← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 65

Sashe 17

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/15, 10:27 AM] +234 903 125 2820: *_15_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Cikin damuwa umma yaganah tace"

Ga irinta Nan ai Nima Dana biyewa roqonku aka biyo din Kuma wlh sbd MAJEED yasan zaku biyo din yasa yace nice zan maida Neesan gida gashi nawa zuwanma baiyi amfanin abinda yaso yayi ba,

Yanzu Ina amfanin wannan mugun ji da mugun ganin ana zaune kalau buki saura kwanaki,
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.

ACn motar suka qara umma na Kiran sunan Inayah cikin Dan sauti Mai tashi tace"

Karki saka wannan aranki kijawa mahaifinki Inayah tunda zuwan qaddarane koma yayane,

Kuma dai Ni nakasa yarda da abinda kuke cewan kungani,Zaid dinne Kuma yake Neman Mata?
Kun kuwa tabbata?
Idan har bawai kamasu kukayi tirmi da tabaryaba karku zartar da hukunci sbd ana maganar Zina ne anan fa....

Cikin wani irin tsananin fushi da kukan gaske da tunda take arayuwarta Bata taba yinsaba sai yau akan wani namiji
Tace"

Umma yaganah kiyi shiru kawai sbd bakisan abinda idanuwana suka ganiba,
Wallahi tallahi tare yake da wannan dai dana gansu ayau nasan tare suke akwai abinda suke aikatawa,
Hannunsa fa acikin rigarta Yana matsa nonuwarta Kuma......

A kidime umman ta katseta da cewa"

Innalillahi Inayah banason ji daina fada,
Kuma karma nakuma Jin wannan zancen banzan,
kema daina fadan wannan maganar a bakinki batada dadin ji kadama koda tsautsayi mubari MAJEED yasan mun biya gidansa da wannan mugun labarin.

Da zallar mamaki Neesah ke kallonta tace"

Umma yaganah idan Abbi baijiba shiru zaayi Inayah ta aura mazinaci?

Kinga Neesah ku Yara ne,
Wannan bawai maganace da Kai tsaye zaa fito afada cewa zaid ga abinda yakeyiba sbd akwai maganar manya ta aure acikin lamarin Dan haka komai a sannu zaa bisa,
Kuma idan ance arusa auren atake sbd haka shi Wanda Zata samu agaba ansan nasa boyayyan halin?

Da yawa akwai mazinata a mazan aure Amma baka taba sani,
Itama Dan Allah yayi Zata sanine kafin Auren,
Idan anzauna an duba komai a tsare zaa iya samun mafitar komai a natse.,
Muje na rakaki ciki na gaisa da haj Salma da dadynki idan Yana gidan nazo mu wuce kafin qawarki ta some Mana anan asirinmu yagama tonuwa.

Daqyar Inayah ta iya danne halinda take ciki suka shiga su dukansu aka ringa Murna da musu sannu da zuwa.

Momyn Neesah murnar ganinsu takeyi sosai itada qanwarta dadyn Neesah din musamman ganin dattijuwa umma yaganah da kanta a gidan Dan kallon mahaifiyar MAJEED suke Mata.

Angama gaishe gaishe da firar dawowarsu lafiya dama firar bikin Inayah dake gabansu Kuma yanzu,

Sai kame kame umman da Neesah keyi sbd kowannensu har lokacin cikin shock din abinda yafaru suke da Inayah dasuketa Allah Allah agama atafi gida kafin ta ringa rusa musu kuka agurin Dan Zata iya gashi Allah yasa tasamu jarumtar dannewa din kada su momy sugane.

Basu wani jimaba suka fito sbd cewar datayi kanta na ciwo su koma gida.

Har mota dukkaninsu suka rakosu har momy.

Shahada kawai umma yaganah tayi tabari Inayah taja motar suka nufo hanyar gida.

Suna fitowa gidansu Neesah hawayen datake riqewa suka fara gangaro Mata zuciyarta na wani irin tafasa.

