← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 65

Sashe 9

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karba tayi cikeda godia jikinta duk a mace da yanayin malam din sbd ko magana bayason yi Kai kawai yake gyadawa Majeed din alamar godiya.

Fita sukayi Yana riqeda hannun Inayar suka nufi makaranta Saida suka qarasa bakin kofar makarantar ta juyo tana kallonsa fuska a Dan shagwabe ta bude madaidaicin bakinta tace"

Abbi Idan kaje asibiti taredasu Umma yaganah waye zaizo ya tafi Dani Idan an tashi?
Na tafi na da kaina abbi Zan iya.

Fararen idanuwansa ya saukar Mata a  'dan bude yace"

Koba yau ba duk ranar Dana samu kin fita kinbi hanya da kanki zakisan Hukuncin dazan dauka akanki,

Kina kina?
Gyada Kai tayi tareda sake cewa"

To Abbi na zaunane nayita jira har kazo?
Umma yagana Bata makaranta Idan antashi zanji tsoro aka barni,
Kazo da wuri kaji Abbi???

Gyara Mata zaman hijabinta yayi Yana gyada Kai cikeda kulawa yace"

Kidai jirani kinji abinda na fada,
Wuce karkiyi latti,
Allah ya bada saa.

Amin Abbi.

Juyawa tayi ta shige ciki shikuma ya juya ya tara mashin ya hau ya nufi gurin aiki Kai tsaye.

Bai wani jimaba gurin aikin ya bayyanarwa da manager uzurinsa ya fito ya kama hanyar asibiti sbd Yagana ta sanar masa suna Isa anbasu gado.

Koda ya Isa asibitin jikin malam din yaqara tsanani sosai Kamar Kar a iso dan haka ya karba takardun magani da abubuwan da aka rubutan.

Ba wasu kudaden ne dashiba shima Amma haka ya tafi gurin siyan maganin Dan yaji ko nawane kudin.

Ana Gama duba takardar a pharmacy aka miqo masa kudin a rubuce.

Dubu talatin harda shida da wata dari  takwas akai yagani rubuce.

Ajiyar zuciya tareda numfashi ya sauke a hankali tareda kallon Mai shagon a hankali ya furta"

Nagode" ya juya ya wuce yabar gurin.

Bayada ko dubu goma a halin yanzu Dan kuwa duka duka dubu shida ce a account dinsa Kuma koshi kansa baya tabata Dan na siyayyar Inayah ne na abincin zuwa makaranta daya kusa qarewa.

Kallo takardar ya Kuma yi tareda sake lumshe fararen idanuwansa cikin tsananin tausayin malam din da yaganah.

A iya fahimta da Dan sanin da yayi musu yasan basuda kowa sai junansu,
Yasan dai Yan asalin jahar borno ne suna cikin Wainda sukayo gudun hijira tunda dadewa dangi da sauran Yan uwa duk sun mutu wasu Kuma Suma sun fada wata duniyar suna ganin garari.

Fuskarsa ya shafa ahankali kafin ya juya ya nufa titi Dan hawa mashin yakoma gurin aikinsa ya gwada rokon manager albashinsa na Wannan watan idan zai samu yanzu koba komai saura sati daya watan ya qare.

Kokarin tare mashin yake Yar qaramar wayarsa ta Itel ta ringa vibrating sbd ya kashe qararta bayaso.

Ciro wayar yayi daga aljihu yaga sunan yaganah ya dauka Yana cewa"

Assalamualaikum" cikin nutsuwar muryarsa Kamar kodayaushe.

Wata sanyayyar ajiyar zuciya Mai zafi tareda mutuwar jiki yaganan ta sauke kafin tace"

Abdulmajeed kadawo kawai malam yariga ya tafi lokaci yayi...
Wani irin kuka Mai sanyi ta fashe dashi tareda kashe wayar sbd sai alokacin kukan ya zo Mata.

Innalillahi wainna ilayhirrajiun" ya furta Yana maida wayar aljihu ya tsallaka titin yakoma cikin asibitin Yana jinjina Kai cikin jimamin mutuwar.

Kuka sosai Yaganah keyi daqyar ya iya furta Mata kalmomin ban hakuri da tawakkali dazai iya furtawa shima.

