwa aiki ta tattara ina ta ina ta ta koma dakinta kafin ya dawo. Ranar friday, da yyi dae dae da kwanakinta biyar a dakinsa yana bathroom yana wanka ita ko tana kan gado tana kallo taga wayarsayyi haske, ta dan kalli kofar bayin, ta dauko wayar taxauna tana duba mai ya shigo wayan, msg din safeenah ne, ta bude tana yastine fuska ta karanta kmr hka,, Honey kwana biyu ka mance dani ko, naje har office aka ce ka dauki hutu, don kuji ddin cin amarcinku da matarka, ni dama nasan duk ddin baki kke min kawae Haiydar......" intisaar ta ja dogon tsaki ta cilla wayar ba tare da ta karasa karanta text din ba, can dae ta jawo wayan ta shiga yi masa binciken inbox na msg, msg din mata sun kai 50 a inbox din, to a ina ya sansu, hka ta dinga dudduba msg din har ya fito daga bathroom, ta tura wayar karkashinta a tsorace, ita dae tasan da wuya tsoran Aliyu ya rabu da ita lkci daya, sanye yake da farar t.shirt da 3quatre don duk xaman da tayi a dakinsa bai taba sa kaya gabanta ba, . hatta singlet baya tsayawa dashi a dakin, bae ko kalleta ba ya isa gaban mirrow ya dauki turare yana fesawa, wayarsa tayi kara, ya juya da sauri yana kallonta, gabanta yyi mugun faduwa ta ciro wayar daga karkashin kafanta, ta ajiye masa kan table din computernsa kmr munafuka, ya karaso ya dauka yana hararta yace "uban me kike da wayata" ta kauda kanta bata ce komai ba, kira ya sake shigowa, ya dde nn a tsaye yana hararta daga bisanni yyi kwafa ya daga kiran, "bbyna ykk, ayya ban manta dake ba wife, wllh abubuwa ne suka sha min kai, but gani nn xuwa ma ynxu, kiyi min fruit salad, kinji dear" yyi dariya snn ya kashe wayar, intisaar ta tabe baki tare da mikewa tsaye tayi hanyar fita, ya bita da kallo tare da daka mata tsawa, xo nn uban wa kike tabe ma baki hka," ta juyo tana masa wani irin kallo duk da irin yanda gabanta ke faduwa tace "ni na tabe baki ne," snn ta bude kofar, ya daka mata tsawa "ina xaki," ta juya tayi masa wani irin kallo snn tace "ae nn ba dakina bne," ya bude baki yana kallonta da mmki yace "da xa a kawo ki gidan nn a dauro maki daki daga gidan ku kin kawo nn ne," ta dan tabe baki bata ce komai ba ta kauda knta, "fice min a daki kar nayi ball dake a nn, raguwar bnxa kawae," ta fice daga dakin tare da jan dan guntun tsaki, ya bita da sauri yana cewa"uban wa kike ma tsaki," amma tuni ta shige dakintata kulle da makulli, tana jinsa ya ja motarsa ya fice daga gidan, . ynxu ita kadae tasan irin tsanar da takema Aliyu a xuciyarta, ranar dae har tayi bacci Aliyu bae shigo gidan ba, ga wani irin yunwa da take ji, dole ta tashi cikin dare ta shiga kitchen ta bude store taga kayan abinci, ta dauki indomie guda biyu da kwae ta dafa ta ci, sae a snn ta sami bacci. Tun daga lkcn kmr anyi ruwan sama an dauke Aliyu ya fita harkarta, tsakaninta dashi kallo, kuma shi ke kallon nata ba ita ba, don ko gaishesa bata yi a gidan, iyaka idan taji shigowar motarsa ta shige daki da gudu.. Randa ta ci ka sati uku a gidan tana kitchen ta gama wanke wanken kwanukan d a ta ci abinci da safe bayan Aliyu ya fita, tana sanye da dan jumper sae bum short, ta ji muryarsa ya shigo gidan, gabanta yyi mugun faduwa, shknn ta shiga uku, ta dan leka falon a tsorace taga ashe shi da safeenah ce ma, taga xae shigo kitchen ta buya bayan kofa da sauri, safeenar ta biyo bayansa tana cewa "honey irin coffee din nn naka xaka hada min ba tea ba," yace "ok bby," ta kwanta bayansa ya juya yana kallonta yace "ae sae ki sa na kasa hada coffeen bby, wait 4 me @ d parlor" ta kankamesa tana 'yar dariya tace "idan naki fa, wae ina matar gidan ne," tsit kke jin Aliyu, ta rungumosa ta gaba tana masa wani irin kallo gnn abinda take so knn tace "ya kayi shiru dear," tasan ba lallae bane ta samu amsa, hkn yasa ta daura bakinta kan nasa tana 'yar dariya, duk wnn abinda sukeyi intisaar da taji kmr numfashinta xae dauke na kallonsu ta bayan kofa, ita kam xuwa ynxu ta gama gane wanene Aliyu, ta gano weak point dinsa, ganin irin kiss din da yake ma safeenar tana mayar masa da martani yasa ta turo kofar ta fito, daga safeenar har shi sun tsorata, ta gabansu ta wuce tare da jan dogon tsaki tace uhum karuwancin ma har sae an biyo mutum gida don rashin sanin ciwon kai," can kuma sae ta juyo tana kallon Aliyun dake binta da kallo gabanta na mugun faduwa tace " ni dae malam kayi hkuri ka daina shigo min da karuwae gidana idan ba hka ba Allah xan hadaka da Abba,".... A fusace Aliyu ya fixgota da karfi yana huci cikin tsawa yace "me kika ce?" tuni jikinta ya dau rawa don tsoro, ya maimaita tambayr cikin tsawa, amma intisaar bata ce komai ba sae daure fuska ma da ta dada yi, hkn yasa ya makureta tana ganin hka ta fasa ihu mai kara tare da durkushewa a wajen, ya bi ta da sauri tare da rikota, a rikice ya fara tambayarta mai ya faru, ta sake
Chapter 18 · 0% Book details