← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 65

Sashe 65

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

MTN card👇
09134848107
[11/10, 9:11 PM] +234 814 138 6337: *_58_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Cikin idon Inayah din ya kalla da qaramin bakinta Daya furta kalmar ya lumshe idanuwansa dasuka saka Inayah din sake Jin son Abbinta ya zauna Yana gaidasu Haj umma da umma yaganah kafin ya kalleta yace"

Bakin Nan baya shiru ko gaban kowa ko?

Murmushi tayi ba zato tasake cewa"

I love you Abbi.

Wannan karon wani qayataccen miskilin murmushi ne ya sauka a fuskarsa Wanda yasa umma yaganah Jin kanta gingirim
Haj umma kuwa duk qarasa rudewa tayi tana lafta shuga a tea..

Umma yaganah ce tace"

Haj umma sugan Nan bazai Miki yawaba kuwa?

Sai alokacin Inayah ta juyo ta kalli Haj umman tana murmushi tace"

Haj umma kema I love you.

Wannan karon kasa hakuri Haj umma tayi tace"

Gidanku Inayah,
MAJEED kana gani yarinyar Nan Zata maidani abokiyar wasanta ko?

Kallon Inayah yayi da idanuwansa dake kasa boye kaunarta wasu lokutan yace"

Ki bawa Haj umma hakuri Kuma ki Dena Mata rashin ji
Bana fada Miki hakanba?

Abbi da gaske nake fa ina Sonta sbd itace mamanka.

Kallon Haj umma tayi cikin kulawa tace"

Kiyi hkr Haj umma bazan sake.

Ciki ciki da murya ta amsa tana cewa"

Zaki sake nama sani
Allah dai ya kyauta yasa kugane ku duka.

Amin" Umma yaganah ta amsa tana murmushi da cewa"

Wasan Kaka da jikane take miki Haj umma Dan Bata dauki bangaren sirikaba.

Shiru Haj umma tayi tanason cewa Bata fata saidai tana shakkar yanda MAJEED ze dauka yanayin sbd tafara gano da gaske dai baya hada Inayah da komai,

'yar datayi sanadin barinka gida,
Ka rabu da uwarka da Yan uwanka da danginka da rayuwarka ta daula ka qare a yawon dako da gadi Amma memakon ka guje wannan 'yar jinta kake kaman kurjin zuciya da Baya ganuwa bare a taba.

Inayah dai yau Satan kallon Abbita takeyi sbd kyan da yayi Mata hakama duk ya diba abinci yakai bakinsa saita kalla bakin cikin wani irin shauqi tana tuno dandanon lips din nasa da zaqi harshensa cikin bakinta.

Jin idonta akansa tun dazu yasashi waiwayowa ya kalleta,
Shima bakinta ya kalla tana tauna chips ahankali ga tomato ketchup ya Bata gefen lips din nata kadan.

Tissue ya dauka tareda kallon bakin ya goge Mata batareda yasan yayiba shaf idonsa da kansa sun manta dasu Haj umma dake zaune taredasu..

Yana goge Mata ta riqe hannunsa agurin a sakalce tace"

I love you Abbi.

Duk lokacinda ta fada wannan kalmar duniyarsa gabaki daya take jijjjigawa,
Neman rasa kansa yake saiya riqe da karfi sbd komai zai iya faruwa idan tana yawan fadar wannan kalmar me yamutsaba.

Wannan karon Haj umma tafara tashi tabar gurin sbd zuciyarta bazata iya daukan ganin wannan rashin mutuncin na Inayah ba gashi Zata lalata Mata tsohon tuzurun 'da.

Umma yaganah ma tashi tayi ta tafiyarta zuwa kitchen tabar gurin.

Suna tashi Inayah ta kalli kofar dasuka fice Yana murmushi ta tashi tsaye tadawo kan cinyarsa ta zauna tana kallon fuskarsa datake Tona asirin zuciyarsa tace"

Abbi na kayi kyau yau sosai,
Nima sainayi adon dazan maka kyau Kuma saika yaba tunda Nima na yaba.

Murmushi ya sake a hankali tareda shaqar qamshinta a boye
Yace"

Meyasa zakiyi rigiman zuwa Abuja?

Sauyawa muryarsa tayi a shaqe yace"

Kiyi zamanki karki bini...

Hannuwanta ta rataya a wuyansa tareda matso da fuskarta kusa da tasa itama qasa qasa tace"

Bazan iyaba Abbi,
Zuciyata ciwo zatayita Yi idan katafi da Dr farhat..

Cikin idonta ya kalla Yana Jan boyayyan numfashi me Qamshin da dumin nata numfashin a kasalance yace"

Waye Dr farhat?