Basuda wani jamaa dagashi har ita yaganar har malam din Dan haka babu maganar tsayawa Jan lokacin jana'iza
Asibiti na Gama nasu aikin suka Basu gawar suka dawo gida da ita.

Sosai jamaar gidan Dana anguwa suka nuna alhininsu akai masa sitira aka kaisa.

Bai samu zuwa maqabarta ba sbd gabaki daya hankalinsa daya rabu biyu Yana kan Inayah da aka tadasu makaranta lokacin Dan haka makarantar ya wuce Kai tsaye ya daukota suka dawo gidan yabarta gurin yagana yabi sauran Wainda zasu maqabartar suka wuce.

Babu wani zaman karban gaisuwa dasukai saidai Wanda yazo yaje har kofar dakin yagana yayi Mata gaisuwa ya wuce sun daiyi Mata tasu karar sun zauna ranar daya rasun daga ranar saidai masu zuwa jefi jefi har akai sati biyu.

Tunda akai rasuwar babu ranarda Inayah Bata fashin makaranta zai kaita da kansa ya wuce aiki
Idan lokacin tashi yayi zai Baro gurin aikinsa ya rakota gida kafin ya koma.

Wani sabon Nauyin ne yakuma hawa kansa na Yaganah sbd kallok uwa dayake Mata gakuma tausayin halinda take ciki din na Rashin miji,Dan uwa,abokin fira,abokin rayuwa Wanda suke tare tun kuruciya gashi ko tashin hankalin daya sakosu gudun hijira Bai rabasuba sai yanzu da Mai gaba daya tazo wato mutuwa.

Sbd matsayin Yaganah agun Inayah yasa Dole ya dauki nauyinta ya ratayawa kansa Dan haka yanzu komai nasu tareda ita yake siya sbd ko aikin ta daina zuwa Dole sbd takaba,

Ta wani bangaren Kuma mutuwar ta tabata sosai Dan komai ya fice Mata arai
Daqyar Inayah ke samu tana dan sakata magana wasu lokutan.

Rasuwar tasa Dole yakoma ya saki gidan daya kama ya karba kudinsa kafin Yaganah ta Gama zaman takaba zai nema musu wani Mai Yar damar Inshallah.
Dan haka kudin saiya tattara ya hada ya siya musu abinci isasshe da siyayyar makarantar Inayah suka shiga jss 1.

Watan malam din shida cif da rasuwa sukabar gidan suka koma sabon qaramin gidan daya kama din Wanda yamafi na farkon kusa da gurin aikin nasa,

Dakuna biyu ne a gidan da qaramin toilet harda broken tiles dinsa.

Daki daya ya dauka
Dayan Kuma haka Dole dai yaganah da Inayah suka zauna daki daya Amma wasu kayan nata na dakin baban nata sbd sabo.

Katifar Inayah ta farko ya dauka sai ya siya musu wata Yar katifar Mai Dan girma tareda zanin gado da pillow sbd sanin Inayah da bacci da pillow.

Labulai ma ba laifi ya Samar musu iya daidai nasu sai kayan aikin abinci da kusan duk nasun ne na da.

Ahaka cikin Dan rufin asirinsu suka fara gudanar da rayuwarsu a sabon guri cikin nutsuwa.

Bayan tarewarsu anguwar Basu wani dauki dogon lokaci sosaiba Yan anguwar Suma suka gane halayensa na Rashin shiga mutane da kamewar Kai dan haka suke mutuntasa duk da zamansa matashi ba wani babba ba.

Kwarjinsa hadi da Kamun kansa da Rashin shigewa al'amuran jamaa musamman wainda Basu shafesaba yasa duk inda ya zauna ake mutuntasa sbd shi kamilin mutum girmamasa akeyi Koda baida wasu manyan shekaru.

Islamiyar dake cikin anguwar ya sakata tareda sauya Mata makarantar bokonma sbd waccan din tayi nisa Dan haka gabaki daya yanzu komai nasu ya Dan sauya,

Yagana ke girkin abinci da tsaftace koina na gidan ta sakewarta Takoma tamkar yanda take a da dinta,

Sosai take kulawa da Inayah tamkar jikarta data Haifa uwarta,
Shi kansa Baban Inayar yana cikin kulawar yaganan Dan kuwa abincinsa  baa Wasa dashi,
Musamman data fahimci shi Mai tsananin tsaftar gaske ne sai baa Wasa da qazanta a gidan ko kadan.