Tunda take rayuwarta Bata taba Jin 'daci da qunci ba irin yau din,

Dukkanin rayuwarta quncinta biyu ne zuwa uku,
'Bacin ran mahaifinta,
Rashin uwa,
Saikuma 'yar damuwar yau da gobe da bazaa rasaba Amma ita ko zafin rashi da talauci Bata saniba tunda koda mahaifinta yayi talauci da gwagwarmayar rayuwa batada wayo Tana qarama Kuma ko a wancan lokacin baitaba barinta ta nema Abu ta rasaba.

Sbd tana tuqi yasa umma yaganah batai Mata maganaba Dan tasan tana buqatan kukan ko zataji sassauci shiyasa taja bakinta tayi shiru tana kallo Inayan na wani irin gudu dasu.

Zuciyan Inayah wani 'daci da zafi take Mata Mai tsanani,
Tayaya Zaid har zai iya taba jikin wata macen ba itaba?
Tayaya zaid zai iya hakan?

Tsigar jikintane yafara tashi sbd tsananin qyanqyami da baqin cikin abin,

Meyasa bazai kasa hakurin sauran kwanakin daya rage aurensuba zaije ya iya hada jiki da wata,
Harma ya iya hada shimfida da ita,

Kuka sosai takeyi har suka Isa gidan,

Parking din motar ma a juye tayisa ta fito tayi ciki da gudu tana share hawayenta Dan batasaniba ko Abbinta na gida.

Dakinta ta nufa ta zauna kan sofa tana kokarin tsaida hawayenta da hannuwanta dake tawa.,

Umma yaganah ce tashigo dakin tareda rufe kofar jikinta a mace ta qaraso gurin Inayan ta zauna gefenta tareda diban tissue dake gaban mirror tafara sharewa Inayah hawayen cikin tsananin kulawa da nutsuwa Dan Inayah ta fahimta abinda Zata fada Mata din,

"Inayah karki daga hankalinki kishiga tashin hankali akan wannan mugun tsautsayin,
Kinga na farko mahaifinki shine babban fargabar yasan kinje gidan saurayi,
Na biyu nima nasan ba qaramin qona ransa zanyiba idan yaji na biye Miki nabada damar zuwan gidan nasa,

Hakama Kinga abinda kika gani bawai kinada tabbacin ya aikata wani mummunan abin bane duk da ba mutunci ko kamun kan dazaisa yakai mace gidansa harma ki samesu a ayanda Bai kamataba,
Dan hakan kiyi hkr karki daga hankalinki da kaina Nima zan fadawa Abbinki idan har ta tabbata Zaid din yagama 'bata rayuwarsa da neme nemen matan banza,
Sbd yanzu MAJEED najin wannan zancen kinsan kome zai faru bazai basu aurenba kuma so gwara afara tabbatarwa Kuma ko an tabbatar akwai tsautsayi akwai qaddara kilan sune suka ritsa dashi kawai bawai halinsa bane,
Kinga idan yayi alqawarin gyarawa ai shikenan ba komai bane sai muyita adduar Allah yasa ya gane din ya daina.

Kasa magana tayi sai kuka datake faman rusawa umman tana share Mata hawaye.

Daqyar umma yaganah ta rarrasheta sukabar maganar akan Abbinta bazaijiba tukuna sai sun tabbarda abin bamai gyaruwa bane Dan kuwa Inayah tayi rantsuwar bazata auresaba matuqar tagane takuma tabbatarda Neman matan yake da gaske Kuma Yana kwanciya dasu sbd ta wani fannin ta gado halin mahaifinta sosai da sosai gurin tsananin qyanqyamin gaske shiyasa take ganin bazata iya hada miji da wata macenba.

Kashe wayarta tayi sbd yanda Zaid din keta faman Kira Kuma batajin Zata iya daga wayarsa shiyasa ta kashe duk da Bata kashe wayarta duk tsanani sbd Abbinta kada yakira yaji kashe Sam ya hanata kashe waya bayan shi Yana shigowa gida yake kashe wayoyinsa sai Kuma idan zai fita kokuma ya saka silent sbd rashin son damuwa.

Da daddare cikin qarfin hali umma yaganah ta sakata fitowa cin abinci suka Dan ringa kamewa sbd kada Abbin yagane.

