← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 65

Sashe 46

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inayah itace tazamo sanyin idanuwansa Kuma qarfin gwiwarsa sbd duka gwagwarmaya dayayi a halin dasuka samu kansu yayisune sbd inganta rayuwarta,

Yayi alqawarin ingata tasa rayuwar da tatane sbd su rayu kaman kowane 'yaya marayu sbd daga shi har ita marayin Allah ne.

**********
Hadiza bayan barinta gidansu majeed hanya tabi tana Jin kanta na juyawa sosai ga uwa uba tafiyar datakeyi kaman Mai koyan tafiya Dan kuwa gabanta tuni yafara zubarda Jini sosai na yamutsin dayake ciki.

Batai doguwar tafiyaba taji tana Neman haukace tuburan Dan haka ta nema bakin wata hanya ta zauna tana rusa kuka sosai tana tasa Inda ke mata sauki a jikinta.

Kukan datakeyi ne tana yagar jikinta yajawo hankalin mutanen dake kusa suka fara kallonta suna tausaya mata wasu Kuma Mai Mata video sbd ganin haukacewa zatai alokacin da alama asiri akai mata suke zargi.

Kayan jikinta take kokarin yagawa wata Mata dake kokarin Shiga motarta tayi saurin zuwa ta tareta tana masifa da masu Mata video.

Cikin kuka da azaba sosai Hadiza ta bude Baki daqyar tana cewa"

Dan Allah ki taimakeni kikaini asibiti su ciremin gabana wlh azaba,
Ciwo,zafi,radadi duka inaji.

Kallonta matar tayi da mamaki tana sake riqe Dan kareta da handbag dinta masu sbd daukanta.

Da mamaki tace"

Me yake Miki azabar?
Me kikeji?

Kasa magana Hadiza tayi tana sake bubbuga gabanta cikin ficewa hayyaci tace"

Dan Allah ku taimakeni.....

Da sauri matar ta tari taxi ta cewa Hadizan ta shiga batareda ta kamataba sbd tsoro da tsaro.

Tata motar tashiga tacewa taxi driver din yabiyota.

Wani asibiti suka nufa tasa aka shigo da Hadiza wadda ta fice hayyacinta tini bayan gurnanin azaba da wahala Babu abinda take.

Da gaggawa suka karbeta zuwa ciki suka fara dubata.

Gaban nata dataketa duka suka fara budewa suka duba.

Wata qara suka ringa saki cikin tashin hankali da tsoro.

Dayake wadda ta kawota asibitin likitace take suka taru suka gano haihuwa tayi gabanta yasamu matsala.

Cikin gaggawa da tashin hankali suka fara taimakonta.

Dayake gurin ya lalace sosai Saida aka hada da yimata Yar qaramar tiyata.

Bayan taimakon data samu sun Gama Mata komai an maidata dakin dazata kwanta tana bacci batareda tasan waye akantaba.

Dr iklimat itace ta biya komai na Hadizan tukuna ta wuce gida.

Kwananta uku a asibitin kafin yadawo cikakken hayyacinta ta zauna daidai tana Jin komai Yana dawo mata sabo yanda yafaru.

Tashi hankalinta yayi tafara kuka Mai tsanani na Dana sani da Neman 'yarta.

Da farko Dr iklimat ta dauka Hadizan nada ciwon qwaqwalwa ne Amma data zaunar da ita ta rarrasheta ta sanar da ita komai sosai hankalin Dr iklimat ya tashi Dan haka Hadizan na samun sauki suka dunguma Neman gidansu MAJEED.

Kasa gane anguwar tayi bare gidan Dan haka suka ringa yawon stations suma Kai report Amma ba wani labari.

Tashin hankalin da Hadizan tashiga yasa take Neman rasa nutsuwa da lafiyarta sbd ahankali yafara taba qwaqwalwarta.

Dr iklimat data fara tsorata da Al'amarin haka ta samu ta lallaba Hadizan takaita Inda tafara ganinta tace tayi tanuni daganan ko Zata iya game gidansu MAJEED din.

Kaman qwaqwalwarta bazata tunaba sai gashi ta tuna suka ringa bin Inda take tunawa har Allah yasa suka Isa kofar gidan.

Basuga tashin hankali ba Saida aka tabbatarda MAJEED da babyn baasan Inda sukeba.

