← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 65

Sashe 15

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya rasa waye yake gurbata Masa tunani da tarbiyar 'ya akan ire iren hakan,

Kwata kwata haryanzu bayajin sha'awar kowace irin mace bare marmarin ajiyeta shiyasa yake tsananin mamakin yanda Inayah ta qwallafa Rai a soyayya da son aure tunda ba ganin tayiba a gidansu ana soyayyar, hasalima shi soyayyarce sam baisan yama akeyintaba bare harka Gama macewa akan wani kaje kana Hana kanka bacci a wofi.

Motar Abbin na barin makarantar ta fito zuwa coffee shop din dake makarantar ta samu Neesah dake can ta zauna tareda fidda wayarta batareda ta iya wata doguwar maganar da Neesarba tafara saka Kiran zaid.

Kasa samunsa tayi dole qarshe tabar Masa sakon murya da cewa idan ya kunna waya yakirata Kuma ya tabbata Dad baije gurin Abbinta ba sbd zasu iya yiwa kansa Abbin ya dakatar da soyayyarsu sai gaba din.

Bayan Gama tura Masa sakon muryan aje wayar tayi gabanta zuciyarta ba wani Dadi ta Dan yamutsa fuska tareda Kiran sunan waiter a tushe tace"

2 Cappuccino's please.

Kallonta Neesah tayi tana cewa"

Kodai zamu samesa ne?

Bazai tsaya sauraren wannan ba namafi zatan Dad din nasa ya riga Abbi Isa office dinsa jiransa.

Kasa cewa komai tayi Saida aka kawo Mata cappuccino din ta fara Sha ahankali kafin tace"

Banajin komai sai bacin ran mahaifina,
Zuwan dadyn Zaid zai fusata Abbi Kuma na fadawa Zaid kada yaje Amma Yana banza da zancen yakuma Dan akan Abbina bana daukan wannan so gwarama ya daina wannan saurin.

Bari naji Inda yake saimu samesa" cewar Neesah tana fidda wayarta daga qaramar Louis Vuitton handbag dinta.

Kinason Abbi ya daina kulani kwata kwata yayi fushi danine?
Kinsan halinda mahaifina zai shiga kuwa idan yaji naje gidan namiji
Gskia bazan iyaba,
Bari anjima idan Bai kiraba na sake kiransa.

Maida wayar Neesah tayi tana cewa"

Amma dai bafa lallai yazoba Sai sungama magana da Abbin hakan Kuma shine qarshen Bata komai.

A qasan maqoshi ta furta"

Allah ma yasa Abbi ya gaji da wannan zaryan ya amince musu ayi auren yanzu sbd Gaskia Ina son Zaid dina sosai,I can't live without him, duk wannan fadan danake na qarfin haline Ina tsananin sonsa gaskia.

********
_AAM's BUILDINGs_

Zaune Yake kan sofa dake makeken office dinsa hankali kwance ya jingina bayansa kadan yana sauraren Former Ambi Mukhtar Asheer mahaifin Zaid.

Gabaki daya idanuwansa dake Dan rikata wanda duk ya zubawa sbd kwarjini su ya zubawa Ambi din Yana kallonsa Yana saurare.

Da gaskiyarsa ta hakika yake sake tsaro jawabansa Dan shawo kan A MAJEED din ya amince da auren 'yayan nasu a yanzu sbd kaucewa barna tunda yaran sun matsa sunason ayi.
Amma abinda Bai saniba gameda A MAJEED shine wannan zuba Masa idon da yayi baida niyar daukan zancen ne.

Qaramin numfashi ya sauke a natse kafin ya Dan dauke kallonsa daga Ambin ya dauki wayarsa dake gefensa ya ajiye gabansa cikin nutsuwa yakuma nagowa ya kallesa yace"

Kaman yanda nafada last time dakuma farkon zuwanku neman auren maganar dai tana Nan a hakan,

Hakuri zaa cigaba dayi inshallah babu wani abinda zai faru ko biyowa Baya dangane da wata barna ko makamancin hakan...

