← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 65

Sashe 47

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sudai su Haj umma mamakin duniya yagama cikasu da kallon Inayah wadda shagwabar da ita da akayi take a fili...

Budurwar yarinya likita guda Amma duka halayyarta da dabi'unta kaman wata qaramar baby.

Bata Gama cin abincinba ta miqe zatabar gurin umma yaganah ta dakatar da ita cikin kulawa tace"

Inayah Ina zaki bakici komaibafa a abincin?
Meyasa kike Wasa da cin abinci yanzu?

Shi abbin naki idan yaji bakya cin abinci aikinsan fadan dazaiyi.

Ba dazu kika Gama cewa afadawa Abbinki kin daina rashin jiba?

Dawo zauna kici abinci.

Zubbi da sauri tasake matsowa cikin kulawa tana kokarin zuba Mata wani abincin sbd wannan ya huce
Inayah din tace"

Barshi zubbi zanci wannan din ahaka.

Dawowa tayi badan tasoba ta zauna tana tura abincin.

Kasa riqe mamaki anty juwairiyyah tayi tana Satan kallon Haj umma cikin ranta tana cewa"

Akwai matsala kuwa babba Dan haj umma tazo qarshen kishin 'danta kila Dan wannan yariyar da alama tagama nisa a tabara Mai lasisi gurin MAJEED.

Koda aka gama cin abincin Saida umma yaganah tasa aka hada fruit salad takaiwa Haj umma daki da kanta harya zauna sukai Dan fira duk da bawani fuska sosai gurin Haj umma din.

Danta MAJEED kawai take buqatan yadawo ta rungumi abinta tashafa kansa ta tsiyayar da hawayenta na shakarun rashinsa dake qasan zuciyarta.

Inayah kuwa hankalinta tashi yayi sosai Dan hakan Bata taba faruwa da itaba na rashin Jin Abbi Kuma Bai sanar da itaba Ina yatafi Dan haka hankalinta yayi masifan tashi daqyar taga safiya.

Duk Wanda yake gidan tun qarfe 6 na safe ta tadasu bacci da tashin hankali harsuma duk saitasa hankalin kowa yatashi sbd kowa yakira wayarsa baya samu

Kosu Haj umma dake basuda numbernsa anbasu kowa yayita Kira baa samu.

Kuka da tashin hankali Babu wanda Inayah bata shigaba ba shiri aka nema CM suka Samar dashi.

Baiso sanar musu tafiya AA din yayiba Saida yaga yanda Inayah ta dagawa kowa hankali tukuna ya kwantar musu da hankalin tafiya majeed din yayi Kuma wayarsa da basa samu sbd layin baya Aiki acan ne.

Hankalinsu ya Dan kwanta anty juwairiyyah Saida tayita fadan yanda Inayah ta dagawa mutane hankali Batasan Haj umma nada hawan jini bane Zata kashe musu ita tunda batada asara.

Itadai Inayah batace komaiba sai Haj umman dataje tabawa hakurin daga Mata hankali datai taqara da cewa bazata sake ba.

Har dare ma still abbin bai kirasu ba haka jiki amace Inayah ta kwana,

Washe gari neesah Zata wuce Dan haka itace da kanta takaita airport tareda Safnah suka rakata ta wuce.

Daga airport gidan anty Hafsat suka wuce.

Acanma anty Hafsat rarrashinta tayi tareda Bata qwarin gwiwa akan auren a fakaici Dan kuwa suma basusan yaushe wannan auren zai Zama cikakke ga ma'auratanba Amma dai kam Zata dage gurin ganin ta ingiza Inayah tako Ina tunda baruwan Inayah din ba doguwar Noke Noke ta iyaba
Babbar matsalar da fargaban na gurin AA MAJEED Wanda kwata kwata matan ne basa gabansa bare Inayah dayakewa kallon 'yar cikinsa.

Sai yamma tadawo gida bayan umma yaganah tayita kiranta tadawo gidan hakanan.

Koda ta dawo anyi sallar magriba Dan haka daki ta wuce Kai tsaye tayi alwawala tayi sallar magriba ta zauna tana sake gwada kiransa Dana Neesah Amm duka Bata samesuba.

Ajiye wayar tayi ta nufi dakin Haj umma ta gaidata kafin ta fito ta wuce dakin umm yaganah ta taddata tana waya da Yan uwanta dake maiduguri.

