Sashe 4
Inteesar Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan ta kashe ac dake dakin ta lulube tadalilin rawar sanyin da takeyi, ranar dae daga ita har momy basuyi bacci ba, momy ta rasa abinda ke damun 'yar tata, duk ita ma hnklinta ya tashi. Gari na wayewa momy taje ta sami abba ganin yanda jikin nata yyi tsanani, gashi sae aikin kuka take, duk ita ma tabi ta daga hnklinta don akwae soyayya da shakuwa mai karfi tsakaninta da 'yar tata don ita kadae take gani taji ddi idan ta tuna mijinta na farko umar, har daki abba ya shigo duba intisaar din, "me ya sameki fatima, ina ke maki ciwo?" ya tambayeta dadamuwa yana yaye bargon da momy ta lullubeta dashi, ita dae ba baki sae kuka, abba yashiga lallashinta yana cewa"damabaki da lfya ne fatima, kuma bakiyi maganaba tun jiyan?" ta girgixa masa kai kawae, xainab tashigo dakin hankalinta a tashe bayan ta tambayi ihsaan ina intisaar don ita har tayi shirin islamiyya da yake tare suke wuce, ihsaan tace mata "my aunty is sick," hkn yasatayo bangaren nasu da saurinta, abba ya dubi xainab da tashigo yace"je ki ki kiramin Ali xainab," tace to sannan ta fice da sauri, a hanya suka haduda kursum take tambayrta ko intisaar ta shirya don ita ma shirin islamiyyar tayi, tunda Aliyu yyi masu mugun duka ranannan suka fara xuwa makaranta gaba dayansu dama, xainab tace "bata da lfya baxa taje ba," kursum tace "hva de me ya sameta," xainab ta yarfehannu tace nima bn sani ba ynxu ma ya Aliyu xan kira abba ma yana can, kursum tayi sashin nasu da sauri xainab kuma ta tafi kiran Aliyu, tana isa tayi sllma ta shiga palon, baya nan, tayita kwada sllma ko yana cikin daki amma shiru, sanin halin yayan nata ne ya sanyata karasawa cikin bedroom din nasa yana ko xaune laptop a gabansa yasa earpiece kunne daya yana danna laptop, ya daka mata tsawa a fusace yana cewa"baki da hnkli ne don ubanki ko ke jahila ce,baki san idan kika yi sllma a waje kika ji shiru gaba xakiyi ba, xaki afko min cikin daki, ban hanaki wannan habit din ba," au ashe ma yana jinta, ta tabe baki cikin rashin damuwa tace "dama abba ne ke kiranka" ta juyafuu xata wuce ya mike da sauri yana cewa "xainab, xainab," amma bata tanka masa ba, ya fito palon da sauri har ta fice ya bita da sauri yana kiranta, ta dawo tana kallonsa fuskarta a hade tace"gani," me yasa abba ke kirana, ya tambayeta yana kallonta don dae yasan sae da dalili ake kiransa, don kan abba ya kirasa sau daya ya kira haisam sau goma,"nima ban sani ba, intisaar dae ce bata da lfya shine yace naje na kiraka" ta fadi tana kallonsa, gabansa ya fadi yace "to menayi ake kirana" tace "ni kuma ina xan sani" hnklinsa ya tashi yace "me tace wa abban?" tace "oho, ni ina shigowa abba yace nayi maxa naje na kiraka" don ta gaji da tambayoyin nasa, bai damu da ohon datace masa ba ya kara tambayrta "ya mood din abba yake" tace a kage "kai yaya ni ma ban sani ba abba nacan yana jiranka," ta juya ta yi gaba ta barshi nan a tsaye. Ya bita da sauri kuma yana kiranta, ta juya rai bace tana kallonsa yace "ina abban?" tace"yana can dakin momy" ya xaro ido yace"yana me?" tace "oho! tayi gaba abinta" ta fara suspect dinsa ita kam. Tana komawa sashinsu intisaar abba ya tambayeta meya tsayar da ita kuma ina Aliyun, tace"nemansa nke a gidan abba amma gashi nan xuwa" ya dubi momy da ta xauna tayi jigum yace "ki hado mata tea xainab," ta mike tace to sannan ta fita, tana fita sae ga inna, tun daga waje suka dinga jin muryarta kmr speaker tana cewa"me ya samu intisaar din, ni rahmatu," abba ya juya rai bace yana kallonxainab yace "donuwarki ca nayi ki ji ki gaya wa inna taxo ta daga mana hnkli a nan ynxu?" xainab ta mike da sauri ido a waje tace "wllh tllh abba ban je wajen inna yau ba ni," abba bae sake cewa komai ba har inna ta shigo dakin, "bukar me ya sameta wae" abba ya dubeta yace "shine ae xa a dubata don bbu wanda yasani," inna tasaki salati tana girgixa kai tace "Allah ubangiji dae ya bata lfya wllh duk hankalina ya tashi da aka je aka gya min," abba bae sake tanka mata ba tana ta surutanta, illa Aliyun da yake jira, murya can ciki Aliyu yyi sllma, duk jikinsa yyi sanyi, ynxu yarinyar nan sae ta iya bude baki tace yyi mata wani abu dama, inna ce ta amsa masa da karfinta tana cewa "maxa shigo," hankalinsa ya kara tashi ya shigo palon ya tsaya yana waige-waige kmr munafuki, abba yace"karaso mana" da kyar yyinamijin kkri ya shiga dakin, ya rusuna ya gaida abba don duk yau bai je gaisheshi ba gashi har karfetara, ya juya ya gaida inna ma sannan yace"abba gani," . Dama fatima ce bata da lfya, shine