Inayah dai tunda nace nabawa Zaid aurenta bazan fasaba kokuma sauyawa matuqar ba itace tace ta fasa Dinba kokuma wani dalilin dazai iya hanawar Kuma ba'a fatan hakan,

Dan haka Ambi Ina sake baka hakuri kuci gaba da hakuri inshallah lokacin ya kusa sbd tana gab da kammala karatun tunda duka duka shekara dayane ya rage Mata inshallah...

Amma tunda Kai kana hango wata barna da Zata iya biyo bayan rashin auren da wuri
To inaga na dakatarda haduwarsu kawai su tsaya iya waya zuwa sbd kiyayewa sai a sanarda shi Zaid din
Inayah Kuma zan fada Mata
Daga yanzu haduwarsu iya wayane ya dakata da zuwa gurinta for now,

Allah yayi Mana jagora duka.

Sake da Baki Ambi yake kallon A MAJEED din Yana sauraron bayanansa dake fitowa suna zuwa Kai tsaye,
Yasani yakuma ji wainda suka San A MAJEED din suna fadar Kai tsaye yake magana Baya wani kwana kwana ko lanqwasa Musamman zancen daya shafa 'yarsa dayake ganin baida abinda yafita.

Jin shiru yasa Ambi ya rufe bakinsa tareda sauke numfashi Yana yaqen dole yace"

Shikenan ba komai zamu cigaba da jiran tunda Shima akwai nasa programs din dazai kammala zuwa next year din
sai abin yazo musu duk a natse ma,
Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi.

Amin" ya furta Yana kallon ruwa da aka kawowa Ambi din Bai Sha ba yace"

Me zaa kawo maka?
Any drink, coffee or something?

No,no,no I don't think i need anything
Thank you,
Ruwan ma is okay.

Daukan ruwan yayi yasha kadan tareda ajiyewa suka Dan fada wata firar daban wadda Bata shafi iyalansuba ta business industries ahakan har ya Dan ja lokaci sosai sai lokacin tashinsa suka fito tare ya maidasa har masaukinsa kafin ya wuce gida da driver dinsa.

Da daddare zaid yazo masaukin dadynsa Dan jin yanda aka Kai qarshe Dan Shikam ma wlh yanzu yafara gundura da qaidan abbin Inayah

Lokacinda dadyn Zaid ke yiwa Zaid bayanin komai Shima sai alokacin yake bayyana zallar bacin ransa da yanda A MAJEED din yaketa ja musu Rai akan 'yarsa saikace itace 'yar datafi kowa gata a duniya,
Saikace shine kadai Mai arzikin dayake da 'ya.

Cikin damuwa Zaid yace"

Dad inason Inayah sosai Amma gskia bazan iya wannan hakurin ba,
Is either ta dagawa babanta hankali akaina kokuma na barta sai ranarda Abbin nata ya tashi aurar da ita Amma gskia zan nema wata yanzu.

Cikin takaici dadynsa yake kallon bakinsa dake magana yace"

Bakada hankali ko?
Kasan me ake nufi da auren connection kuwa?
Duk da connecting naku akaiba kune kuka hadu da juna da kanku Amma wannan auren shine yanzu kowa keson ace 'yayansa sunyi wato auren arziki da samun connections.

Duk tarin arzikinsa da uban dukiyar daya tara 'yarsa 'daya,
Hakama Bayada Mata bare asaka ran zai Kuma haihuwar wasu 'yayan,
Duka wannan arzikin da dukiyar 'yarsa yake tarawa Dan haka duk Wanda zai aureta shine Mai babban rabo tunda 'yar tasa mace ce wani abun dole saidai mijinta,

Ahakan kake maganar ka nema wata ka bar Inayah din?

Ka kuwa San waye A MAJEED da abin daya mallaka?
Ka kuwa San tarin arzikin dayakedasu a Nigeria ma kawai?

