Sashe 30
Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miqewa yayi ya fice zuwa masallacin gidansa sallar ishai.
Ana Gama sallar yadawo ya rufe sashensa ya zauna Dan tattara abinda yake yawo cikin kansa Yana Neman juyawa.
Dafe gashi yayi Yana Jin gaban kansa kaman zaiyi bindiga tsabar nauyi da zafin daya dauka.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Meyesa wannan matar da Baya fatan sake ganin fuskarta har abada Zata bayyana rayuwarsa da 'yarsa a daidai wannan lokacin Kuma ta bullo ta mabulla mafi firgici da tashin hankali.
Tun a shekarun baya tsanarta ta ginu cikin ransa tsanarda tasa ya rufe shafinta ruf daga rayuwarsa gabaki daya Dan ko a kamanni baya fatan sake ganin Mai kamarta,
Shin ita dince ma kuwa wadda yake tunani kokuwa?
Bazai taba manta kamannintaba sbd itace ta taka mahimmiyar rawa gurin ruguza rayuwarsa a karon farko,
Itace wadda ta wargaza buri da gatansa na zama cikin iyaye da 'yan uwansa tasakashi a matsatsen hali mafi matsuwa da Muni.
Kamanninta Zane suke da baqin alqalami a idanuwansa,
'yarsa Inayah da girman mahimmancinta da qauna Mai tsanani ta uba da 'ya dayake Mata yasa ya yafewa matar Nan Amma Kuma har abada bayajin zai iya cire tsanarta Mai girma a ransa bare kallonta da daraja ko qima.
Haduwarsu ta farko da ita Bata Zama Alkhairi ba Dan hakan ko yanzu yasan bayyanuwarta rayuwarsa ba Alkhairi bane a rayuwarsa data 'yarsa Dan haka Dole yanason Jin amsa biyu rak daga bakinta daga ya samu amsoshinsu bazata Kuma ganinsaba dagashi har 'yarsa har abada.
Shi idan Yana cikin damuwa ko tashin hankali Sam baa wani ganewa sbd alokacin nutsuwarsa da kamewarsa take fin yawa,
Shiru yakeyi Yana nazari batareda buqatan hayaniya ko katse Masa nazariba shiyasa su Inayah dasun gansa irin yanayin suke yin tsit gidan duk da dama ba hayaniya ce dasuba gidansu.
*******Qarfe goma da mintuna Ashirin ya fito harabar gidan sanye da black hoodie Thom Browne Riga da wando masu kauri ya nufa White jaguar motarsa ya bude ya shiga tareda tada motar ya nufi gate dama tuni Bosco yaga fitowarsa da sauri ya bude Masa gate ya fice.
Yana fitowa daga street din gidansa motar Abdulsamad Tasha hanasa tareda danno Masa full light.
Wani banzan numfashi ya saki tareda Dan juyar da kansa cikin takaici da baqin ciki ahankali yace"
Wannan matar tabbas zatasan waye AA MAJEED.
Babu tantama yasan itace a motar Abdulsamad din
Itama Babu tantama dama tasan yau komai dare saiya fito nemanta sbd dukkanin Susan amsar tambaya daddaya dake zukatansu kafin daurin auren gobe Dan kuwa amsoshin tambayar dake ran kowannensu itace future din yayansu da zaa daurawa aure gobe Dan haka a wahalce ta saci jiki ta fito bayan tasa Abdul yabar musu motarsa incase idan ciwonta zai tashi da dare su wuce asibiti ya samesu acan.
Batada lafiya sbd jininta yakai kololuwar hawa ko tsayuwa Bata iyawa sosai Amma bazata iya kwana ayauba batareda tayi magana da mahaifin Inayah ba,
Zuciyarta bugawa zatai da sake sake da fargaba harma da tashin hankali matuqar yau batai magana dashiba taji abinda takeson ji.
Da wani irin speed ya fizgi motarsa yabi ta gefen motarta ya wuce Yana Jin tsohon tabon baqin cikin daya dade Yana dannewa yana taso Masa.
Ribas tayi ta rufa Masa da gudu itama duk da qarfin haline kawai takeyi Dan sosai takejin kaman zuciyarta Zata fashe,
Tsohon famin baqin ciki da quncin da tarin Dana sanin gaske datake dannewa shekaru masu yawa ne suke birkito Mata tako Ina tanajin zuciyarta na azabar zafi da qunci.
