← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 65

Sashe 57

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana ganinsa ta maida idanuwanta akansa tana Jan numfashi cikin zafi..

Hannuwansa biyu yasa ya tallafota Kai tsaye daga kan kujera zuwa jikinsa Yana Kiran sunanta cikin yanayi na kulawa sosai da damuwar meya sameta.

Daqyar taja numfashi tana tsiyayar hawaye ta bude Baki ahankali tace"

Abbi aure zakayi????

Bata fuska yayi cikeda mamakin yanda taji zancen take ransa yayi mummunan baci Amma dayake bakowa ke gane yanayinsa ba duk Basu ganeba.

Ruwan da umma yaganah ke miqowa ya karba ya Kai Mata abaki cikin sanyi yace"

Relax and breath,
Just breath,
Yawwa deep breath,
Sake Jan numfashin...

Yanda yace tayi takeyi ahankali numfashin nata na daidaituwa ahankali ahankali.

Sam taqi dagowa ta kalli kowa dakin sbd haushi da zafin kowa takeji hardasu umma yagananta.

Ganin tadan dawo hayyacinta yasashi juyowa ya kalli Dr farhat dake kallon ikon Allah Dan tasan Inayah itace mafi so da kauna a rayuwar Abbinta Kuma tasan sangarta da shagwaban Inayahn Amma Batasan yaushe tafara boriba haka kokuwa Dan Bata taba rigima bane gabanta?

Qatuwar budurwa na irin wannan tashin hankalin Amma mahaifinta ko damuwa yayi Mata ko 'yar tsawa baiyiba saima kokarin dawo da ita daidai yakeyi cikin sanyi da nutsuwa tareda boye tashin hankalinsa na ganinta hakan.

Haj umma dake tsaye sake da Baki cikin mamakin dayafi na kullum ya Dan kalla Yana danne yanayinsa kafin ya kuma maida kallonsa kan Dr farhat Kai tsaye yace"

Dr zaki iya tafiya I can handle this,
Thank you.

Juyawa tayi ta kalli Inayah cikin kulawa ta nufeta zatai Mata magana
Inayah tayi saurin fara kokarin miqewa tana kokarin janyewa anty Hafsat ta dafeta tana kokarin tausarta kafin takuma borewa.

Ganin hakan yasa Dr farhat dakatawa tana kallon MAJEED Daya dauke Kai ba annuri ko daya a fuskarsa da duka abinda kowa yayi agidan.

Murmushin yaqe tasaki tareda yimusu sallama ta yiwa Inayah fatan samun sauki ta wuce.

Shiru ya danyi tareda sake hadiye 'dacin ransa ya juyo ya kalli Inayah dake hawaye sosai har lokacin ta dago ta kallesa take taji wani sabon 'daci da qunci na cika ranta matuqar Abbinta zai auri wata mace....

Tasowa tana sakin sabon kuka Zata bar dakin umma yaganah ta riqeta tana cewa"

Zan mareki idan bazaki nutsuba
Ba'ason hauka kinji ko??

Sabon kuka Mai qarfi ta saki tana cewa"

Umma yaganah bazan iya nutsuwaba Ni kubarni natafi banason ganin kowa....
Aurenma banayi na fasa bazan zauna da kowaba da Abbina.....

Sai alokacin Haj umma ta fahimci duk wannan tashin hankalin akan meye,

Takaici ne da mamaki suka tarar Mata wato duk wanna daga hankalin jama'ar gida da borin kaman me tashin iska da asthma duk akan ance MAJEED zaiyi aure ne?

Wannan halin na Inayah na shashanci Yana Bata takaici da damuwa Dan haka cikin siqewa tace"

Yanzu dama duk wannan ihun da tashin hankali dakikeyi kika daga hankalin kowa duk akan majeed zaiyi aure ne?

To so kike gabaki daya ya qare rayuwarsa gurin tattali da renonki shi Kuma bazai Gina tasa rayuwarba?
Da Ina tareda shi tunima dayayi auren Dan bazai zauna saidai yaga 'yaya wasu na tarawaba shine zakizo kina shirmen ihun kuka da......

Cikin kuka Inayah tace"

Ni nace bazan Tara Masa 'yayan bane?
Ai Nima Zan Haifa Masa idan kika barmu...