Wani irin Dadi da farin ciki maganarsa ta sakata Batasan lokacinda ta rungumesa ba tana dariyar farin ciki tace"

She's no one.

I love you Ab.......Bata qarasaba ya dago fuskarta yayi bakinta kyakkyawar kamawa da nasa sbd tundazu datake juya Masa Kai da kalmar..

Wani irin kiss yakewa bakinta Yana matseta jikinsa tana sake matsesa zuciyarta cikeda farin cikin abinda ya fada.

Itace tafara Jin motsin zubbi Dan haka ta zame bakinta tareda dagowa ta kallesa gabaki daya ya juye da alama ma ya manta Inda suke...

Murmushi ya saki tana boye dariyarta tace"

Abbina nawa Ni daya,
Kana lattin fita fa.

Murmushi dabai San dashiba ne ya zuwar Masa.

Tayar da ita zaiyi zubbi tashigo tattara gurin tagansu ahakan da sauri ya juya a rude tayo Palo Haj umma dake zaune tana gadin lokaci tace"

Makanta zakiyi Nan gaba ma indai Inayah ce,
Nema zauna ki nutsu tukuna ki koma aikinki.

Cikin ranta ta qarasa da cewa"

Tanacan tanawa bawan Allah iya shege.

Shine yafara fitowa daga dining room din Yana Dan gyara wuyan rigarsa da hannu daya data yamutsa
Dayan hannun Kuma Yana cikin na babyn nasa data riqe tanata sakin murmushin farin cikin Abbinta da maganar da yayi akan Dr farhat.

Bai lurada Haj umma ba Saida Inayah taga yanda Haj umma ta daure fuska sosai tace"

Haj umma mun fito......

Sai alokacin ya lura da Ido ya kalli Inayah da alaman"keep quite"

Shiru tayi tana sakin hannunsa ta tsaya daga Nan ya wuce ta juya zuwa dakin umma yaganah.

Acan dakin takira anty Hafsat ta sake sanar da ita maganar tafiyan da ita zaayi.

Tana Gama waya da Anty Hafsat saiga Kiran umma Hadiza yashigo wayarta.

Cikin sakewa ta dauka tana cewa"

Good morning Umman Dr.

Murmushi da dariyar farin cikin yarta data Zama free mutum ba ruwanta tayi kafin tace"

Antashi lfy Dr INAYAH A MAJEED¿
Yasu umma yaganah da Abbin naki?

Murmushi tayi tana dawowa gefen umma yaganah ta zauna tace"

Lafiyansu kalau,
Ya Dr Abdulsamad?
Oh sorry kaman a asibiti zai kwana jiya right?

Eh a can ya kwana gashi Zaki Kuma tulawa 'dan bawan Allahn yarona aiki ki gudu da Abbinki sbd gata ko tausayin 'dana bakwayi Yana aiki asibitinku.

Dariya Inayah tayi tana cewa"

Bazan dadeba Zan dawo
Kuma ai namasa waya na sanar dashi tunda ai sune manya a asibitin.

Wane time zaku wuce inason kawo sakon Anty iklimat ki wuce Mata dashi sbd idan kinje idan abbin naki ze Bari saiki Kai Mata ku gaisa tanata son ganinki kinji?

Shiru ta Dan kafin tace"

Sai Abbina idan ya yarda zanje.

Ok ganinan zuwa gidan Banda mintuna Zan kiraki saiki fito.

Ok Tom.

Suna aje wayar umma yaganah tace"

Idan ta iso tashigo Mana tunda dai ba cewa yayi kada ta Kuma shigowa gidanba,
Koba komai ai anzama Daya Dole ko baa so tunda ita sirikarsa ce itama Kuma sirikinta ne uwa uba su biyun kaman sune asalinki.

Acan Hadiza kuwa wasu kayan dataiwa Inayah siyayya tun kwanaki da Anty Hafsat tafada Mata aurenda ake tunanin Haj umma Zata saka MAJEED yaqara takeson Bata Amma tana dakatawa sbd batason batawa AA MAJEED din kokuma yaga tanason Bata Masa 'ya yasa Bata bawa Inayar ba Amma yanzu Kam Bata zatayi suje can su qarata ko zaa samu ya rage wannan kame kamen fuskar ya dawo mutum kaman kowa.

Mintuna masu Dan yawa dauka kafin ta iso gidan sbd sunada Yar tazara
Tana parking takira wayar Inayah saiga zubbi ta fito tashigo da ita har dakin umma yaganah.

