← Book details Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aliyun taga kallonta yake yi, da sauri ta dauke kanta xuciyarta na bugawa, abba yagama wayan ya juya yana kalln Aliyun yace "sae ynxu garin ka ya waye knan malam," ya shafa kansa ya danyi murmushi yace "kayi hkuri abba, yau na tashi da ciwon kai ne," abba baice masa komai ba illa Allah ya sauwake, yace"ameen" sannan yace "ina kwana abba," lfya lau, ka tashi lfya?" abba ya amsa yana kallon intisaar da har ynxu kanta a sunkuye yake, kun gaisa da yayannaki ne? Ta dago kai da sauri tace "ina kwana yaya?" Aliyun yace "lfya lau, da kina jiran na gaida ke ne halan" ya fadiyana kirkiran murmushi ganin yanda abban nasa ya kafa masa ido, ita din ma murmushin ta kirkiro tace cikin muryar da ba tata ba"kayihkuri na sha'afa ne" abba ya dubi intisaar din yace "yauwa ina jinki fatima," ta gwalo dara-daran idonta ta rasa me ma xata ce da abban, sae kawae ta samu kanta da cewa "aa dama abba gidan momy nke sonnaje ne yau," abba yace "wace momyn knan?" da sauri tace "momynsu maryam" yace "ohhk gidan nafisa xaki" tace "uhm," abba yace yaushe xaki dawo idan kinje? Da yamma xan dawo abba, ta fadi da sauri tana kallonsa, duk da tasan idan taje ba lallai bne ta dawo kuma, kila can xae fiye mata xaman lfya. "wa xae kai ki knan?" tayishiru sannan tace "xan hau tricycle abba" abba yace "aa Aliyu dae ya kai ki, tunda yana gida. Intisaar ta dago kaida sauri tana kallon Aliyu, taga yyi wani murmushi irin tamugunta, ta girgixa kai gabanta na faduwacikin tausasa murya tace "abba ya haisam yace xae kai ni kuma..," Aliyu ya kalleta yana murmushi yyi saurin cewa "ni cinyekixanyi a hanya knan?" ita din ma kirkiran murmushin tayi tace "aa ba hka bne, kaga na riga da na fara gya masa, da bn gaya masa bne sae ka kaini," to ai ni da haisam daya ne, meye a ciki idan ni na kai ki din? Ya tambayeta yana kallon tsakiyar idonta, Ta xaro ido xuciyarta na bugawa tace"gskya ne," abba yace "toma wae a ina kika ga haisam din?" ta fara kame-kame tama rasa abinda xata ce masa, abba yace"tun asuba ya shigo yace min xae tafi jigawa, ko ya fasa ne?" ta dan sata kallon Aliyun da ya kafa mata ido yana murmushin da ta san na mugunta ne, ta rumtse idonta cike da tsoro tace "na manta ne, hka ne abba," Aliyu yyi 'yar dariya yace "to yanxu kin yrda na kai ki?," tace "uhm" yace "aa kiyi magana mana, ta mike tana cewa "bari naje na shirya," abba ya kirata ya dauko dubu biyar ya bata, yace"ki gaida min dasu shaheed," ta durkusa har kasa tayi masa gdya sannan ta fice da sauri kafarta na hardewa, abba yyi murmushi, yana jin ddin alakar 'ya yan nasa, don a nasa tunanin, Aliyun son intisaar din yake, ganin actions dinsa. Intisaar na fita da gudu tayi sashinsu don tana tsoron kar ya biyota, momy ta kalleta tace "har kin dawo?" tace "uhm, momy manta da innar nan, gyangyadi take ta minna gudo," bedroom ta shige da sauri ta fada kan gado, ae xuwa gidan anty nafisa kam ya sha ruwa ysu don ko hauka take ita kam baxata bi Aliyu ba. Aliyu kam yana barin falon abba ya shige bedrom dinsa cike da jin ddi ya shirya, irin abinda xae mata ya dinga kitsimawa a ransa, rannasa na dada baci, ya gama shirinsa tsaf ya fito,hajiya na tambayrsa inda xa shi amma baetanka mata ba, kujera ya ja a tsakar gidan ya xauna jiranta, amma har kusan karfe sha daya da rabi bata fito ba, ya gaji da jiragashi bbu kowa a gidan bare ya aika kiranta, shi kam yau idan bae ma yarinyar nan abinda ke cikin ransa ba ciwon xuciya xae iya kamasa, yyi huci me xafi ya mike tsaye yana waige- waige, kasa daure wa yyi yaje sashin nasu, yana isa ya bude kofar falon momy na xaune tana duba wani littafi, intisaar ma lkcn ta fito falon tana kwance tana kallon Mbc2, ya kalli intisaar din ya dake yace "kin shanya ni ina ta jiranki?" ta mike tana kallonsa tace"tafiyar nan fa ina ga na fasa kayi wuce war ka kawae," ta juya ta shige bedroom xuciyarta na bugawa, don taga kkrinta na fada masa hkn, tsaye yyi bakin kofar kmr ruwa ya cinyeshi, ya juya ya bar wajen xuciyarsa na harbawa, lallai yarinyar nan tadauko hnyr raina shi ne kuma xae yi maganinta, ransa a bace ya bar gidan yanatunanin me xae ma intisaar yaji ddi idan ta shiga hannunsa?" kiranta momy tayi bayan ya fice fuskarta daure tace "meya hada ki dashi, kuma ina xakuda?" nan ta koro ma momy yanda sukayi momyn ta hade rae tace "karki kuskura, ko da wasa kuma." yau kusan sati biyu knan suna wasar 'yar buya da Aliyu duk inda tasan xasu hadu bata xuwa, bangaren inna ma ba kasafai take xuwa ba kullum dae tana kunshe a