Fiddo idanuwa Haj umma tayi cikeda mamaki,

Su umma yaganah da Anty Hafsat ma tsit sukai yau ciwon bakin Inayah yayi musu Dadi duk da duk kunya ta kamasu da sauri umma yaganah ta buge Mata bakin sbd karta qarasa.

Shi kansa abbin kasa magana yayi sbd mamakin bakin Inayah Daya Gama wuce tunaninsa hakama da bacin ran zancen dasuka sanar Mata da wani abin yasameta ayau acikinsu babu Mai abin fada masa sun kashe Masa 'ya ko me??

Numfashi ya sauke a boye Yana sake kawar da bacin ransa ya kalli Haj umma dake kallonsa jiran abinda zai fada sbd duk suna iya hango zallar bacin ransa duk da boyewar dayake kuwa.

Daidaita kalamansa yayi cikin nutsuwa yace"

Umma Ina dauka maganar auren Dr farhat bamu gama meyasa zaku dagawa Inayah hankali da zancen bayan bawai Kai karshen maganar akayiba.

Umma yaganah da Anty Hafsat ya kalla suma yace"

Meyasa zaku sanar da ita umma tunda kinsan halinta
Yanzu gashi tana neman illata kanta akan hakan,

Maganar aurena da Dr farhat Kar akuma tadasa a gabanta sbd ba........

Maganarsa tasa Inayah fashewa da sabon kuka tareda juyawa da gudu tabar wajen tana cewa"

Kenan yin auren zaiyi da Dr farhat.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/9, 9:52 AM] +234 806 355 6266: *_53_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Rintse idanuwansa dasuka Dan sauya yayi tareda juyawa yabar gurin shima Yana kansa na Kuma sarawa dama gashi kwana biyun Yana fama da ciwon kan.

Yana barin gurin umma yaganah Haj umma suka kalla itada anty Hafsat sukaga yanda tayi zuru da mamaki dashiga tunanin agaban kowa MAJEED zaiyi mata magana Mai Kama da fada kaman shine uban nata.

Juyawa tayi jiki a sanyaye ta koma bedroom dinta tanaji wayarta na ringing juwairiyyah na Kira takasa dauka sbd ranta ba Dadi ko kadan bazata iya wani bacin ranba sbd yanzu juwairiyyah Zata sake dorata akan abinda zai quntata ranta.

Anty Hafsat Kuma bayan Inayah tabi zuwa dakinta Dan tausarta Amma rarrashinta duniya tayi Inayah din Taki Dena kuka.

Har bayan magriba suna fama da Inayah din Haj umma dake dakinta tana Dan jiyo yawon umma yaganah da Anty Hafsat gurin rarrashin Inayah din sama sama
tayi banza dasu sbd gabaki daya ganin takeyi su suka Gama lalata Inayah din da bakinta baya tauna magana sam Sam.

Ana gap da ishai haka anty Hafsat ta hakura ta tafi gida tabar umma itama tayi nata rarrashin ta hakura ta zubawa sarautar Allah Ido.

Abincin dare ma kusan daga ita sai Haj umma ne sukaci Inayah taqi fitowa shima MAJEED din baizoba Koda Haj umma takirasa shayi kawai yace akai Masa.

Zubbi ce takai ta ajiye Masa a palonsa ta fito ta dauki da Inayah ma da umma tace ahada Mata takai mata Amma ko motsawa Inayah batayiba tana kwance.

Duk dubara da rarrashin umma yaganah Inayah kin Shan ko tea tayi Dan haka jiki a mace umman ta barta taje ta kwanta.

Zafi da ciwo zuciyarta ke Mata sosai bayan hawaye Babu abinda takeyi sbd bazata taba iya kwatanta Abbinta da wata macen ba,

Wannan zafin datakeji har abbin ma takejin zafinsa akan lamarin.

Kwana tayi da ciwo a Rai da damuwa me tsanani Dan haka Koda garin ya waye da wani zazzafan zazzabi ta tashi Mai qarfi.

Zubbi da umma yaganah ne akanta hankali tashe umma na rage Mata zafin gashinta da farin qaramin towel
Zubbi kuwa chocolate custard me zafi ta hado Mata da farin soyayyan qwai Mara komai aciki.

