← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 65

Sashe 49

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daqyar hajiyar ta sakesa ta dago tana kallon fuskarsa da shima ita yake kalla muryarsa a sanyaye yace"

Umma..kin yafemun?

Gyada Kai tayi da sauri tana hawaye tana murmushi duka alokaci daya tace"

Na yafe maka MAJEED,
Na yafe maka,
Nice nayi kuskuren bakaiba..

'dana yadawo gareni ya Allah nagode maka.

Ahankali ya Dan sunkuyar dakai Yana hadiye hawayensa cikin nutsuwa da farin ciki Mai yalwa shima yake yiwa Allah godia,.

Kuma dagowa yayi ya kalli anty juwairiyyah dake tsaye itama tana kallonsa duk tunanin duniya ya ninku akanta sbd ganinsa ya tabbatar Mata da arzikin dasuka gani ma kenan Wasa ne,

Majeed din yakoma wani hakimtaccen namiji Mai zallar kwarjini da cika ido,

Ita kanta datake yayarsa Jin tayi tana Neman kasa hada Ido dashi Saida tayi da gaske Bata Ankara ba taji bakinta na furta"

Sannu da dawowa MAJEED.

Qayataccen murmushinsa yasake cikin nuna farin cikin ganinta itama ya miqa mata hannunsa daya Yana cewa"

Ina farin cikin dawowarku rayuwata kema anty juwairiyyah.

Dayake sun saba da shaking hannuwa tun suna Dan kaunar juna Dan haka ta miqa hannu takama nasa tana bayyanarda farin cikinta na ganinsa itama.

Hannunsa cikin na hajiya da Anty juwairiyyah ya juyo ya kalli umma yaganah da Inayah dake tsaye tana kallonsa da idanuwanta dasuka Dan sauya da yanayi Dan Jin wani iri Abbinta zai Zama ba nata Ida kadaiba yanzu tunda family dinsa zunzo Bayan tasaba da Baya hadata da kowa bare komai.

Kasa sakinsa hajiyarsa tayi Dole anan suka zauna duk da gajiyar tafiyarsa ta sakesa take sbd farin cikin ganin mahaifiyarsa.

Cikin nutsuwa da sanyinsa yace"

Umma yaushe kukazo?
Waye yakawo?
Ya kukasan Nan?

Cikin farin ciki tace"

Majeed bazan taba iya rabuwa dakaiba yanzu sbd haryanzu Bayan ganinka ciwon da zuciyata take na rashinka Bai dainaba..

Alhaji babbah da kansa yayi aikin mutum har gida aka taho damu Bayan Kiran waya dayayita yimun..

Banda zabi Bayan zuwa din sbd Nima Ina Neman 'dana Ido rufe,

Meyasa katafi baka dawo gareniba MAJEED?
Meyasa baka taba waiwayataba majeed?

Kuka ta fashe dashi tana bayyanarda tsananin radadin da zuciyarta tashiga na rashinsa duk tsawon lokacin.

Anty juwairiyyah ce dashi suka ringa rarrashinta Yana sake Bata hakuri akan kuskuren rashin komawa dakuma kuskuren zaban tafiya yabarta,

Bai tsaya Jan tado zancenba ya yarda da suka shine mai lefin yabata hakuri tareda alqawarin insha hakan bazata Kuma faruwaba.

Umma yaganah ma ta Dan saka baki tasake bawa hajiyan hakuri da adduar Allah ya tsare gaba.

Inayah data matsu sugama tayi magana da Abbin ta matso tareda Zama gefensa daya tana kallonsa cikin yanayin son magana zatai magana ya Dan saci kallon hajiyarsa Dan yasan idan ba yanzu ta sauyaba zataji damuwar shigewar da Inayah Tai Masa Dan haka cikin Dan kulawa da nutsuwa ya kalli Inayah din yace"

Inayah kina gaida hajiya yanda yakamata tunda tazo kuwa?

Kallon hajiyar tayi tace"

Eh Abbi kullum safe da yamma har dare ma wani lokacin.
Kuma tare muke cin abinci a dining.

Dan murmushi yayi Yana cewa"

Kin kyauta to.
Jeki ki saka kayan sanyi
Ana wannan sanyin Zaki fito haka?

Umma yaganah ya kalla yace"

Da mutane a gida shine take yawo hakan?

Kallon Inayah tayi tace"

Kasan Inayah ba Jin maganata takeyi sosaiba.

