← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 65

Sashe 12

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran Dr ne yashigo wayarta da sauri sauri ta dauka tace Masa"

I'm kinda busy
I will call you.

Aje wayar tayi tareda nufar gaban madubi ta shafa Neutrogena oil dinta ta fesa spray kawai ta koma gurin kayanta ta saka wata chiffon wide neck gown Mara nauyi ta ziro slippers ta fito ko wayarta Bata daukoba.

Kai tsaye hanyar palon Abbi ta nufa tana tunanin yanda ya shammaceta Saida yadawo ya fada Mata da ba lallai ta jima gurin aikinba ayau.

Da farin ciki bayyane kan kyakkyawar fuskarta tayi knocking kofar harso biyu kafin taji muryarsa daga ciki a natse ya furta"

Yes Inayah,
You can cm in.

Shigowa tayi da sallamar dake bayyanarda farin cikinta na ganinsa ta qaraso har gefensa ta zauna tana cewa"

Abbi kana tunawa danima kuwa?
You look more than cool and calm.

Wani qayataccen murmushi Mara sauti ya sake Yana kallon yanda itama tayi Yar rama ta yanayin aikin data samu kanta aciki da cikakkiyar kulawa yace"

Dr INAYAH A MAJEED ko gaisuwa babu tukuna kafin complains su biyo baya.

Cikin murnarta tace'

Abbinah barka da dawowa
Munyi kewarka
Kagani har Rama nayi sbd ban saba dadewa hakaba bakanan,
Ga stress na aiki.

Yar dariya kadan yayi Yana cewa"

Duk kokarin Dr Abdul akanki menene da stress acikin aikin?

Dr Abdul yana fadamun irin kokarin da kike keep it up okay.
Tun yanzu Ina alfahari da 'yata Zata Zama babbar likita wata ran.

Taji dadin kalmomin nasa Dan babu abinda yafi komai faranta ranta kaman ta faranta ran mahaifinta harya bayyanarda hakan.

Firar familyn CM tafarai Masa tana sanar dashi irin kulawa da kaunar dasuke Mata harma da umma yaganah.

Sosai yaji dadin hakan Kuma a gaban nata yakira Cm yayi Masa godia a gajarce na yanda iyalansa suka karbi nasa iyalin da hannu babbiyu.

Daganan firar Dr Abdul suka koma wadda kusan duk Rabin firar itace taketa fadar halayen Dr Abdul din dakuma yanda take kulawa da tattalinta.

Abbinta saurarenta kawai yakeyi Yana nazarin irin shaquwar data samu da Dr Abdul din lokaci daya,

Yana fatan alaqar da tsaya iya ta aiki sbd irin wannan yabo da Inayah ke Masa baya fatan tasake shiga wata soyayyar yanzu Musamman ko Dan yanayin weak heart nata
Duk da wani bangaren Dr Abdulsamad ya kwanta Masa sosai a Rai.

Sai dare tabaro gurin Abbin Dan abincima acan palonsa sukaci tare sbd shi kansa yariga yashige ne bazai fitoba sai gobe shiyasa shima Bai fito main hall ba cin abincin dare.

Tana baro palon Abbin gurin umma taje sukai Saida safe ta wuce daki ta kwanta bayan tayi waya sama sama da Dr Abdul akan daga gobe a
Shift din dare zasu sake komawa.

Washe gari da safe batada zuwa asibiti Dan haka baccin safe tayi sosai sai 11 ta fito lokacin Abbi baya gida ya fita.

Sanye da Riga da skirt na atampa ta fito tana waya da Neesah.

Breakfast tayi ita kadai sbd tasan ko umma ta jima da yin nata.

Tana gamawa ta nufi dakin umma yaganah acan tayi kwanciyarta tana chatting sama sama saiga su Mimi sun taho gidan dukkaninsu yiwa Abbi barka da zuwa aikuwa take gida ya kaure da hayaniya.

Mimi harda tsarabar wasu kayan atampopin tayiwa Inayah aikuwa umma ta gode Mata sosai itama Inayah din tanajin dadin kayan Dan haka ta gode mata.