daki kmr sabuwar amarya, shi kam kullum cikin addu'ar ta shigo hannunsa yake, ya rasa kwanciyar hankli har sae ya mata abinda ke ransa har gobe idan ya tuno kalamanta sae ransa yyi mugun baci, ya ma daina ganinta kwata-kwata a cikin gidan, har yyi tafiya xuwa lagos basu hadu ba. faruuq kam kullum suna manne da juna, idan bae xo ba to xai kirata, shakuwarsu ya wuce misali, shi kullum matsalarsa ta xamomatarsa, dn yaxo ya sami inna tace ya bata wata guda suna shawara ne da abba, to gashi har anyi wata biyu shiru, intisaar a ko da yaushe cikin kwantar masa da hnkli take, takan ce masa ae babba baya magana biyu, tunda inna tace ya kwantar da hnklinsa an bashi, kawaeya daina tada hnkalinsa ita din tasa ce. yau kam wajen innarta ta shirya xata je suyi hira don ita bata cika hira da momy ba, falon abba ta fara shiga da sllamrta tana tunanin ko dae ta jaraba abinda maryam tace mata a kan karatunsu, "ya dae fatima ba matsala ko?" abba ya tambayeta bayan sun gaisa, tayi murmushi tace "dama abba ca nayi don Allah ka bar mu muci gaba da karatunmu," abba yyi murmushi yana kallonta yace "karku damu fatima, xakuyi karatu sosai ammaa gidan maxajenku, don hka tsarin inna yake, kinga nafisada kike ganinta ita ma a gidan mijinta ta karashe karatun ta kuma kinga ynxu tana aikinta," tayi shiru kanta a kasa, duk da bata so hkn ba, kawae tace masa "to abba ngd" Abba yyi murmushi yace "dama ina san magana dake intisaar, wannan yaron da yake xuwa wajenki faruuq kin tabbatar kina sonsa?" tayi shiru ta kasa cewa komai ga kunya da ya lullubeta, abba ya cigaba dacewa"manyansa sun xo sun sameni ne, amma nace su dakata don akwae wata shawara da mukeyi da inna, duk me ake ciki nace xan sanar da su," ke kina sonsa?Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba sae wasa . ... Salon ku batawa dana suna daga ke har gantalalliyar yar taki, to ahir dinku, aure kuma kmr anyi an gama ne indaiina raye, ina nan ina lissafi yau shekara daya knan da ta kaso aurenta ta dawo mana gidan nan take ta tsula tsiyarta kun sa mata ido, umma a fusace ta mike tana rike da kugu tace "to a kanki take xaune a gidan ko kuma ciyar da ita kke ko....." tsawa abba ya daka mata ya mike yana kallnta a fusace "fice min daga falo," inna da tuni ta fara matsar kwalla tace "wllh ka korata idan ba hka ba ni xan bar maku falon," umma tace "ko bka fada ba dama, amma wllh tllh baku isa kuma 'yata dole ba" ta juya fuu ta fice, fadila ta mike ita ma tana kuka xata fice Aliyu ya daka matatsawa "gidan ubanwa xaki, c'mon get back kar na ballaki" ta koma tana goge hawaye ta xauna, abba ya dubeta fuskarsa a hade yace "ki sa a ranki cewa nan da wata biyu ne bikinki, kuma daga yau bna sn ko kusa da gate ki je," inna ta cafke "ae wajena ma xata dawo har ranar bikin, kinakomawa ki tattaro kayanki ki dawo bangarena" abba yace kin dai ji, kuma bna son a tunasar dake a kan hkn, hajiya ta rike haba cike da jimami tace "abu dae bae yi ddi ba, kuma nasan wannan xugi ne akayi, amma Allah ya fi koma wa yyi," ta fadi hkn ne tana satan kalln momy da tayi jigum tana sauraransu, abba yyi tsaki yana kallon hajiyar amma bae ce kmai ba, ita kuwa sae girgixa kafa take bakinta a tabe, haisam kam tv ya kafa ma ido, abba ya dubi haisam din yace "ya maganr da mukayi da kai haisam," haisam ya danyii murmushi yace "abba ni na amince ae xabinku shinenawa," abba yace "to Allah yyi maka albarka," yace "ameen abba," abba ya dubi maryam din Anty nafisa yace"daughter kema dae kin amince ko?" ta rufe fuskarta bata ce komai ba, abba yyi murmushi yace "to Allah yyi maku albarka, yasa hkn shi yafi alkhairi," gaba daya falon suka ceameen, inna baki har kunne sae sa masu albarka take, Aliyu yyi dubara ya koma gefen haisam murya can kasa-kasa yace "wae da maryam abba xae hadaka kace ka amince?" haisam ba tare da ya kallesa ba yace "um" Aliyu ya wara ido da mamaki yace "gosh, amma an cuceka, kai din yaro ne da xa a xaba mka mata, me xakayi da wannan kwailar da bata wuce 18 ba battun ga big babes a gari? Kaiian cuceka wllh, ae abba yasan baxanyi toleratn hkn ba shiyasa bai dosheni da wannan wawan xancen ba," in kagayanda ran Aliyu ya baci sae ka rantsa kace shi aka xaba mamata a lkcn, amma haisam ko a jikinsa don bai da wata mafita tunda abba ya dde yana masa mgnr ya fito da mata,kuma abba sae da ya nemi shawarsa kafin ya hadasa da maryam, kuma dae maryam kanwarsa ce, bayan hka ma maryam kyakkyawa ce ga ilimi both, sannan ga hnkli da nutsuwa shi kam bae ga aibunta ba shiyasa bae ma yiwa abbansa
Chapter 8 · 0% Book details