Zama tayi gefenta tan saurarenta harta Gama tukuna tace"

Umma yaganah ke kisake gwada Kiran Abbi ko zaa samesa.

Bara mugani to"
Nemo numbernsa tayi tasaka Kira Amma Bata shigaba Dole suka hakura.

Fira umman kewa Inayah Mai Kama da nasiha saiga Kiran Hadiza yashigo wayat umman ta kalli Inayah tace"

Ga mahaifiyarki Nan nakirana.

Dauka tayi da sallama suka gaisa Hadizan ta tambaya ko AA MAJEED din yadawo daga tafiya umma ta sanar Mata Bai dawoba.

Inayah ta tambaya cikin sanyin murya da jiki.

Kallon Inayah umma tayi kafin tace"

Lafiyanta kalau gatanan zaune Bata nabata ki gaisa.....

Aa,aa kyaleta tunda naji lafiyartama ya Isa zanci gaba da jira har AA din yadawo kaman yanda nayi alqawari Inshallah Zan jira sai ranarda ya yafemun ya hadani da ita Dan kansa Zan tunkareta.

Tausayin Hadizan yasa umma Dan rintse Ido tana cewa"

MAJEED baida matsala Inshallah idan Anbi komai a hankali zakiga da kansa zai hadaku.

Godiya Hadiza tayi kafin sukai sallama suka aje wayar.

Inayah shiru tayi batace komaiba
Itama umman tana aje wayar batacewa Inayahn komaiba.

Tashi sukai Sakai sallar ishai suna gamawa Inayah tayi dakinta jikinta a mace tanajin wata irin damuwa da tashin hankalin rashin ji daga Abbinta.

Wanka tayi tana fitowa ta sanya D&D off-white Riga da wando masu Dan kauri Amma guntaye Dan wandon Bai Gama kaiwa gwiwarta ba Amma yanda Fadi sosai
Rigar kuwa daidai jikinta ce saidai yau tasaka condom bra.
Kanta farar qaramar wulace akanta data bayyanarda kusan Rabin gashinta dayake sauran gyaran aurenta har lokacin.

Slippersta ziro ta fito qamshinta Mai dadi Yana tashi daga jikinta ahankali.

Tun kan ta iso palon anty juwairiyyah tajiyo Dan qamshinta Dan haka ta waiwayo tana tallon hanyar kofar dakin Inayah din.

Dukkaninsu me zaune a palon har Haj umma da umma yaganah sun Dan zatawa sama sama.

Zuwansa yasa Haj umma kallonta ta dan dauke kai sbd kayan Inayah din kullum Babu na arziki tasaba da rayuwar turai da sakewa a gida ba ruwanta.

Umma yaganah data lura da yanayin haj umma da Anty juwairiyyah dakewa Inayah kallon mamaki
Saita miqe a Dan fuske ta kalli Inayah zatai Mata magana aka bude kofar palon Kai tsaye Wanda yasasu juyawa duk su dukan sbd Babu mai shigowa Kai tsaye batareda Danna doorbell ba idanba Mai gidanba dakansa.

Cikin nutsuwa kuwa yashigo sanyeda black Armani's fuskarsa fes tana daukan idon kwarjini Mai tsanani,
Take qamshinsa ya doke Wanda Inayah tacikasu dashi.

Cak kowa ya miqe suna kallonsa dukkaninsu shima cak din ya tsaya yana kallonsu.......

Inayah data Gama kallonsa cikin tsananin farin cikin ganinsa da Murna taje a guje ta fada jikinsa ta maqalqalesa da wata irin kyakkyawar rungumar datasashi dafa kofa.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/7, 10:23 AM] +234 903 125 2820: *_43_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Daga gidan Dr iklimat Hadiza sake komawa tayi gidansu hajiyar MAJEED wannan karon tana kuka tana komai Amma irin wulaqanci da tozarcin dasu anty juwairiyyah sukai Mata baisa ta hakuraba haka ta ringa zuwa rokonsu su fada Mata Inda MAJEED ya tafi da yarta.

Tun tana zuwa tana samun ganinsu har takai idan tazo Mai gadi ke yimata korar wulaqanci yana zaginta.

