← Book details Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fice tayi cikin gidan da sauri, ya bi bayanta tun kan ta hau sama ya risketa ya fixgota, yace "direct bedroom dina xaki shiga, ba sae kin shiga naki ba," ta turasa tana masa wani irin kallon raini, "nayi maka uban me," bata rufe baki ba ya dauketa da mari, ta fasa ihu ta durkushe wajen, ya bita da sauri, ya rikota, kuka ta shiga yi tana ihu, dukya gigice ya rungumota yace " don Allah kiyi hkuri fateema, am vry srry," ko sauraransa bata yi ba taci gaba da rusa kukanta, ya dauketa cak, ya hau sama yyi bedroom dinsa da ita, duk irin yanda yaso intisaar ta basa hadin kai kin yrda tayi, don kuka ta dinga masa sosai tana rokansa yyi hkuri bata so, hkn yasa ya kyaleta kawae yyi kwanciyarsa bayan ya lallasheta yace tayi baccinta baxae mata komai ba, ta jima bata yi bacci ba sbda tsoro, gnin kmr Aliyun yyi bacci ne yasa ta dan kwantar da hankalinta ita ma ta fara baccin, duk da kuwa idonsa biyu ba baccin yyi ba, yana ganin ta fara bacci kuwa ya mike ya bar mata dakin ya kohaleesat HaiydarDa asuba Aliyu ya shigo dakin yin alwala, tayi shame-shame hankali kwance tana bacci, kallo daya yyi mata ya dauke kansa ya shige bathroom, yana fitowa ya bude fridge ya dauko ruwan gora mai sanyi ya bude ya xuba a hannunsa ya watsa mata, ta mike xaune a firgice tana kalle kalle, ya juya ya fice daga dakin ya wuce masallaci, ta yi tsaki, a xuciyarta tace Allah ya isa na, snn ta mike tsaye ta shige bathroom tayi alwala, tana idar da sallah tayi jigum a dakin, can dae ta mike xata fita idonta ya sauka kan wayarsa da yyi haske a gaban mirror, ta dan kalli bakin kofar snn ta karasa ta dauki wayar, taga msg ne, ta bude taga na safeenahne, ta tabe baki bata damu ta karanta ba ta fita daga inbox din kawae,. ta xauna gefen gadon wayar a hannunta ta shiga hotuna, duk hotunansa da na safeena ne, wasu yana rungume da ita, wasu tana kwance jikinsa, wasu suna kiss, gasu nn dae ba kyan gani, duk da ba son Aliyu take ba sae da taji baddi, wani bakin ciki ya dinga yawo a xuciyarta, tana nn a hka har Aliyu ya shigo dakin tayi saurin boye wayar cikin hijab dinta, ya galla mata harara yace"fice min a daki kar nayi ball dake," ta mike ta fice daga dakin ba tare da ta kallesa ba wayar tasa a hannunta, yyi kwafa yace "xaki gane kuranki ne yarinya," har Aliyu ya fita ranar bata ji yyi mata maganar wayarsa ba, gabanta kuwa sae faduwa yake kar yaci ubanta. Da yamma wajen karfe biyar tana kwance a daki tana kallo, aka bude kofar dakin ta mike xaune a dan tsorace tana kallonsa, daga bakin kofar yace "ina jiranki a falo, kuma kar ki fito min da shigar nn na iskanci," ta tabe baki ta ci gaba da kallonta kawae, bayan kmr minti goma ya sake dawowa, ta mike a dan tsorace yace "kina hauka ne,me nace maki," ta hararesa tace "gani nn xuwa," yyi murmushi ya juya ya wuce, ta dauko hijab dinta har kasa tasa ta sauko falon, dama tasan bako na falon tunda har ya kira shigar ta ta iskanci, da can da take sa wa bae san na iskanci bne, ta karaso falon ta xauna tare da gaisuwa "ina yini," ya dago yana kallonta yyi murmushi yace "lfya fateema, ya gida ya amarci," komai nata ya tsaya cak ganin faruuq, ta kasa dauke idonta daga nasa, shi kansa yanayinsa ya canxa duk da yyi kkrin boyewa, yyi yake yace "kai wnn kallon kmr kin ga dodo intisaar,"ta dauke kanta da sauri ta kasa cewa komai ga hawayen da taji na neman cika idonta, Aliyu yana danna wayarsa duk da hankalinsa na kanta yace "kikawo masa ruwa mana" da kyar ta mike jikinta a sanyaye tayi hanyar kitchen ta dauko faranti da cupta daura juice da ruwa a kai ta dawo falon ta dire gabansa, yyi murmushi yace "thank yhu fateema" . tajuya xata bar falon Aliyu yace ina xaki, hira yaxo kuyi fa, kin juyowa tayi sae da ya sake kiranta snn ta dawo ta xauna tana kirkiran murmushi, Aliyu ya mike ya bar falon yana mata wani irin kallo, ko lura da hkn ma tayi, faruuq ya dago yana kallonta yace"kinyi mamakin gani na ko," bata ce komai ba yyi murmushi yace "ya amarci," nn ma shiru tayi, "yace common fateema, baki yrda da kaddara bne, ki tuna fa matar mutum kabarinsa," ta gyada masa kai kawae, yace "cheer up kanwata," tayi murmushi kawae, yace "yauwa ko kefa," nn dae intisaar ta sake suka dinga hira da faruuq din kmr ba komai, Aliyu ya sauko ya xauna falon shi dae bae sa masu baki ba sae dae yyi murmushi, intisaar tace "yayanain xubo maka abinci to?" faruuq yace "haba dae sae kace jaki daxu fa muka ci da Aliyu," ta juya tana kallon Aliyun ya