Sashe 21
Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai, ya fice ya bar mata falon, nn inna ta sa ta gaba bayan ta hadata da fura mai sanyi tana mata tambayoyi, cutar ki yake yi a gidan ko, da gske ne bbu abinci a gidan nasa ko, to me kike ci ni Rahmatu, ynxu ma nasan kila Bukar ne yace ya kawo ki nn ko, to wae a ina gidan yake sun ki gaya min da na ringa xuwa kullum da kaina, intisaar ta fara tarin karya ta buge innar tace "kae inna ae gashi kinsa har ina kwarewada wa innan tambayoyin naki, inna ta koma gefe da sauri tace "yi hkuri to gama tukunna," hka intisaar suka dinga cafter da inna dake ji kmr ta maida ta ciki har su Zainab suka dawo gidan, duk suka yi murnar ganinta sosae suka sa ta gaba sae kallo suke, kursum tace kai kinga yanda kika yi wani fresh da kyau intisaar, intisaar ta galla mata harara tace "a inda bbu fresh din da kyau ba," duk suka dinga dariya, ita kanta tasan tayi kyau sosae, ramewa kadae ne tayi, inna tace "ku rabu da ita ciki ne da ita" nn da nn intisaar ta hade rai tana kallon innar, suko sae tuntsira dariya suke, inna kuwa ko a jikinta sae tauna goranta take, suna xaune a hka Aliyu ya shigo falon duk suka yi tsit bayan sun gaishesa bnda intisaar dake ta xuba abinta bata kara kallon inda yake ba, ya daka mata tsawa yace"kina jiran abba yaxo ya same ki a nn ne, kafin ki gaida shi," ta mike da sauri tace "lah na manta," ta ja gyalenta tabi ta gefensa ta fice daga falon tayi bangaren Abba, ya bi ta a baya, su xainab suka kwashe da dariya inna na taya su. . Da fara'arta ta shiga falon Abba ta rungumesa tana dariya tace"Abbana ina yini," shima yyi dariya ya amsa yana kare mata kallo snn yace "baki da lafiya ne fateema," ya juya ya hade rae yana kallon Aliyun da ya nemi kan tiles ya xauna yace "bata da lafiyane," ya fara kame kame kmr munafuki yace "Abba lafiyarta qlau ka tambayeta," abba yace wae hka fateema, Aliyu ya gyada mata kai da sauri yana kallonta, ta galla masa harara, snn ta mairaice murya tace "ni Abba makaranta nke son na koma lkci yana ta wucewa,"Haiydar Abba ya juyo yana kallon Aliyu yace, "amma lst tym da ka xo nn nai maka maganar karatunta me kace min," Aliyu aka fara kame kame da shafa kai "No Abba dama fa, dama tun lkcn nayi mata magana tace min ba ynxu ba tukun shine yasa ma ban sake mata maganar ba," Abba ya juya yana kallon intissar da ta tsaya kallon Aliyun da mamaki, yace"wae hka ne fateema" Aliyu ya shiga gyada mata kai wae tace hkne, ita kam ta rasa dalilin da yasa taga Abba da Aliyunsa kmr basa shiri kmr da, don dae tasan duk iskancin da Aliyu yake da wuya abba yace masa komai sae dae yyi ta kallonsa, yau kumataga ya hade masa rae kmr wanda yyi masa babban laifi, ta kalle Abba tace "ehh abba ya taba min mgna sau daya," Abba yace "ok, wni makarantar kike so," tace "bayero Abba," "medicine kika ce xa kiyi ko," ta gyada ma Abba kai, Aliyu yace"ke din ce xaki iya medicine? Abba baxata iya ba" abba ya galla masa harara yace "kai din da kayi kai goma gare ka?" Aliyu bae ce komai ba ya kauda kansa, Abba yace "sae kaje kayi abinda ya dace, ta fara karatu vry soon, idan nace vry soon, i mean vry soon" ba tare da ya kalle abban ba yace "to abba," intisaar ta mike tsaye tace " Abba sae anjima, ngd" abba yace "yaushe xaku koma gida," ta dan sace kallon Aliyu tace "aa abba ni kwana xanyi dama" Aliyu ya juya da sauri yana kallonta, amma bae ce komai ba, abba yace "to shiknn nima fita xanyi sae na dawo, ina da magana dake " tayi ma abba Allah ya kiyaye snn ta fice daga falon. Aliyu ya mike yyi masa sallama shima ya fice, da sauri ya bi bayanta,amma tuni har ta shige falon inna, ya shiga falon shima ransa a hade yace "wllh xuwa karfe shidda kishirya kafin na dawo," ya fice daga falon, ta tabe baki, tana kallon inna da ta bude baki tana kallon bakin kofar da ya bari, intisaar tayi dariya tace "innarufe bakin," inna tace "ae abun ne kmr wani mahaukaci," ynxu irin xaman da kuke yi knn intisaar, intisaar ta tabe baki tace "wae don nace xan kwana shine wae baxan kwana ba," inna tace"to uban me xaki masa a gidan, manta dashi kawae ai in kin koma gidan nn ke da kanki kika ce xaki koma," intisaar ta dinga dariya da jin ddin abinda inna ta ce mata, nn suka dinga hira har dae intisaar tace ma inna bari taje wajen momy, snn ta yi bangarensu. Bayan sllhn isha'i Aliyu ya shigo gidan,intisaar har ta fidda rai da ganinsa ta