← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 65

Sashe 7

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin tayi wayon datake dashi yanzu yasha wata irin gwagwarmayar wahalalliyar rayuwa Dan samarda abinda zai rainar masa ita.,

Karatun jamia yake alokacin hakama bayada aikin komai face kalolin aikin wahalar daya ringa yi Yana samarda abubuwan da kowane baby zai buqata.

Cikin wani irin tsananin hali yasamu ya kammala karatunsa yayi service yafara zuwa yan ayyukan da zasu ringa taimaka masa Dan lalurarsa data 'yarsa.

Sana'ar gadin wani gida yafarayi tsawon watanni kafin Mai gidan yabar qasar Dole ya nema wata aikin.

Daqyar yakuma samun aikin security a wata private hospital.

Da Wannan aikin yake rayuwa kafin raga baya yasamu aikin wankin mota yana hadawa dashi.

Shekarar inaya uku yafara tunanin aure badan Jin dadinsaba ko Dan yanajin buqatar hakan
Kawai dai zaiyi auren ne Dan ya samarwa 'yarsa kwanciyar hankalin samun mutum ataredasu ko zata sake tayi rayuwa Kamar kowanne yaro,
Amma badan wai ya Samar Mata uwaba,
Har abada shine uba Kuma uwar INAYArsa,
Har abada babu mace data Isa ta zamto uwa ga INAYA,
Shine uwa Kuma uba
Ita kanta Inayah duk da qarancin shekarunta tariga ta Dan San halayen Mahaifinta Dan haka ta daina ambatar sunan mahaifiya tuni sbd Hani da yayi mata da hakan aduk lokacinda bakinta ya furta Mama.

Alokacinda yayi neman auren farko ga 'yar Mai Basu sallah a masallacin anguwar da farko lafiya kalau yafara zuwa fira bawai danma yasan Mai zaiyita fadaba sbd shi miskilin mutum ne shiyasa Bai cika shiga mutaneba,

Iyakacinsa da 'yan anguwar da mutanen gidan hayarsu gaisuwa
Itama gaisuwar sbd sanin mahimmancinta a addini ne.

Da yawa mutanen anguwar da mutanen gidansu na haya kallon me girman Kai da Rashin mutunta mutane suke masa saidai Kuma basa iya fada gaban idanuwansa sbd kwarjinsa da kamewar mutuncin kansa duk da kasancewarsa qaramin matashi.

ABDULMAJEED ABBI kamar yanda yarsa ke kiransa kusan hakan kowa ya sansa,
Wani irin baudadden mutum ne da babu Wanda yake iya gane inda ya dosa,
Meye ne acikin ransa?,
Meye abinda yake tunani?,
Waye shi?

Sam babu Wanda yace yataba ganin koda murmushinsa bare dariyarsa sbd
Bayan 'yarsa babu Wanda ya taba yiwa koda murmushin bare dariyar
Dan haka kusan kowa baya masa dogon shishigi
ciki kuwa harda yan saka idon anguwa da munafukan anguwa kowa ya kama kansa dashi
Zagi dai ne Idan anzauna dattijawan anguwa da Basu San su kama girmansuba sai sunyi saka idon kullum cikin zaginsa sukeyi sunayi dashi a fakaice
Idan yawuce ta gabansu yayi musu sallama ya gaishesu haka zasu ringa washe Baki suna amsawa suna yabonsa da yabon 'yarsa
Daya wuce zasu fara zundensa.

Aurensa da Hafsat yar liman ya lalace ne bayanda aka zuga mahaifin nata da cewar ana zargin zafin zuciyarsa da baqar zuciya kamar kuturu ya ringa azabtarda matarsa da duka da yunwa da wahala da baqin talauci ta gudu ta barsa da jinjirar 'ya bayan ta haihu,

Wasu Kuma suka ringa fadar bada aure ya Haifa yarsaba Dan haka hafsatu renon 'yar gaba da fatiha kawai zata tayi.

Wannan zugar ta lalata maganar aurensa da Hafsat wadda take tsananin sonsa Kuma shi kansa har cikin ransa ya yaba da nutsuwarta yayi shaawar auranta ta zauna da Inayah.