harareta ya dauke kai, faruuq bae bar gidan ba sae kusan maghrib, har bakin kofa ta rakasu da yake shi da Aliyun xa su fita kuma, tace"yayana ina da magana da kai fa," ya juya yana kallonta yace "ina jin ki kanwata," ta harare Aliyu daya xuba masu ido tace "ba da kai nke ba," yyi murmushi yyi gaba, faruuq yyi dariya yace "to ina ji,"tace "yayana dama nace don Allah don annabi, tunda Allah yyi ni ba matarka bace, to ka nemi 'yar uwata mana," ya juyo da sauri yana kallonta yace"wa?" tace "zainab," ya harareta da wasa ya juya xae wuce tace "haba yayana, abinda yyi zainab shi fa yyi ni, ni da xainab daya ne" yace "haba dae, da gske?" . ta lura yana son shashantar da maganar ne, ta dinga masa magiya kmr xatayi kuka, daga karsheyyi murmushi yace "shkkn kanwata xanyi shawara,"ta ce "haba yayana kasan fa ba talarta nake mka ba,tana da manema dayawa, kawae dae xumuncin mu nake so yyi karfi kuma...." yyi dariya yace "to shknn fateema, ngd da kulawarki sae da safe," ya juya da sauri ya bar wajen, tayi dariya ta daga masa hannu ta koma cikin gida. Bayan kwana biyu da xuwan faruuq intisaar na daki a kwance tana ta game da wayar Aliyu da ta mayar nata don har lkcn bata gansa ba bare ta sa ran xae mata maganar wayar tasa, hkn yasa ko da yaushe cikin kiran inna da Zainab take su yi ta hira don akwae kudi sosai a wayar, momy dai sau daya ta kirata suka gaisa, abun da ya bata mamaki bae wuce na rashinganin kiran safeena ba don jira kawae take ta kira tayi mata rashin mutunci amma har lkcn bata kira ba kuma bata yo tex ba, sau dayawa kiran abokanansa da 'yan mata kan shigo amma ko sau daya bata taba dagawa ba, ta goge duk hotunan haukan da sukayi da safeenah dake cikin wayar, snn tayi deletin tex din safeenar da na mata da dama a wayar, karar bell taji downstairs ta mike a dan tsorace don Aliyu baya dannabell, ita tun ranar ma da ya fita raka faruuq bata sake ganinsa ba, kar dae Hajiyarsa ce ta dawo don ita tsoran matar nn take, a tsorace ta sauko kasa cikin sanda ta isa bakin kofar ta dan leka ta glass taga Anty Nafisa ce, ta bude kofar tare da doka tsalle ta rungumota tana mata oyoyo cike da farin ciki, Anty nafisa tayi dariya tace "ni kar ki karya ni," suka shigo falon intisaar na tambayarta Maryam fa, meyasa har ynxu bata xo ba, Anty nafisa tace sun fita waje da abbanta ai, intisaar tace Anty mu hau sama mana, Anty nafisar tace "ina fitsararren mijin naki," intisaar tace "uhm baya nn," snn ta mike ta kawo mata lemo a fridge ta dire mata a gabanta tana tambayr ya su shaheed da ummi, Anty Nafisa tace suna nn lfya, snn ta mike ta hau sama tana cewa "bara naje naga dakin amarya," intisaar ta bi ta a baya tana dariya, hira suka dinga yi da Anty Nafisa tana bata lbarai, duk da anty nafisar taso jin irin xaman da suke yi da Aliyun, amma intisaar ta dinga shashantar da batun, karfe sha biya tace bari taje ta daura girki tunda yini Anty Nafisar xata mata, Anty Nafisa ta mike tana inspect din dakin tace "duk da dae nasan ke ba kaxama bace intisaar bari dae na dudduba ko ina, don randa naje gidan fadila duka ne kadae ban mata ba, gskya mijinta na kkri don fadila muguwar kaxama ce ta karshe," intisaar dae tayi dariya ta sauka kasa don ita kam tun tana karamarta take da kyankyani, kuma ko a gida ma inna na yaba tsaftarta, ko shakka bbu tasan Anty nafisa baxata ga datti ko kadan a dakinta ba, dama ko ina na gidan, lafiyayyar jollof rice da plantain sai farfesun kaza ta shiga girka ma Anty nafisa, ta dan hada mata cream salad kadan, snn tayi ginger drink, gidan ya kauraye da kamshin girkinta, tana jerasu a faranti don sama xata kai mata taji an rungumota ta baya, ta tsorata sosae xata fasa ihu ya juyo ta yasaka bakinsa cikin nata, ta turasa da karfi tana maida numfashi, "meye hka," ta tambayesa tana hararan sa yace "ni kika yi ma girki?" tayi masa wani irin kallo tace "kai a su wa," ya tabe baki yace "kinga ina cin ko wani girki? Ae wnn kaxanta ce kika hada," bata kara ce masa komai ba ta gama jera abincin a faranti ta dauka xata bar kitchen din, ya fixgota, saura kiris farantin ya fadi daga hannunta, ta xaro ido tayi saurin ajiye farantin kan table, "wae meye hka don Allah," ta tambayesa kmr xatayi kuka, yace "to dibar min nawa," ta galla masa harara tace "ban yi girki da kai ba, kai da ba ko wani girkikke ci ba," yace "to kuwa baxa ki bar kitchen din nn yau ba knn," ta ce " Anty Nafisa na jirana fa a sama," ya dan wara ido yace "Nafisa? metaxo yi?" muryar Anty Nafisar suka
Chapter 22 · 0% Book details