Yan anguwama ganin irin kauna da kulawa Mai girma dake tsananinsu yasa suke daukar yaganar a matsayin mahaifiyarsa.
##MAMUH#

*_For More pages ku garzaya arewabooks_*

#LOVE/ROMANCE#
#INAYAH#AYSHATOUH#
#ZAFAFA BIYAR

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS  4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_Mamuhgee 8_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Farkon zaman yaganah dasu duk wata Yana fidda kudin Albashinta na zama da kulawa da Inayah,

Lokacinda ya fara Bata kudin sosai ta nuna masa Rashin Jin dadinta sbd sune suka taimaketa bawai itace take taimakonsu ba,

Kai tsaye ta nuna masa Karya Kuma nuna mata kudi da sunan biyanta akan zaman datake da Inayah harma dashi..

Ganin ta nuna Rashin Jin dadin hakan sosai yasa Bai Kuma tinanin Bata dinba Amma Kuma bayajin ya nutsu da Rashin Bata Wannan haqqin nata Dan haka cikin dabara ya jata banki ya bude Mata account batareda ya sanar da ita asalin dalilin hakan ba,duk wata Yana Sanya Mata 3k a account sbd shi mutum ne da bayason haqqin kowa akansa,
Bayason Alfarmar mutane sbd Rashin yarda da kowa musamman akan sha'anin da duk ya shafi Inayah duk da yaganah ta musamman ce a rayuwarsu yanzu,
Tsananin qauna da shaquwar dake tsakaninta da Inayah yasa tasamu matsayi Mai girma a idonsa harma da wani bangare mai girma na zuciyarsa.

Haryanzu dasuke rayuwa da Umma yaganah shine maiyiwa Inayah wasu abubuwan Kaman koyaushe Idan zata Sanya Kaya tafi zuwa gurinsa ya zabar Mata Wanda zata saka,
Shine suke Cin abinci tare kaman yanda tasaba hakama bacci a dakinsa Saida Umma Yaganah tayi da gaske kafin suka samu ta daina kwana gurinsa sbd wani irin Sabone datayi da hakan tun tana jinjira tareda Mahaifinta take bacci harta Wannan girman shiyasa takasa sabawa da rayuwa ba gurinsaba.

Shi kansa duk dare ya ringa haske haske fitilar wayarsa Yana leqowa dayaji motsi sbd duk inda yake bayajin cikakkiyar nutsuwa Koda rana Koda dare Idan baya ganinsa guri daya da ita,

Allah ya sanyosa cikin irin iyayenda sukeda wata irin taka tsantsan akan tarbiya da safety na rayuwar 'yayansu,
Sam Sam bayada yarda ko nutsuwa akan komai indai gameda 'yarsa ne Cikinma ahakan yasamu nutsuwa sosai dakuma yarda matuqar sosai da Umma yaganah.

Umma yaganah tun Bata iya rayuwar Majeed dinba harta iya ta karance komai nasa musamman tsaftarsa dake wahalar da ita farko Amma daga baya ta saba shiyasa yanzu take tsananin Jin dadin rayuwarta dasu hankali kwance su ci Mai kyau da lafiya su Sha Mai kyau da lafiya.

Kullum safiyar fari yana dawowa masallaci yake ficewa morning jogging (gudun safe),
Koda yake dawowa Inayah tagama Shirin makaranta zai rakata makarantar yadawo yayi wanka wata ran ya tsaya yaci abinci kafin yafita wataran baya tsayawa sbd kaucewa lattin Isa gurin aiki,

Baida wani Abu dake gabansa bayan jajirwa tuquru akan aikinsa sai kulawa da gidansa,

Bayada aboki ko daya a yanzu,
Baya doguwar mu'amala da kowa data wuce ta aiki saita gaisawa da Yan gajerun abubuwan da baa rasaba na mu'amalantar mutanen.
Chapter 9 · 0% Book details