Dakinta suka koma itada Safnah suna firarsu ta matasan 'yan mata,

Fira suke akan anty Hafsat da Bata isoba sun biya sun ajeta gidan yayar mijin qanwarta dasuke tsananin mutunci sosai, daga can zaa kawota Nan din.

Saida suka gama cin abincin Rana kusan karfe biyu da mintuna kafin Anty Hafsat ta iso gidan.

Da farin cikin ganin siyama Inayah tarbota tun daga harabar gidan.

Faruk Ismail shine Wanda yakawo anth Hafsat daga gidansu.

Kallo daya yayiwa Inayah yaji Tai Masa sbd shima tunda yayo karatu a Malaysia yadawo yakasa ganin macen datai Masa gashi dama iyeyensa sun takurasa akan aure.

Ganin dayayiwa Inayah da yanayin gidan nasu yasa Kai tsaye ya 'dan fahimci wayayyu ne jama'ar gidan,
Da alama sun danyi nasu yawon bude Ido wata qasar.

Inayah gabaki daya batama wani lura dashiba sbd hankalinta dake anty Hafsat da Siyama tana murmushi dukkanin kyanta na Kuma bayyana.

Anty Hafsat ce ta juyo ta kallesa tana cewa"

Ok faruk nagode sosai
Ka Isa gida lafiya.

Gyada Kai kawai yayi tareda tada motarsa yabar harabar gidan ya fice Yana ayyanawa aransa shikam yaga matar aure irin class dinsa dayakeso.

Inayah kam Anata bangaren ko kula batai dashiba Dan a daukarta driver nema yakawo antyn.

A gidan suka wuni Anata fira da hayaniya sai yamma da Abbin yadawo aka kaisu palonsa suka gaisa a matuqar mutunce da girmamawa.

Sai dare suka tafi bayan Abbi yayi musu kyautar kudi na Musamman ga Yara.

Inayah Jin tayi kaman kada su tafi sbd yanzu da qarfi da yaji tafara sabo da rayuwar hayaniya Dan duk Wanda zai Yi rayuwa a Lagos dolensa ya koya daukan hayaniya duk da sukam anguwarsu batada abinda ya hadata da hayaniyar ko hayaniyar ma Kai securities basa Bari magana suke maka sbd gudun shiga haqqin wasu.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/14, 11:35 AM] +234 703 262 0576: *_Mamuhgee 11_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Washe gari ba wani dogon walwala ta tashi
Saima guraren 9 ta tashi Dan tun asuba tayi sallarta,

Zare dukkanin kayanta tayi ta jefa kan kujera ta wuce toilet tashige tana kokarin daura towel jikinta.

Sosai ta jima tana wankan sbd tasaba Bata lokaci gurin kyalekyalen wankan,

Sai bayan mintuna ta fito daure da milk towel kanta Kuma nade da wani towel din mara girma.

Natsatsen Qamshin shower gel dinta na AESOP Mai sanyin Dadi ne ke tashi ajikinta ta kalla Inda qaramin bedside agogonta yake ta kalli time taga goma yakusa Dan haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror tagara shiryawa.

Moisturizer kadan ta shafa na LA PRAIRIE sai oil na Neutrogena da kome Zata shafa saita shafasa takejin skin dinta daidai.

Dama kafin ta fito daga wanka zubbi tagama gyara mata dakin ta kunna humidifier dasu fresheners masu sanyin qamshi ta fice da kayan data cire zuwa laundry.

Elira kaftan dress ta saka dark brown da scarf sai Cassandra wedge sandal ta fito gabaki daya qamshinta na JO MALONE sea salt yana gauraya iskar hanyar datake biyowa.

Kai tsaye dakin umma yaganah ta nufa tasan lokacin umman bacci takeyi sbd a qaidarta haryanzu data fara tsufa Bata daina saka hannu akan aikin abincin A MAJEED matuqar yana gari tariga ta saba
Matuqar baka ganta kitchen ba A MAJEED baya gari Dan hakan Bata komawa bacci bayan asuba saita tabbatarda abincin breakfast yagama kammaluwa a dining saita koma ta kwanta sai 12 take tashi tayi wanka ta Kuma leqawa kitchen din sakawa zubbi hannu a abincin ranar.