Bayan an hana masa auren hafsa bai cire raiba sbd yanzu sosai yakeda shaawar samarwa Inayah Mai zama da ita Dan haka tunanin yin auren yashigesa sosai bawai Dan har lokacin tunaninsa ya sauya akan Mata bane dakuma Wai Jin Yana son aure ko mace ba,
Sam Mata bayada shaawarsu ko kadan,
Baya Kuma Jin tunaninsa da tsananin yanayinsu zai sauya a zuciyarsa har abada.

Fatima yakuma nema aure a bayan layinsu
bayan ya Dan kwana biyu Yana zuwa fira gunta daganan ya aika Mijin Yagana da Daman shine kawai yake tsananin ganin girmansa da mutuncinsa ya nema masa aurenta.

Kamar yanda tafaru farko hakance takuma faruwa
Har anbasa auren daga baya aka fasa sbd wasu maganganun da aka Kuma kaiwa mahaifanta itama.

Cikin qanqanin lokaci Saida ya nema aure so hudu ana hanasa daga Nan Mata suka Kuma ficewa a Ransa kwata kwata
Musamman sbd yanda aka dauki hanyar aibata masa 'ya sai hakan yakuma tsananta qamewar zuciyarsa akan Mata da mutane,
Bai Kuma shaawar neman kowace macen ba,
Yacire maganar aure daga ransa kwata kwata har abada bayajin zai Kuma kallon kowace mace da sunan wani abu face sunansu na mace.

Daga Wannan lokacin burinsa ya sauyu ya karkata ga ilmantar da 'yarsa yakuma dage ba dare ba Rana da Neman aiki da mafita dama Kuma karatu dayakeson qarawa sbd babban burinsane Dana mahaifinsa tun Yana raye.

Aikin wahalarsa dayakeyi ya matuqar tsananta Dan kuwa bayan security na asibiti da aikin wankin mota yanzu harda sana'ar 'dan acaba yanayi Idan yasamu abokin aikinsa na gurin aikin security ya basa Aron mashin dinsa yayi.

Rayuwa Mai tsanani da wahalar gaske yake gudanarwa,
Baya samun cin abincin dazai kosar da cikinsa,
Duk Rana da dukan ruwan dayake Sha na fafatawar ayyukan wahalar dayake duk na inganta rayuwar Inayah ne,
Ita yake siyawa Yar sitirar sakawa sbd ko sitirar arziki basudashi,
Abincinta da Shanta sune yake iya kokarin samarwa,

So da dama haka yake wuni da yunwa  saidai yasha ruwa da Dan biredi haka ya kwanta amma Inayah baya taba Bari ta nema abinci ko abin buqata ta rasa.
Ahaka yake gudanar da rayuwarsa acikin wani irin tsananin hali.

Yagana tana samun aiki a private school ta primary ya dage yayo wahalarsa yasamu ya saka Inaya duk da kusan shekarunta sunyi qanqanci Amma haka ya sakata sbd a gida yagana ta dena zama aikin take zuwa
Shima gashi yanzu ya sake dagewa da ayyukan wahala iri iri da yawon Neman aiki
Dan haka kullum yake kaita makarantar idan yadawo da wuri ya biya ya daukota Idan baidawoba anan take zama tareda yagana har sai antada Yan primary kowa ya tafi sai sudawo gida ta zauna gurin yagana harya dawo,

Yana dawowa yake tsayawa gurin yagana ya dauketa su shige Bata qara fitowa dakinsu sai washe gari Idan zaije sallah wani lokacin yakan kaita gurin yagana yaje yadawo
Wani lokacin Kuma rufeta yake a dakin yaje yadawo sbd itama Kaman tayi gadon mahaifin nata miskilace ta gaske batason zuwa koina tafison ta zauna gurin Abbin nata.
Musamman sun saba rayuwarsu daga ita sai shi.

*****
Wani tsautsayi daya samesu shine dakinsu daya fara zubar ruwa ta sama Idan ana ruwa yasa tunda damunar ta tsayu sosai yadaina baccin dare,

Zaune yake kwana yayi gadin Inayah tayi bacci sbd gudin yanayi na tsautsayi ko zai riskesu,

Da safe kafin su fita zai kwashe ruwan daya taru a dakin ya goge musu ya gyare dakin dako ledar qasa babu sai Rabin dakin ne kawai keda Leda Shima gurin katifar Inayah sbd kada sanyi ya kamata.

Sauyin aiki akai masa daga security na asibiti zuwa na wani super market.