Daga qarshe police suka saka aka kamata daqyar tasamu Dr iklimat ta karbota bayan ta sanar dasu Hadizan nada matsalar qwaqwalwa.

Tun daga lokacin tashiga wani mawuyacin hali na ciwo da nauyi a zuciya.

Gabaki daya bata gane komai batajin komai sai kukan jaririyarta,
Kuka tuninya Dena zuwan Mata ya qafe..

Ta dan samu lokaci ahakan cikin masu aikin gidan Dr iklimat kafin Dr iklimat tafara janta ajiki Dan ta warware tafara dawowa daidai.

Da fari Al'amarin yayi wuya Amma da dr ta dage sosai Kuma lokaci yaja sai gashi tafara sakewa sbd kyautatawa Dr iklimat dataketa dawainiya da ita.

Itama aikin ta dauketa cikin gidan na abinci data iya.

Ganin qwarewarta a iya abinci yasa Dr iklimat ta maidata restaurant dinta sbd taga qaruwar da zatai da Hadizan.

Dayake tasaba aikin restaurant sai Bata wani Sha wuyaba tasaba da aikinta sbd Sam yanzu Babu wani digon farin ciki ko daya a rayuwarta,
Zuciyarta rufe take ruf da tarin baqin ciki da damuwa Amma a fili tana iya kokarinta gurin mu'amala me kyau da mutane.

Dr biyanta albashinta takeyi Mai kyau ba gayya Kuma kullum ta gamo aiki a can da daddare gidanta take dawowa ta kwana Saida sassafe ta koma.

Ahaka yayi fiyeda shekara daya a tareda Dr wadda Takoma tamkar wata babbar yayarta sbd sabo da kulawa,

Fes Takoma tayi fresh abinta sbd nutsuwa da cigaban data samu sosai.

Ana hakan abokin babban yayan Dr wani soldier yaganta yayi shaawan aurenta sbd yafi shaawan auren macenda batada kowa ganin yakeyi tafi maka biyayya hakama Zata riqeka amatsayin kowa nata tabika duk Inda kakeda ra'ayin juyata ko kaita.

Dr iklimat tana duba ribar da Zata samu a komai na rayuwa Dan haka MJ Muhammed na bayyanarda buqatansa na auren Hadiza tasan cigabansu sbd yanada arzikinsa sosai saidai yawan auri saki Amma yanzu kila ya daina tunda ya samu irin wadda yakeso wadda bazata iya Musa Masa komaiba sbd batada kowa.

Hadiza batada ra'ayi ko shaawan aure yanzu ko kadan aranta Dan haka Bata boyewa Dr iklimat ba ya fada mata batada ra'ayi.

Dr batai qasa a gwiwa ba ta ringa lallaba Hadizan tana cusa mata ra'ayin da auren kawai Zata samu sukuni da nutsuwata rayuwa tareda komawa cikin 'yan uwanta dasuka gujeta,

Aure ne kadai rufin asirinta Kuma shine zai Bata Daman sakin kudi ta nema majeed da 'yarta duk duniyar daya gudan Mata da 'ya.

Zancen Ayshatouh da Dr tasaka yayi tasirin sauya Mata raayi Akan yin auren.

Ba bata lokaci kuwa Dr tafara karban kudi sosai gurin MJ Muhammed aka fara gyaran Hadiza daman gata da sauran kuruciyanta.

Gaggawa Dr iklimat tasaka akan auren Wanda yasa Hadizan kejin damuwa Amma Kuma bazata iya fasawaba tunda tabbas batada qarfin dazata nema 'yarta sai tana tareda Mai qarfi.

Batada ra'ayin komawa gida Amma Dr iklimat ta dage akan suje gidan a daidaita Yan uwanta su daura Mata auren da kansu sbd kaucewa wata fitinar gaba.

Bayan ankai ruwa Rana itada Dr da Yan uwanta suka karbeta Bayan sun tabbatarda Mai kudine sosai Wanda zata aura.

Tunda Hadiza tadawo gida Babu Wanda ya tambayi Inda yarta takeba sai Inna wadda take fushi sosai dasu kabiru tun Bayan barin Hadiza gidan.

Ita kanta hadiza Bayan dawowar tata bayan gaisuwa Babu abinda yake hadata da Yan uwanta da matansu da 'yayansu,
Chapter 47 · 0% Book details