nace a kiraka ka dubata, abba ya fadi yana kallonsa, Aliyu ya saki ajiyar xuciya, sannan ya maida dubansa ga kangadon yana kallonta, idonta a lumshe yake, duk da dae ba bacci take ba, ya karaso kusa daita yace "meke damunki?" tayi shiru kmr mae bacci, hkn ya bata masa rai don yasan idonta biyu, a dan fusace yace"kinajina xakiyi min banxa?" inna cikin tsawa tace "kai mahaukacin wani gari ne, baka ga bacci take ba yarinya tana fama da kanta xaka dinga mata ihu," xainab ta karasa kusa da ita tana bubbuga kafarta a hankli tana kiran sunanta, ta bude ido tana kalln xainab din, Aliyu ya juya yana kallon abban nasa yace "ko dae a wuce da ita clinic kawae abba" inna tayi karaf tace"wllh bbu inda xa a kaita, gamu da likita a gida kace xa a wuce da ita wani wajen, meye amfanin ka" Aliyun ya dubeta rai bace yace "to ni din Allahn musuru ne da xan san abinda yke damunta," cikin tsawa inna tace "shiyasa naga an kai fadila asibitida bata da lfya, don ubanka ba kai ka dubata ba ka bata magunguna da allurori ba kuma gashi nan ta warke," Aliyu ya dubeta a walakance ya kauda kai kawae, abba yace "shknan bari a kaita asibitin ka iya tafiya" da sauri yace "aa abba bance baxan dubata ba ae, guri nake jira su ban na dubata," ya fadi yana kallnsuinna, haisam ya shigo dakin da sllmrsa ya karasa kusa da intisaar din ya xauna cike da damuwa yana kallonta yace "intisaar me ya sameki, dama jiya baki dalfya baki yi magana ba," ta sunkuyar da kanta kawae sae hawaye, nanya shiga lallashinta, ya dube abba yace "asibiti xamu wuce abba?" inna tace "asibitin lfya ga likita a gida, ynxu xae dubata ae" sllmrsu hajiya da umma ne yasa kowa yyi tsit a dakin, momy ce kadae ta amsa masusuka shigo suna cewa ashe abinda ya faruknan, momy ta basu waje suka xauna sannan suka gaisa, suka tambayeta mae jiki tace masu da sauki, hajiya tace Allah sarki duk ta rame sae kace warce tayi sati tana jinya, umma tace wllh kuwa baiwar Allah, inna ta tabe baki tace "ikon Allah" xainab ta girgixa kai cike da takaici, ynxu har anje an barbada masu shine suka kwaso jiki suka xo gulma, kumatasan baxae wuce kursum ba ko rahma, abba ya dubi gaba dayansu yace "to ae kwa bashi waje yyi aikinsa de ko" hajiya ta mike tana cewa"me xae hana, Allah dae ya bata lfya yasa xakkan jikine," suka mike gaba dayansu har da yaran xasu bar dakin, Aliyuyace "to..to abba ya xa ayi treatin din nata?" abba da har ya kai bakin kofa xae fita ya juya yana kallonsa cikin rashin fahimta yace "kmr ya fa?" yace"aa...dama...emm, to to ae naga sae da magunguna da allurori xa ayi treatn din nata, kuma ni...." sae kuma yyi shiru yana kallon tagan dakin, abba yyimurmushin takaici ya girgixa kai yace "to nawa xa a baka?" inna ta mike ta saki salati tana girgixa kai tace "ita intisaar din sae....." da sauri abba ya katse ta yace "aa baaba ae hakkinsa ne bari a basa" nawa ne kudin treatment din gaba daya? Abba ya tambaya yana kallonsa, cikin bacin rai haisam yace "abba ka bari na wuce da ita asibiti kawai," abba yyi saurin cewa "aa haisam ka bari xae dubata," abba ya sake tambayrsa nawa xae basa, yyi shiru kmr me lissafi sannan yace ba tare da ya kalli abban nasa ba "dubu takwas da dari biyar gaba daya," abba yyi murmushi, haisam cike da takaici yace "to yyi kyau, ka dubatani xan baka," da sauri ya juya yana kallon haisam din rai bace yace "to da baki na xan siyo kayan ne koya? Ko kuma ina da kudin xan tsaya cewa abba ya bani," inna cikin ihu tace "Allah ya babbake mae krya sannan ya tsinemasa," Aliyun ya juya ya galla mata harara sannan ya dauke kansa, haisam ya ciro dubu biyar daga aljihunsa ya mike xae fita abba yace ina xaka, yace xan dauko kudi ne,abba yace nawa ne a wajen ka ynxu, yace dubu biyar, abba ya ciki dubu hudun haisam ya mikawa Aliyun ya karbe yana kirgawa, duk wannan abinda akeyi a kan idonsu hajiya ne, hajiya taji kmr ta maida dan nata ciki don murna, sae murmushi take yi, umma kuma ji tayi kmr ta tsine ma haisam da bai yo hali irin ta Aliyu ba, shekaranjiya tace ya bata dubu goma yace bai da, amma sae gashi ynxu ya kirgo har dubu biyar ya bada don a duba wata bnxa ita kam bata san irin dan da Allah ya bata ba, momy kam sunkuyar da kanta tayi tana jin duk abinda sukeyi cike da takaici, intisaar kuwa idonta ta rufesbda axabar da take ji ko ina na jikinta ciwo yke mata barin ma kanta sannan kuma ga ciwon mara shima ya kunno kai, abba kam tuni ya fice su hajiya suka bi shi a baya a xuciyarsu suna fatan Allah yasa cikita yo, don rahma ca tayi masu amai take ta kwararawa, Aliyu ya dube inna yace"a bata tea kafin