Kaman yanda tasani bacci umman keyi Dan hakan fitowa tayi dakin Kai tsaye ta nufi hanyar dakin cin abincinsu tana shiga abbin na shigowa ta dago ta kallesa da fararen idanuwanta dasukaji tsadaddiyar fenty beauty mascara da eyeliner

Qamshinsa daya doke nata ta shaqa tareda dakatawa daga zaunawan da zatai cikin nutsuwa da girmamawa tareda tsananin kauna irin ta 'da da mahaifi tace"

Good morning Abbi,
Barka da fitowa.

Saida ya kalleta cikin nutsuwa ya ja kujera ahankali ya zauna yana sake kallonta ganin yanayinta na sanyi jiki har lokacin
Basarwa yayi sbd karta samu damar fara Masa hawaye agurin yace"

Morning,
Kin tashi lfy?
Ya umma yaganah?
Tana bacci ne?

Zama tayi tana cewa"

Eh Takoma bacci.

Itace ta zuba Masa breakfast din kafin tazuba nata Takoma ta zauna tafara ci.

A natse yakecin brown past din da aka hada da soyayyan dankali da hanta sbd Sarai umma yagana tasan Baya wani cin kayan fulawa sosai yafison abinci Mai suna abinci bawai wani jagwalgwalon gayuba.

Satar kallonsa Inayah keyi tanason magana akan roqonsa maganarsu ta jiyan amma tana shakkar hukunci ko dokar ta qara tsanani akan iya ta jiyan.

Kasa daurewa tayi ta aje fork din hannunta tareda dagowa ta kallesa a marairaice tace"

Abbi....

Tissue ya dauka tareda goge bakinsa kafin ya dago ya kalleta da dukkanin fararen idanuwanta ya zuba mata yana jiran abinda takeso fada.

Ganin yanda ya zuba mata idanuwansa yasata sauke Kai tana qaqalo hawaye cikin idanuwanta ta dago ta kallesa hawayen na gangarowa kan kumatunta tace"

Abbi Dan Allah kayi hkr bazan sake tsallake zuwa school ba I promise
Amma Dan Allah kada ka hanani fita ko zuwa wani gurin.

Hawayenta dake gangarowa ya kalla tareda Dan sake wani gajeran murmushi dayayi Masa zuwan bazata sbd ganin qarfi da yaji wai 'yarsa daya Rena da hannunsa keson yimasa dabara,

Duka duka Inayah nawa take?
Yaushe tayi girman da wayon datake ganin Zata iya Masa wani sisina da hawayenta tunda tasan bayaso..

Ita Bata tashi da mahaifiyaba bare ace takoya ko tagani agurinta Amma wai hartasan taringa Masa hawayen kirsa Dan yaringa barinta tana yanda takeso.

Sake fadada murmushinsa yayi kadan yana Kuma kallon hawayen nata datake tsiyaya da gaske Wanda badan yagama saninsu a yanzuba da tuni zuciyarsa zatayi 'daci da ganinsu Amma yanzu mamaki yake sosai ta yanda take iya hakan.

Numfashi ya sauke ahankali tareda zaran tissue dake kan dining din ya miqa mata yana cewa"

Ya Isa idan kingama tashi muje nine zan aje school din yau kafin na wuce office.

Share hawayen tayi da tissue din daya Bata tana jin Dadi cikin ranta na yanda kwata kwata Abbinta baya juran hawayenta.

Miqewa tayi tabiyo bayansa tareda daukan LV hanbag dinta tafito tana duba wayarta dake ringing da sunan Zaid akai.

Bata wani dauki wayarba ta jefa jaka sbd tanason samu ta lallaba abbinta yabarta taringa zuwa duk Inda ta saba zuwanta itadai tanaso gskia.

Cikin black BMW 7 series suka fita shine da kansa yake tuqa motar tana gaba zaune,
gabaki daya Qamshin tsadaddun turarukansu yagama sauya numfashin motar Amma dayake motar tasace shine Wanda yafi shigarta sai nasa ya take natan sbd tuni akwai qamshinsa acikin motar.
Chapter 12 · 0% Book details