Abbi banajin sanyi fa,
Nidai Zan sauya Kaya Amma saika yafemun kadaina fushi Dani,
Abbi Dan Allah kayi hakuri ka daina fushi Dani wlh nafadawa umma yaganah nayi alqawari ko sunan Heart bazan Kuma ambataba,

Ni har aurenmu ma na karba zanyi
Amma Dan Allah Abbi ka yafemun.....

Hawaye tafara tana riqeda hannunsa cikin yanayi da dana sanin lefin data aikatadin duk da batasan takamaimai akwan wanne daga cikin lefin take fushi da itaba.

Nauyin mahaifiyarsa mai tsanani yakeji Musamman ganin duk sunyi zuru suna kallon ikon Allah Dan Inayah dinnan tafara wuce tunaninsu
Gashi kaman majeed din biye Mata yake da alama shiyasa tabarar tata take yawa.

Zame hannunsa yayi Yana kallon umma yaganah yace"

Kuje ciki zamuyi magana gobe idan na nutsu.

Gangarowa hawayen Inayah sukayi tace"

Abbi gobe?
Nidai bazan iya bacci ba idan baka dena fushi daniba ka yafemun.

A natse ya juyo ya kalli fuskarta cikin kulawa yace"

Bana Hana wannan kukan ba?
Kije ki saka kayan sanyi
Anjima zamuyi mgn.

Ok Abbi" tace muryarta a sanyaye.

Tashi tayi ta wuce umma yaganah tabita suka Basu guri yabisu da kallo kadan sbd yasan Inayah saitayi kukan idan suka Isa daki.

Baki sake Haj umma suke kallonsa
Ya dawo da kallonsa kanta Yana sake Jin farin ciki.

Bata Bari Inayah tashiga damuwarta akan danta ba sbd tasan Babu Wanda zai taba samun matsayi irin nata a zuciya da rayuwar 'danta.

Anty juwairiyyah Kuma mamaki da tunanin zaman da Haj tace zatai a gurin 'danta takeyi Dan kuwa akwai matsala.

Haj na kishin 'danta
Inayah ma da alama batason kowa ya rabi Abbinta sbd ta taso da kaunarsa da kulawarsa akanta ita kadai Bai taba hada kaunarta da kulawarta da komaiba Dan haka a take tagano Inayah ma zatai kishin wani ya rabi Abbin nata Wanda yake mijinta yanzu duk da ba mijin ta daukaba haryanzu a Abbinta yake.

Hmmmnn""ta sauke ajiyar zuciya a fili.

Sun dade a palon sosai suna magana kafin yasamu ya nufi dakinsa.

Akwatinsa daya dawo da ita yafara ajewa closet kafin ya tube ya fada toilet.

Wanka yayi tareda alwala yafito sanyeda bathrobe fara ya nufi gaban mirror yafara tsane jikinsa.

Bawani dogon shiri yayiba yagama ya tada sallar magriba da ishai dake kansa.

Inayah kuwa suna Isa daki ta zauna kan sofa tana kokarin tsaida hawayenta,

Umma yaganah Bata zaunaba tana kallonya daga tsaye tace"

Ki nutsu Inayah kisan yanzu bamu kadai bane a gidan akwai mutane,

Mahaifiyar majeed ake magana bazance kakarkiba yanzu saidai nace uwar mijinki ce,

Bakowane shiga zakina yiba yanzu sbd Bai kamataba,
Dacan dakikeyi baa hanakiba sbd mune kadai a gidan Kuma Kinga wancan lokacin Abbinki mahaifinda ya haifeki muke mgn Amma yanzu hakan zai iya saka wani abin daban Musamman agaban hajiyarsa sbd yanzu Kam mahimmancinta yafi na kowa da komai a gunsa...

Shiru Inayah tayi Jin abinda umman tafada Kuma ya taba zuciyarta sosai dahar take sake Jin zafi da ciwon rashin zamanta jinin Abbin.

Har umma yaganah ta fice shiru take tana kokawa da 'dacin ranta na cewan yanzu akwai Wanda yafita matsayi gun Abbinta.

Hawaye taji suna neman cika idonta na kishin hakan itama,
Saidai duk matsayin hajiya agunsa batajin nata matsayin itama zai sauka sbd Abbinta ai yanzu harda mijinta ya Zama Dan haka itama matsayinta biyu akansa bazata yarda a qwace Mata matsayinta na Yar gatan Abbinta ba Kuma ai itace sanyin idaniyansa kaman yanda kowa yasani Dole itama Haj umma tayarda da itace Yar lelen Abbi.