Kasa Shan komai tayi Saida umma yaganah ta nuna Mata rauninta na itama Zata iya kuka idan Inayahn bataciba kafin Tasha custard din aikuwa ko Gama Sha bataitaba amai ya taso Mata da sauri zubbi ta kamata takaita toilet ta ringa Aman cikin wahala sbd rashin qarfin jiki.

Bayan tagama ruwan zafi zubbi ta hada Mata tayi wanka ta fito umma ta dauko Mata wata qaramar Riga Mara tsayi Mai taushi ta saka Takoma ta kwanta jikinta na tsananta zafi.

Wanke toilet zubbi tayi ta gyare dakin tsaf ta kashe Mata AC ta kunna humidifier bayan tazuba wasu turaruka cika masu dadi suka fice daga dakin har umma.

Umma na barin dakin tana Isa nata ta dauki wayarta ta saka Kiran MAJEED.

Ta jima tana ringin kafin ya daga murya ahankali yace"

Barka da yau umma.

Barka MAJEED,
Yau baka fitoba Allah yasa lfy dai ko?

A natse Yana danne yanayinsa yace"

Lafiya kalau alhmdllh,
Yaya Inayah?
Tana Nan tana Rigimar ko?

Numfashi ta sauke a sanyaye tace"

Tanata rigima tun jiyan gashi yanzu ciwo yashigo ciki sbd zazzabi Mai qarfi takeyi custard ma datakeso Tasha tayi amansa,

Bansaniba ko Dr farhat din zaa Kira tazo ta dubata Amma Kuma wata sabuwar rigamat zatayi tana ganin Dr farhat din.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda cewa"

Ganinan zuwa zanfara dubata kafin Akira likitan.

Kashe wayar umma tayi tareda ajiyewa gefe tana Zama kan kujera tana cewa"

Allah yasa ta tsaya taji maganarka.

Kwance take tanajin zazzabin sosai bacci na Dan daukanta Yana sakinta duk da hakan tunanin Abbinta da aurensa na maqale cikin ranta.

Turo kofar dakin yayi Kai tsaye tareda shigowa a natse sbd shima ciwon Kaine atare dashi.

Fararen Fendi wears ne ajikinsa
yau Qamshin nasa ma ahankali yake tashi daga jikinsa sbd Bai wani saka turareba Qamshin na jikinsane daya dade da Kama Turaren Mai sunyin Dadi.

Cikin nutsuwa ya tako har bakin gadon ya tsaya Yana kallonta ahankali cikin nutsuwa ya lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta cikeda kaunarta Mara sirki da qarfi wadda take gine cikin ransa shiyasa Sam Baya son bacin ranta ko damuwarta Amma tacika rigima yanzu duk akan aurensa dake kanta data dauka ta saka arai.

Bude idanuwanta dasukai nauyi da sauyawa sbd zafin zazzabi Jin mutum akanta tasan Abbin ne sbd qamshinsa daya shiga hancinta.

Maida idanuwanta tayi ta rufe tanajin nauyin kirjinta na qaruwa sai kawai hawaye suka fara gangaro Mata.

Yana ganin hawayen nata yaji jikinsa yaqara sanyi ya zauna ahankali bakin gadon nata tareda Kai hannunsa dakeda sanyin ACn Daya fito ya taba goshin yaji zafinsa sosai

Da kulawa sosai yace"

Da wannan zazzabin naki ajikinki kike sake wani kukan Inayah??

Kinason ciwo ya kwantar dake ne?
Meyasa bazaki Dena kukanba haka?

Juyar da kanta tayi tana sake sakin kuka Mara sauti a wahalce batareda tace Masa komaiba.

Shigowar Haj umma ne tareda Salimat data kawo wasu ruwan da towel Zata rage Mata zafin jikinta da umma yaganah tace zubbi takuma Yi Amma zubin na aikin gyaran Haj umma Dan haka ita takawo.

Haj umma kuwa duba Inayah din tazo yi sbd rashin lafiyarta yasa gidan kaman anyi mutuwa kowa tsit ba walwala tunda princess din gidan ba lafiya.
Chapter 57 · 0% Book details