Take agurin Hadiza ta suma,
Haj umma ma Jin maganar dake bakin Hadiza yasata zubewa itama tana dafe kirjinta dake kokarin tashewa da tashin hankali Mai tsanani.

Daqyar su Anty safiyyah da taimakon Dr iklimat ta Dan dawo daidai.

Kuka tafara tana yiwa Hadiza Allah ya Isa akan abinda tayiwa MAJEED ta rabasa da uwarsa akan 'yarta Mara uba da asali.

Hadiza Kam saidai akai asibiti da ita.

A asibiti tana farfadowa Bata iya kukaba sbd zuciyarta dake barazanar daina bugawa.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/7, 10:23 AM] +234 903 125 2820: *_44_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Inayah da kafafuwanta suka kasa riqeta sbd kukan datake Mai tsanani Mara sauti ahankali ta juya tana dafa bango ta nufi dakinta...

Daqyar ta iya Kai kanta daki sbd ko ganin gabanta batayi sbd kuka hannuwanta na toshe da bakinta.

Tana Isa bakin gafo ta silale Wasa ta zauna tana sake sabon kuka.

Abbinta kawai zuciyarta kewa wannan kukan sbd sam ita batajin tanada wani abun tausayi tun jarinta har yanzu sbd Abbinta bai taba Bari ta Zama abar tausayawaba tun tana cikin zanin goyan da uwarta ta yarda ita ta tafiyarta.

Taji tausayi da kaunar mahaifiyarta saidai Kuma har lokacin kaunar kaunar Abbinta daban take a ranta Musamman yanzu datake qaunar tasa na qara nauyi da cikin ranta Dan kuwa har abada Batajin Zata karbi mahaifiyarta matuqar ba abbin ne ya yafe Mata ba ya hadata da ita.

Neesah ce ta fito toilet taga yanda Inayah din ke kuka ta qaraso tana kallonta cikin mamaki da firgici tace"

Lafiya?
Wani abin yakuma faruwa ne?
Haryanzu Baki samu abbin bane a waya?

Kasa magana tayi ajiyar zuciya datake jerowa idanuwanta sunyi jajir.

Umma yaganah ce tashigo dakin fuskarta jajir da alamar kukan datasha sbd tausayin MAJEED datake Jin itama kaunarsa da girmansa  sun ninku a ranta sbd ya tabbata Mai tautasayi da kyakkyawar zuciya duba da yanda itama ya riqeta da Maigidanta kafin ya rasu har zuwa rayuwarta daya Gama ingantawa yazama gatanta Mai kare mutuncinta da martabarsu yabasu suna da mutunci a idon duniya.

Tabbas har abada daga ita har Inayah basuda tamkarsa Kuma zasuci gaba da Zama a qarqashin ikonsa da sunan Daya Basu,
Yazama ubansu gatansu Kuma zaici gaba ra zama hakan har abada da yardar Allah.

Inayah na ganin umma yaganah ta sake fashewa da kuka tana fadawa jikinta tana cewa"

Umma yaganah Abbina nakeson gani kawai yanzu,.bana samun wayarsa Dan Allah ki kirasa yadawo gida na Dena duk wani rashin jin magana,,,
Ni har aurenma na karba zanyi auren dashi Dan Allah kice ya Dena fushi Dani yadawo.

Umma yaganah data kasa cewa komai bayanta kawai take Dan bubbugawa tanajin kaunarsu su dukan duk da Inayah tako ina bata Zama abar tausayiba Dan kuwa rayuwarta tagama samun haske tunda MAJEED ya tsaya Mata.

Umma yaganah Bata sake Jin tsananin kaunar auren MAJEED da Inayah dinba sai yanzu Da komai ya bayyana.

A duniya Babu Wanda ya cancanta da Inayah dai Abbinta majeed Wanda shi wannan auren ya zamarwa dukkaninsu RIBA BIYU.

Rarrashinta umma yaganah tayi tareda Neesah wadda take sauraran maimaicin zancen komai abakin umman wadda ke fadawa Inayah komai batareda tasan taji komai ba.