yi xaton ya hkura ne, ya tsaya masu kmr soja a bakin kofa wae ta tashi su tafi, intisaar ta yi kmr bata gansa ba tanata kallo abinta, kiri kiri inna tace bbu inda xae je da ita, kwana da kwanaki xata yi a gidan, sae ta gaji don kanta tace xata koma, ya hade rai yana ta kallon intisaar din dake kwance kan kujera tana taunar cingam, ko kallon inda yake ma bata yi ba, yasauke ajiyar xuciya tare da kwantar da murya ganinba ihunsa xae sa inna ta basa intisaar ba yace "don Allah inna ki bari, akwae fa inda xamu ynxu," ya kalle intisaar din yace "kiyi mata bayani mana fateema, wllh xuwa nxt wk sunday xan kawo ki kiyi sati ma idan kina so," intisaar ta tabe baki tace "ka dae je kawae nxt wk sunday din sae ka xo daukata," snn ta mike ta shige bedroom, ta barsa nn a tsaye, inna tace "to ka dae ji," snn ta kashe wutan falonta tace "Allah ya bamu alkhairi nima kwanciya xanyi, sae da safe," snn ta shige dakin ita ma ta kullo kofar.aleesat HaiydarAliyu ya kasa cewa komai sae kofar dakin da ya tsura ma ido, ya dde wajen a tsaye, can dae ya juya ya fice daga falon ya rufe kofar, inna na jin fitarsa tace "munafuki kawae, ki kwantar da hankalinki, ke da barin gidan nn sae ran da kika ce xaki tafi," intisaar ta gyara kwanciyarta don dama har tayi shirin bacci tace "kin ma san mene inna, bari na yake ni kadae fa kmr mayya a gidan, kuma bae ma san ci na da sha na a gidan ba, sae nayi sati ban gansa ba ma," inna ta bude baki tana kallonta "ke 'yar nn da gske," ta tabe baki tace "uhum ke dae barikawae, wllh kuwa inna," inna tace "to ni ae ca nke ciki ne da ke," intisaar ta galla mata harara tace " kaji ana mgnar arxiki wnn tsohuwar wae ciki, cikin lafiya, ni bnda komae" inna tace "ikon Allah, kina nufin har ynxu bbu abinda ya shiga tsakaninku intisaar" intisaar tayi mata bnxa ta juya mata baya snn ja bargo ta gyara kwanciyarta, inna xata yi magana wayarta ya shiga ruri, . ta mike da sauri ta dauko tana cewa "ina xan danna ke," intisaar tace"kai inna shekararki nawa da wnn wayar amma har yau baki san ina ake dannawa ba," inna tace "aa wani lkcn rudewa nake yi ne wllh," da kanta tayi pick din wayar dan intisaar kin mikewa tayi, ta doka uban sllma tana tambayar wanene, can kuma tace"A'a Bukar ne, lfya? Ayyo na ba fateema, to ga ta nn," inna ta mika ma intisaar wayan, intisaar gabanta yafadi ta amsa a sanyaye tace "Na'am Abba," murya can kasa tace "to Abba," snn ta kashe wayan, sae tafashe da kuka, inna ta rude "ke lfya me ya faru?" cikin kuka tace "kina ganin inna hada ni da abba yaje yyi ko," inna ta hade rae "to uban me Bukar din yace maki ynxu," ta goge hawayen idonta tace "waenaje yana nemana," inna tace "to bbu inda xaki je yi kwanciyarki, ni nn Rahmatu nace bbu inda xaki je, idan Bukar din ya isa yaxo ya tunkareni" intisaar ta mike tsaye ta dauki hijab har kasa tasa tace "ba dani ba xa ayi wnn ba inna, Abbana na kirana xanje na amsa kiransa," snn ta fice ta bar ta nn a tsaye. A hankali tayi sallama falon abba ta shiga, suka yi idohudu da Aliyu dake xaune falon a kasa gefen abba, ta nemi guri ta durkusa ta gaida abba, ya amsa yana kallonta yace "ki shirya maxa ku wuce gida fateema," a sanyaye tace "to abba" don bata iya ma abba musu, abba yace "ynxu meye naki a wajen inna, xainab taje ta dauko maki," ta girgixa kai tana kkrin maida hawayen idonta tace "bbu komai, kawae jakata ne, wani lkcn xan dauka," Abba yace"yauwa fateema, maxa tashi kuje kuyi ma momyntaku sllma, ku kama hanya ku wuce gida," ta mike tsaye ba tare da ta bari abba ya ga hawayen da take yi ba ta fice daga falon bayan tayi masa saeda safe , Aliyu ya mike shima yyi masa sae da safe, ya bi bayanta, bae ce mata ba, ita ma bata ce masa ba har suka isa sashinsu, falo suka tarda momy, ya nemi kujera ya xauna ya gaidata kmr wani munafuki, ta amsa batare da ta kallesa ba, ita dae intisaar tv kawae take kallo, suka dde a falon a xaune momy na gyara ma ihsaan gashi na xuwa sch gobe, ganin har karfe goma ya wuce Aliyu ya kasa tashi ne yasa intisaar ta mike tana kallon momyn tace "momy xamu tafi sae da safe," tace"Allah ya kaimu, . Aliyu ma ya mike tsaye yyi mata sae da safe tayi kmr bata ji sa ba, ya ajiye ma ihsaan dubu biyar ta sha ice-cream snn suka fice, ita kam bata ga laifin momy ba. Har suka isa gida bbu wanda yyi magana tsakaninsu, shi dae ne ke ta waya da safeenah suna soyewa, yana parkin ta bude motar ta