Baisan tasan Lagos ba sosai Dan haka ya ringa ratsa manyan anguwannin dazai bacewa ganinta saidai sosai ta nace tana binsa idanuwanta ma tuni suka fara tsiyayar hawaye Dan kuwa hakan ya tabbatar Mata da tunaninta Gaskia ne akansa shine Wanda ta gudu tabarwa Jaririyarta AYSHATOUH.
A daidai gaban ma'aikatarsa ya faka motarsa tareda qin fitowa zuciyarsa na qara daukan wani irin zafi da bacin Rai da baqin ciki Mai zafin gaske.
Baya kaunar ganin fuskarta sbd ganin fuskarta na tunatar dashi kowace daqiqa na lokacinda ya rabu da gatansa da iyayensa harma da farin cikinsa akanta.
Jajir idanuwansa suka kada sosai sbd tsananin zafi da zuciyarsa ke dauka.
Bude motar tayi ya fito ya wuce zuwa ciki tabi bayansa da sauri itama hawayenta na tsananta gudu kaman yanda bugun zuciyarta da tashin hankalinta ke tsananta.
Cak suka tsaya a tsakiyar office dinsa koina tsit ba kowa sai securities din ma'aikatarsa.
Zubewa tayi agabansa tareda fashewa kawai da kuka Mai tsanani da taba zuciya sbd Batasan me Zata fara fadaba ko tambaya.
Kukanta sake zafafa ransa yakeyi Musamman wannan sautin kukan shine ta ringa Yi Masa a wancan lokacin batareda da duba girmewar datai masaba ta lalata rayuwar 'dan matashin dake tsakiyar karatunsa cikin kwanciyar hankali da kulawar iyaye.
Wani mummunan 'daci da qunci Mai nauyi ya hadiye ta wuyansa tareda juyowa ya kalleta da idanuwansa dasukai jajir Kai tsaye Yana danne fushinsa da nutsuwa yace"
Bansankiba ko wancan lokacin hakama bansakinba a yanzu,
Banda alaqa kowace iri dake bayan wadda zamu qulla a goben ta auren 'yayanmu Kuma itama zan bar 'danki ne kawai ya auri 'yata sbd farin cikinta dakuma kaucewa abinda zai sameta idan akai fashin auren Dan haka ki amsa mun tambaya daya rak itama sbd kaucewa Mummunan Al'amari.
Kuka takeyi sosai sbd tasan Babu abinda daga ita harshi sukewa tsoro kaman alaqar 'yayansu
Saidai kafin komai yabiyo baya na abinda ya faru a baya shine susan makomar alaqar dake Shirin qulluwa goben wadda tuna abinda zai biyo batama tashin hankali ne da wata babbar masifar.
Cikeda baqin ciki yakuma kallonta Jin batada niyar amsawa sai kukan datake Yi kaman zata shide.,
Zafi da quna ransa ke qarawa Dan haka ya juya yanajin kansa na sake yamutsewa da babban tashin hankalin da Inayah Zata iya Shiga akan wannan matar...
Yanada zafin zuciyan gaske Mai tsanani Amma tunda rayuwarsa ta sauya ya iya boyewa da dannewa Babu Mai gane yanayinsa duk kafiyarka Amma yau zafin zuciyan tasa ya gagara dannuwa a zafafe ya buga glass table din dake gefensa take ya tarwatse da qara Mai tsanani
Saida Hadizan ta firgita tana dagowa da jajayen idanuwanta dasuka rine take sbd tashin hankali Mai tsanani da kuka.
Miqewa tsaye tayi hawayenta har lokakacin basu tsayaba Dan ba tsayawar zasuyiba muryarta na rawa tace"
Ina AYSHATOUH???
Wani matsiyacin kallon baqin ciki da takaici yayi Mata yanajin duk duniya Babu Wanda yakai Hadiza sonkai
Ya dauke Kai Yana kokarin danne kansa daga zafin fushin dake taso Masa Kai tsaye yace"
Idan kece kika haifi Abdulsamad menene alaqarki da 'yar da kika Yar????