Zaunawa tayi suka gaisa a sake sbd zuwa yanzu sun saba sosai Musamman kullum sai Hadizan takira umma yaganah.

Kallon Inayah dake kwance tana faman chatting take bayan sun sake gaisawa tace"

Ga sakon Anty iklimat" wata qaramar envelope ce da takarda aciki.

Karba tayi tana cewa"

Iya sakon kenan?
Na dauka Babba ne¿

No wannan dinma Babbane sbd yanada mahimmanci sosai agunta takardan Daya shafa aikinta ne.

Fira suke sama sama ita Kuma tana chatting a waya sosai suke fira Neesah akan tafiyan nata da Abbi.

Umma yaganah ce tace"

Inayah tashi ki raka ummanki taje ta gaida Haj umma Basu gaisaba
Dagacan kuje dakinki ta tayaki hada kayan tafiyar sbd idan aka biyeki sai abbin yadawo Baki hada komaiba.

Tashi tayi suka fito tareda Hadizan tana cewa"

Yanzu muna zuwa zanyi lefi agurin Haj umma.

Suna shiga kuwa dakin ta zaune kan kujera Salimat na gasa Mata qafafunta ta kallesu da mamaki bayyane kan fuskarta tace"

Baqi akai gidan kenan?

Zaunawa Hadiza tayi tana gaidata cikin girmamawa da Yar sakewa...

Inayah Kuma gadonta ta nufa Zata zauna sbd sun cike kujerun biyu dake sakin
Cikin babban sauti tace"

Maza karki haumun gado ki yamutsa kaman yanda kike mulke gadon yaganah sbd Bata Miki fada,
Zo zauna gefen mamarki karki yamutsan gado.

Kai Haj umma daga Zan Dan hau?
Baga Salimat nanba saita gyara Miki.

Banaso jeki kiyita yamutsa Wanda kika Saba na yaganah.

Miqewa Hadiza tayi suka fito tare tana dariyar Rigimar Haj umman da Inayah.

Suna Isa dakin Inayah
Hadiza tafara kallon koina dakin cikin nutsuwa da kulawa tareda mamakin zuciya irinta MAJEED,

Dakin Inayah yafi kowanne daki girma da tsaruwa tareda Jin dukiya a gidan bayan dakinsa Wanda Batasan Yaya yakeba,

Komai na Inayah a gidan da rayuwarsa is different,
Komai nata na Musamman ne sbd ya banbantata da kowa a rayuwarsa,

Meyesa yake tsananin so da kaunarta irin haka Bayan qyamatarta yakamata yayi sbd rayuwarsa data lalace sanadinta Dana uwarta.

Zama tayi kan sofa tana ajiye qaramar paper bag din hannunta me tambarin Alex Mill.

Cikin kokarin sakewa da 'yarta tace"

Ina luggage dinki?

Zubbi ta qwalawa Kira a waya tazo tace ta dauko akwati Daya acikin akwatinanta dake sama jere kan closet dinta.

Rimowa suitcase din da zubbi ta dauko Hadiza ta kalla tana kiyasta kudinsa a ranta sbd MJ Muhammed yanada irin set din cikin luggages dinsa.

Da kanta tanufi closet din Inayah din tana zaban Mata kayan dazata saka Mata a akwatin..

Kaya kalilan ta daukan Mata marasa nauyi da wahala sai tsadaddun designer kayan baccin data siyo Mata tazo dasu.
Undies de tasa Mata da yawa sbd lurada Inayahn nada tsafta sosai Dan ko undies dinta dake jere basa iya kirgiwa tun daga kan wainda aka fasa da wainda Bata taba amfani dasuba.

Tana Gama hada Mata kayan ta tsayar da akwatin gefe ta dawo ta zauna gefenta tareda karban wayar hannunta ta ajiye gefe tana cewa"

Inayah kin taba tafiya kuwa dagake se Abbinki?

Girgiza Kai tayi tana kallonta tace"

Baya zuwa damu koina koyaushe muna gida nida umma yaganah.

Numfashi umma Hadizan ta sake tareda riqo hannunta tana Mata Yan maganganu irin na uwa da 'ya.

Sun jima a dakin kafin suka fito taje tayi bankwana da Haj umma suka fito itada umma yaganah da Inayah har harabar gidan ta Shiga mota ta wuce suna shigewa Abbi na dawowa gidan.

Bai Bata lokaci ba kawai dakinsa ya nufa Kai tsaye ya shiryo yafito janyeda qaramar givenchy luggage Mai shegiyar tsada da kyau
Kai tsaye yacewa Inayah ta samesa mota sbd sun Dan Yi latti zuwa airport din.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
Chapter 65 · 0% Book details