Sun jima a daki suna rarrashin juna kafin a dakin Inayah din dayafi kowane daki girma da tsaruwa a gidan Banda na Abbinta daya banbanta da nata ta hanyar tsarararren palonsa dake hadeda master bedroom dinsa Wanda shima komai na cikinsa milk ne sbd tsananin tsaftarsa yafison komai me haske bazai bayyanar Masa da komai qaqantar datti Dan ya rabu da ita.

Gidan tsit kaman ba kowa saisu zubbi da Salimat dake aikin kaida kawon abinci da maimaicin tsaftace gidan,

Haj umma da Anty juwairiyyah na daki
Anty juwairiyyah sai kame kame takeyi sbd kunyar kanta data mahaifiyarsu saidai Kuma tana maimaitawa Haj umma girman lefin MAJEED dayaqi waiwayo gida ya zabi 'yar tsintuwa akan mahaifiyarsa.

Itadai Haj umma Bata tankataba sbd yanzu Babu wani Hadi dazai sake rabata da 'danta ciki kuwa harda Inayah wadda ta tsaya Mata arai sbd kaunar da aketa maimaita majeed dinta nai Mata.

Sai dare kowa ya fito cin abinci suka hade a dining kowa na kallon dan uwansa Banda Inayah wadda kafin ta fito sai yawon zuwa kiranta tazo taci abinci kowa keyi daga umma yaganah har masu aikin da Neesah.

Saida suka fara cin abincin ta fito sanyeda Gucci Riga da wando gajere Wanda ya bayyanarda fararen qafafunta masu kyau da lafiyar fata.

Rigar batada Fadi sosai Kuma Bata saka bra ba sbd kusan Shirin baccine tayi.

Slippers ne a qafarta da wayarta a hannu tana sake saka Kiran Abbinta Wanda duk yakira bai shigaba sai idonta yacika da hawaye.

Qamshinta kawai yasa Anty juwairiyyah sake Baki tana kallonta sbd tasan Qamshin Turaren da tsadarsa tunda tana yawon qasashe.

Haj umma kuwa kayan jikin Inayah din da yanda take wani irin Bata fuska kaman zata fasa kuka take kalla cikeda mamaki,

Lallai yarinyar tasamu sake fiyeda yanda suke tunani.

Zama Inayah tayi Kai tsaye batareda ta kalli anty juwairiyyah ba ta gaida haj umma da cewa"

Haj umma Ina wuni?

Ita kadai ta gaida Dan haka kowa yayi tsit,

A natse hajiyar ta amsa itama batareda takuma kallontaba.

Cikin daure fuska umma yaganah tai Mata nuni da juwairiyyah wadda ke juran Inayah din tawi gaidata Tai mata fada tatas ba ruwanta da gatan dataga yayiwa yarinyar yawa.

A hankali ta gaida anty wadda ta haifeta nesa ba kusaba Dan kuwa yarta ta fari ta girma Inayah din sosai.

Wannan auren datakeyi yanzu yayanta biyu Dan haka yayanta uku
Auren ne irin na yayan masu kudi bawani Zama takeyiba kusan koyaushe taso tana gidansu kokuma yawon wata qasar dauko kayan business,

Anty safiyyah ce kawai take Dan Zama gidanta itama sbd aikinta datakeyi Dan haka Bata wani yawo ko tafiya sai wadda ta danganci aiki
Itama yayanta uku bayansu Bata qaraba ko yanzu da Alhaji babbah dakansa ya aiko nemansu Bata samu biyosu Haj umma ba sbd aikinta da Bata Wasa dashi shiyasa sukazo su kadai.

A taqaice anty juwairiyyah ta amsa gaisuwar tana zuba abincin dazataci.

Zubbi Inayah tafara zubawa tuwon semo da vegetables soup dataji Naman rago da ganda da kifi.

Tana Gama zuba Mata ta kawo Mata ruwa Mara sanyi dan ita batashan ruwa Mai sanyi
Yana daya daga cikin koyarwar Abbinta tun tana qarama baya barinta da sanyi kowane iri ne sbd sanyin dayaso shigarta tun tana jaririya.

Da spoon takecin tuwon Dan haka hankalinta ya rabu akan abincin da wayar hannunta.

Dungurar da wayar tayi da qarfi akan dining tana sakin qaramin tsokin rashin samun Abbinta Dan zuwa yanzu hankalinta yafara tashi da rashin jinsa.
Chapter 46 · 0% Book details