Gangaro Mata hawayen daci da danasani sukai muryarta a dashe tace"
'yatace nice na haifeta da ita da Abdulsamad duk nice na haifesu Kuma mahaifinsu daya idan Inayah itace AYSHATOUH to uwarsu daya ubansu daya da Abdulsamad.......""da kuka ta qarasa zancen Dan kuwa babbar masifa ta diro ta sameta a zazzafan tabon ciwon qunci..
Idan Abdul Mai samu Inayah ba haukacewa zaiyi"" innalillahi wainnan ilaihrrjiun
Na shiga uku Ni Hadiza rayuwata tasake shiga wata babbar jarabawar Mai nauyi...
Mutuwar tsayece ta samu AA MAJEED Dan kuwa yayi fargabar Jin hakan Amma Bai yarda da zaiji tabbatar hakan daga bakintaba.
Qarasa rikidewa idanuwansa sukai jajir yanajin wani gumin zafi da babban tashin hankali na shigarsa.
Abinda yakeson tabbatarwa kenan daga bakinta dan shakku da fargaban daya shigesa na iya yiyiwar hakan Kuma ta tabbatar Masa Dan haka baida sauran buqata da ganinta kona second daya Dan a Karo na biyu ta sake wargaza rayuwar 'yarsa.
Juyawa yayi Yanayinsa na ninkuwa ada sauti Mai 'dacin gaske yace"
Zaki iya komawa ki sanar da danki dagani har 'yata yanzu bamuda alaqa daku Auren anfasa.
Juyawa yayi zai fice Dan hankalinsa gabaki daya yagama yamutsewa qarshe kaman kansa zai buga
Inayah yakejin tashin hankalin yanda Zata karba kaddarar rashin auren Abdulsamad sbd bazai taba fada Mata dalilinba Dan kuwa bazai taba barin Hadiza ta kusantar Masa 'ya ba.
Da saurin Hadiza Tasha gabansa tana rokonsa cikeda tarin nadama tace"
Dan Allah kafadamun idan Inayah ce Ayshatouh na,
Har abada nasan bazan taba samun yafita a zuciyarkaba Amma Dan Allah kada ka hanani Ayshatouh Inayah,
Wlh nayi Dana sani nayi nadama.....
Sauraronta tafasashi sukeyi tako Ina Dan shi kansa komai ya kunce Masa a yanzu.
Wucewa yayi Yana daga wayarsa zuciyarsa a quntace ya saka kirana Mr Al-amen Yana dauka Kai tsaye yace"
Ai Mana booking tickets da komai na tafiya nida familyna gobe kafin 12 zamu bar qasar....
##MAMUH
##MARRIAGE/LOVE
##AYSHATOUH INAYAH AA MAJEED
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/26, 1:50 PM] +234 703 262 0576: *_28_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tashin hankali Hadiza tashiga Jin abinda ya fada a firgice Tasha gabansa tana rokonsa cikin mummunan hali na kuka tana rokon ya hadata da 'yarta Ayshatouh Inayah.
Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiyar zuciya Mai dumi kafin ya Dan dago ya kalleta kadan cikin nutsuwa kaman Wanda zuciyarsa ba tsananin quna takeba da 'daci takeba yace"
Babban taimakon da zakiyiwa kanki da Abdulsamad shine ki cirewa ranki da kanki tunanin sanin mahaifin Inayah bare ita Inayah din,
Inayah 'yatace Kuma Babu Wanda zaizo Rana tsaka yacemun shine ya haifeta,
Bansankiba Baku nada alaqan komai dake..
Ki nema yarki a Inda kikasan son zuciya yasa kin barta.
Zafi maganganunsa suka farai Mata sbd duk yanda tayi aikin son zuciya abaya Inayah dai yartace Kuma tayi danasani daga ranar data gudu ta barta.
Wlh bazata yardaba taga yarta sannan ya dauketa su bar qasar tasan bazata Kuma ganintaba har abada Dan haka cikin rashin tunani da tauna zancen abinda yafada matan tace"
Har abada saidai ka Kira kanka matsayin mariqinta uban daya raineta Amma bazaka taba sauyata daga nice wadda na dauka cikintaba na haifeta.
Bai tsaya saurarentaba ya fito Kai tsaye yashiga motarsa Yana cewa security a rufe Masa koina.
Cikin zafi ga figi motarsa da matsiyacin speed yabar gurin batareda yajira ganin fitowartaba.