To idan kanka ya daina lissafi Bari na maka budaddiyar wasika,
Idan ka rabu da Inayah wlh ka tabbatada wadda zaka kawo mahaifinta yafi A MAJEED Jan wuya,

Dama ba sonta kakeba dakaketa ikirarin bazaka iya rayuwa babu ta ba,zaka mutu idan baka sametaba,
Nonsense,
Uban me kakesha da duk kabi ka dagawa mutane hankali akan son auren yanzu?
Duk ma abinda kake biyewa su Sufian suna baka kanasha da kabi duk da rikice da Neman mace gwara ka daina Sha sbd Ni Future dinka tsayayya nake hango maka,

Duk tarin nawa arzikin danakeda kaima kakesa nafison ka hada Dana uban matarka koina yazama kanada connections dinsa da tarin arziki
So idan ma ki fita hankalinka better cm back to your damn senses
Neman Mata ko buqatan mace bashine naka ba yanzu.

Duk abinda dad din yafada Masa yasan hakan ne Amma dai gaskia shi yanzu mace yake buqata matuqa,

Kuma kaman dai yanda dad yafada akan abinda yake ikirari kan son dayakewa Inayah gaskia ne
haryanzu tsananin son Inayah na Nan daram a ransa saidai Shima tasa buqatar Gaskia ce Kuma tabbas wasu abubuwan sukesha taredasu Sufian.

Dan haka zai sama Inayah suyi magana dole ita kadaice Zata iya saka Abbinta yabarsu suyi aure yanzu.

Koda yakoma gida Bai kirata ranarba sai washe gari da safe.

Tana ganin kiransa lokacin tana taredasu Abbi da umma kan dining Dan haka tsulum ta miqe tareda cewa ta koshi tabar dining din.

Umma ce kawai tabi bayanta da kallo Shikuwa abincinsa yake cigaba daci hankali kwance bawai Kuma Dan Bai fahimta komaiba.

Fada sosai tayi Masa a wayar Shima farko fadan yayi Mata kafin ya sauko Yana rarrashinta.

Kashe wayarta tayi itama tareda jefarwa tana cewa"

Saina Rama Nima kaji yanda naji.

Bai sake kiraba kaman ita yanda tayita yi daya kashe Mata wayar

Sai abin yamata ciwo itama ta sharesa badan tasoba.

Sanin Inayah nayi Masa tsananin so yasa ya daga mata hankali kwana biyu da rashin Kira kafin Kuma daga baya qarshe Bai Ankara ba yafara mata yar barazanar auren wata kafin tagama nata karatun saiyayi ta biyu da ita.
#MAMUH#
#RIBA BIYU/MARRIAGE
#A MAJEED/AYSHATOUH INAYAH/LOVE/ROMANCE

*_FOR MORE PAGES KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOKS@Mamuhgee_*

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS  4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/15, 10:27 AM] +234 903 125 2820: *_14_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Farko Inayah tayi mamaki sosai da maganganun Zaid din sbd Bata dauka Yana fada da gaske bane kawai dai yanason daga Mata hankaline sai kawai Bata dauki zancen da wani mahimmanciba tadaiyi mamakin Inda yasamu guts na iya fada Mata hakan.

Shima Zaid din ganin ta watsar da maganar yasan Bata dauka maganan bane Dan haka ya tattara Shima ya watsar Yafara Dan kula tsohuwar budurwarsa data maqale tanason su dawo tare dama friend din Sufian ce.

Tunda dad din yazo yasamu Abbi sukai magana da yanda sukai da me ake ciki babu abinda Abbi ya sanar masu daga ita har umma yaganah,

Maganar dakatar da zuwan Zaid ma shine da kansa ya kirasa ya sanar Masa Dan haka Inayah Bata saniba Shikuwa Zaid din tuni hakan yasa ya sake watsar da zancen Inayah yanzu yakama Amal suka bude shafin soyayya duk da ba wani jinta yakeba Inayah ce kawai a ransa har koda yaushe.

Illar Abokai masu aikita barna Dana Amal yasa tuni yafara samun cikakkiyar nutsuwar samun mace atareda Amal dan haka yanzu yasamu nutsuwa sosai hankali kwance yake jin dadinsa da Amal.
Chapter 15 · 0% Book details