Kallo daya yayiwa Inayah lokacinda take qarasowa gurin cin abincin sanye cikin Riga da wandon Prada farare masu kauri sosai kaman na sanyi da qaramar hula gabaki daya saita fito kaman qaramar baby.

Yanayin shigarta da fuskarta datake fresh ba komai da alama wanka tayi Kuma Bata shafa komaiba sai turarenta da qamshinsa ke tashi ahankali.

Shine yafi kowa sanin Inayah sbd shine mahaifinta Dan haka fuskarta da yanayin shigarta ya bayyanar Masa da 'yarsa na cikin damuwa...

Sake kallon yanayinta yayi yanda take cin abinci jikinta amatuqar sanyaye bakuma wai Dan tana jin yunwa ko dadin abincin ba,
Cusawa kawai takeyi.

Gun umma yaganah ya 'dan maida kallonsa yaga yanda ita Kuma take Dan hada kokarin share guminta akai akai duk da tsananin sanyin Aircon da babu Inda babusa a cikin gidan...

Maida kallonsa yayi a natse kan Inayah da hankalinta Baya kan kowa saina abincin datake ci Shima bawai hankalinta na kan abincin bane.

Jin yayi kwata kwata abincin dayake gabansa fita ransa sbd yasan akwai abinda suke boye Masa Dan daga umma yaganah har Inayar babu Wanda Bai San halayensa ciki da wajeba,hakama kallo daya yake musu kowannensu ya gane halinda suke ciki sbd Sam Baya Wasa da kulawa dakuma tarbiyar gidansa Wanda umma yaganah ta jima da Zama cikin ahalinsa Dan haka itama duk da tana matsayin uwa shine Mai lurarda ita lokuta da dama.

Ruwan sanyi da aka Dan zubawa lemon ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha tareda ajiyewa ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar dining din.

Daga umma yaganah har Inayah babu Wanda yayi Magana daya miqe din sbd hankalinsu Baya Kai Kuma hakan yasake tabbatar Masa da zarginsa akansu na akwai abinda suke boyewa basason ya sanin Dan Bai taba miqewa daga dining batareda dayansu ya ringa maimaita Masa ko ya qoshi da abincinba Dan sun San rashin zamansa yasa Baya wani samun damar cin abinci yanda ya kamata shiyasa daya miqe zasu fara tambayar ya koshi kokuwa ya zauna yaqara ci.

Yana barin dining din Umma yaganah ta kalli Inayah cikin qosawa tace"

Inayah kinason sakawa Abbinki tunanin akwai wata matsalar ne?

Ba nace Miki da kaina zan sanar Masa ba idan aka bada lokaci akasan Gaskiar lamarin¿

Kallon umman tayi tana jin damuwa sosai,
Ita sbd batada uwa batama San uwartaba shiyasa Abbinta takejin idan Abu ya sameta Bata sanar masaba kaman zuciyarta Zata buga.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa"

Abbi fa kinsani kwana biyu cikakki bazamuyiba muna wannan boyon zai gano mu.

"Nasani shiyasa nakeson kiyi kokarin cire damuwar komai aranki.

Bata iya cewa komaiba ta miqe tana daukan tissue tace"

Zan kwanta da wuri umma,
Goodnight.

Daqyar ta iya tattara kanta ta nutsu yanda Abbinta bazai gano kamaiba ta qarasa palonsa cikin sanyi da shagwaba ta nuna Masa bacci takeji Zata kwanta da wuri tai Masa goodnight Shima ta fice.

Bai bi bayanta da kalloba sbd Baya buqatan qari fahimta yasan for sure akwai wani abu,

Idan irin hakan tafaru bayace musu komai sharesu yake sbd cikin kwana biyu yasan zai Gama sanin meke faruwa.

Tana barin palon Abbi taji idanuwanta na cikowa da hawayen rashin sanar dashi damuwarta sbd Abbinta shine maganin kowacce damuwarta Wanda Allah ne ya tsaya musu duka akan hakan.
#MAMUH#
#LOVE#
#MARRIAGE

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902
Chapter 17 · 0% Book details