Ranta a cunkushe ta dauki wayarta dake ringing taga sunan anty Hafsat ta dauka tana farawa da cewa"

Anty Hafsat Abbi yadawo,
Amma yanzu Haj umma ce.....

Tareta anty Hafsat tayi da cewa"

Ashe tashin hankali yaqare tunda yadawo
Kuma ya tadda hajiyarsa
Fatan dai Kun taru Kun tayasa Murna?

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa"

Eh mun Masa Murna sosai ai tun baima dawoba kinsani.
Sanyi jikinta yayi ahankali tace,

Yanzu anty Hafsat Abbi zaifi son Haj umma akaina ko?

Murmushi Anty Hafsat tayi tana tausasa murya tace"

Inayah mahaifiyarsa cefa,
Tayaya bazaifi Sonta akan kowaba?
Ai uwa ba Wasa bace,
Kema Taki uwar duk abinda tayi haka zakiyi hakuri ki rungumeta sbd itama shedan ne kawai yashiga zuciyarta bawai Dan bata sonkiba.

Banajin haushin umma Hadiza anty Hafsat Amma dai zuciyata tafi kaunar Abbi haryanzu akanta sbd bansantaba,
Bantashi da kauna ko soyayyar uwaba saita uba Wanda kaunarsa ta ginu araina shi kadai tun ina qanqanuwa,
Abbina Ni kadaice tasa Amma yanzu da hajiyarsa tadawo yafi Sonta akaina.

Kasa cigaba da magana tayi Tai sallama da Anty Hafsat din ta jefar da wayar.

Zubbi ce tai knockin tashigo dakin cikin kulawa tace"

Umma yaganah tace kifito zakuci abincin kowa yafito.

Gyada Mata Kai kawai tayi a gundure tace"

Kije am coming.

Bayan fitar zubbi Saida ta dauki mintuna tana danne damuwar zuciyarta kafin ta miqe ta nufi closet dinta ta dauko dogon wandon Burberry kawai ta saka batareda ta sauya rigaba ta fita.
##MAMUH#
##LOVE/ROMANCE/A&I

*_ZAFAFA BIYAR_*

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/7, 10:23 AM] +234 903 125 2820: *_46_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tana fitowa Kai tsaye dining room ta nufa jikinta sanyaye da sabuwar damuwar data saukar mata arai.

Da kallo suka bita data iso sbd ganin Bata sauya kayanba kawai dogon wando ta Sako ta suturta dogayen qafafuwanta dake bude a fili dazu.

Zama tayi ahankali batareda tace komaiba.

Drink din da Umma yaganah tazo dashi daga kitchen ta ajiye kan table tana cewa"

Inayah kije ki sanarda MAJEED table yazama ready.

Tanajin haka ta miqe har lokacin jikinta a sanyaye ta juya Zata tafi saiga qamshinsa yafara isowa take tasan yana hanyar shigowa ta dakata tana kallon kofar.

Reebok hoodie wears ne ajikinsa farare sai black Valentino slippers.

Fuskarsa fresh as usual kaman sabon saurayi ba damuwan komai saidai nutsuwa da sanyinsa daya Riga ya kama rayuwarsa tun barinsa gida Dan haka wannan walwalar da faran faran ba lallai yadawoba.

Inayah ya kalla da fararen idanuwansa take yagano sanyinta.

Ajiyar zuciya ya sauke a Dan takaice kafin ya kalli qafafunta yaga ba safa ga kayanta dai ba wani na arziki bane.

Da kulawa yace"

Menene Kuma yanzu kike Bata fuska?

Ba nace abar kukan hakaba?

Biyosa tayi tana sake marairaice murya tace"

Abbi ni haryanzu Banga ka yafemun bane ai to.

Da nutsuwa yace"

Saikin Dena yawan kukan Nan da Kuma Jin maganar umma yaganah.

Zama sukai a dining Haj umma na kallon 'danta tana Masa adduar kariya daga mugun Ido da mugun Baki sbd 'dan nata tubarkallah yakoma Mata tamkar ba itace ta haifesaba fes kaman Dan baqaqen larabawa.

Cikin girmamawa ya sake gaidasu Haj umma kafin suka fara cin abincin.

Inayah ta zuba Masa abincin iya yanda tasan yanaci sai gashi ko farawa baiyiba Haj umma tace"
Chapter 49 · 0% Book details