Ranar farko daya fara aiki a super market din yahadu da wani class mate dinsa a gurin.

Da farko Nuradden ya bayyanarda mamakinsa sosai ganin A MAJEED a matsayin security sbd sanin tsananin ilimi da kyakkawar takardun da MAJEED din yake dasu Dan haka Bai wani boyeba ya bayyanarda mamakinsa tareda yimasa tayin wani aikin wanda yafi Wannan.

Da farko MAJEED yaso kaucewa tayin Amma Nuradden din ya dage tareda tabbar masa ba daga garesa bane taimakon dagaske maikatan ake nema.

Amincewa yayi washe gari ya Isa makekiyar maaikatar kasuwancin mahaifin Nuradden din cikin saa yasamu aikin cashier na daya daga cikin manyan malls dinsu sbd sunason fara jarabta aikinsa kafin su basa wani aikin daya kamata shima sbd Nuradden yayita zuzuta musu ilimi da MAJEED din yakedashi
Dan hkaa ahankali cikin yardar Allah yafara aikinsa na cashier a gurin.

********
Tunda yasamu aikin cashier a taqon mall din rayuwar tafara yi masa sauki shida yarsa harma da yagana da mijin yaganar sbd shi din mutum ne Mai alkhairi musamman ga mutanenda suke tsananin kaunar Inayah,

Duk Mai kaunar Inayah to tabbas matsayinsa a cikin ransa Mai girma ne,
Yanda yake tsananin kaunar 'yarsa Jin yake komai zai iyayiwa duk namijin daya aurawa ita duk ranarda ya cutatar masa da ita,

Wasu lokutan har fargabar yanda zai fara fuskantar bayar da ita aure zuwa wani gurin yake Dan haka alqawarine Mai girma acikin ransa na zai wadatar da ita da ilimin Mai zurfi sbd rayuwa a gidan wani tayi Mata sauki.

Majeed sam Bai damu da abun hannunsaba duk lokacinda yasamu 'yan kudade baya qyashi haka zai kashewa Inaya sauran Kuma ya bawa su yaganah Suma tunda ba laifi suna cikin yanayin rayuwa suma,

Basu taba haihuwaba itada mijinta wanda yake zaune baya iya fita nema sbd yanayin Rashin lafiya dayake ciki na sugar gashi anyanke duka qafafun nasa biyu duk sbd lalurar a keke yake rayuwa,
Dan haka shigowar Inaya da Abbin nata rayuwarsu ba qaramin taimakawa rayuwarsu yakeyiba
Hakannema yasa duk yanda ake gulmar da zindensa babu ruwansu basa shiga sbd sukam majeed kusan shine rufin asirinsu yanzu
Suma qarshe aka ringa binsu da zagin makwadaita Dan sungansa kalar 'yayan masu arziki dama Kuma a wani bangaren da yawansu suna masa kallon Wanda yafito daga zuriar masu hannu da shuni Kuma duk iya gulma da bin diddiqi ankasa sanin asalinsa dakuma inda yafito.

***Ahankali Lokaci yaja sosai har INAYA ta kammala nursery tashiga primary hartayi nisa tana primary 4.

Har lokacin a mall yake aiki saidai ba laifi yasamu qarin girma sosai harya zama assistant manager,

Alhmdlh komai Yana tafiyar musu a daidai dan kuwa babu kalar Jin dadin da Inayah Bata samu gurin mahaifinta sai Wanda baa rasaba daidai gwargwadonsa.

Yanason tashi yabar gidan ya kama haya wani gurin sbd 'yarsa datake girma gashi gidan gidan tarone mutane iri daban daban
amma Kuma sbd rayuwar kadaici da zata iya wargaza Mata walwalarta data fara samu sakamon girma data fara shiyasa Bai tashiba gidan har lokacin Amma zuwa lokacin yanada halin sauyawa din tunda sunfara samun rufin asiri.

Inaya na gaf da kammala primary 4 yasamu hayar wani gidan acan hanyar gurin aikin nasa Dan haka yafara musu shirye shiryen tashi duk da ba wani kayan suke dashiba bayan katifar baccin Inayah sabuwa Mai dakan mutum daya,
Sai qaton bargon dayake shimfidawa qasa ya kwanta sai jakar kayansu da 'yan abubuwan amfanin cin abinci.
Chapter 7 · 0% Book details