← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 65

Sashe 50

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Majeed ko abinci bakaci sosai kenan yanzu?

Murmushi yasake ahankali Yana diban brown rice din yakai bakinsa yace"

Kusan komaiba ya canja umma ai.

Murmushi tayi itama tana cewa"

Duk da hakan Bai kamata kana Wasa da abincinba duk busy din dazaka Zama kuwa,

Yaganah haka kuna kallo yake Wasa da abinci?

Wani rolling da Ido Inayah tayi cikeda mamakin zancen hajiyan tace"

Abbi da daddare ne bayacin abinci sosai Amma ba ranarda Zan bar Abbina da yunwa tun dama can....

Dangwalar cinyarta umma yaganah tayi alaman tayi shiru Amma hakan kawai takejin bazata Bari Haj umma ta nuna tafiya son Abbinta ba.

Cikin nutsuwa da kulawa Abbi yace"

Keep quiet Inayah.

Ba abinci kike ciba har kike tsayawa zance.

Bakin nata ne ai Ni Naga gabaki daya kaman bakwa kwabarta,

Kaida yaganah Kun taru Kun sangartata qatuwar budurwa kaman wannan da ta Isa ace tuni tana gidan miji Amma tana zaune ka Gama tabarar da ita magana daya biyu sai kuka,
Wannan ma banajin likitar gaske ce Dan ko kanta Bata Gama saniba bare marasa lafiya.

Shiru dukkaninsu sukayi suna sauraron jininin hajiyar wadda sangartar Inayah tafara isarta Dan kaman MAJEED din yagama shiriricewa akan 'yar Sam Baya wani tsawatarta.

Inayah kuwa raurau tayi da Ido tareda kallon Abbin zatai magana da fararen idanuwansa yayi Mata alaman tayi shiru kartayi magana.

Hadiye maganarta tayi tareda kokarin miqewa Zata tafi sbd abincinma ya isheta Dan dama Bata wani Jin yunwa sbd ranta dake cunkushe.

Come back here Inayah,
Ina zaki?
Kinfara Wasa da abinci ko?
Zauna kici banason wannan shirmen naki,
Haka Zaki ringa fushi da abinci idan anmiki fada?
Zauna banason Jin komai agurin.

Dawowa tayi ta zauna tareda fara cin abincin batareda tace komaiba saidai ranta yayi sanyi da Abbinta ya nuna haryanzu kulawansa akanta yana Nan fiyeda komai.

Murmushi tafara sbd takasa boye farin cikin hakan ta dago tana kallonsu Haj umma dakecin abincin cikin mamakin majeed Amma dai batace komaiba.

Anty juwairiyyah kuwa cewa tayi"

Zaa fara kenan¿
Dan kuwa ita dama wuri Zata wuce bazata zaunaba taga alaman MAJEED din yanzu yafi qarfin reni duk da Yana qaninsu,

Dukiya kuwa idan akace a miqa Masa gadonsa arzikinma yawa zai Masa Dan duk tarin gadonsa ba komai bane akan tasa dukiyar daya tara da guminsa saidai abin takaici da baqin ciki kusan duk yawancin dukiyar sunan Inayah ne akai,

wannan Inayah dai tazamar musu qarfen maqoshi tun ba'aje koinaba.

Koda aka Gama cin abincin Abbi na miqewa ta miqe ta goge Baki da tissue ta bisa zuwa palonsa kaman yanda suka Saba kafin taje ta kwanta.

Suna Isa palonsa ya zauna tareda daukan remote ya kunna tv
Ta qaraso ta zauna gefensa tana cewa"

Abbi bakace ka yafemunba?

Waiwayowa yayi kalleta dakyau ganin harda Rama tayi duk tabi ta Hana kanta nutsuwa kwana biyu cikin kulawa yace"

Tunda kince kindaina shikenan na yafe lefin Amma yanzu tunda umma tana Nan zakina Kama wannan bakin naki karki yarda naji kina Mata maganganun dakikeyi gaban umma yaganah sbd ummana Bata daukan shirme.

Kinji,right?

Gyada Masa Kai tayi ahankali tareda cewa"

Anan Zata zauna taredamu daga yanzu?

Gyada Mata Kai yayi ahankali idonsa na kan tv.

Turarenta ne yaketa son damunsa sbd kansa na Dan ciwon gajiyan tafiya Dan haka ya juyo yace"

Ok kije kije kiyiwa ummana Saida safe kije kiyiwa ummana yaganah ki wuce ki kwanta gobe Zaki koma aikinki.

Bata Masa wani musu Dan haka ta miqe tareda yimasa saida safe ta wuce dakin Haj umma Tai mata Saida safe ta wuce gurin umma yaganah tasake rage darenta acan kafin ta wuce bedroom dinta tana shiga ta zare dogon wandon data saka ta nufi toilet tayo brush da sauran abinda zatai ta fito ta kwanta.

Washe gari tun bayan sallar asuba data koma ta kwanta Bata farkaba sai 9 na safiyar,

Wanka tafara Yi ta shirya tafito sanyeda dark green fitted jallabiya da qaramin black veil nade akanta sai handbag da wedges takalmin Chanel.

Fuskarta ba make sbd Bai wani dameta Amma sai tasaka eyeliner da lipbalm
Shikam qamshi ba'a ma maganarsa Dan kuwa Sam ta manta da cewan aurene yanzu akanta saka Turaren haramun ne gareta idan Zata fita.

Tana fitowa Palo Kai tsaye hanyar palon Abbinta ta nufa duk da tasan lokacin Yana wuya idan ba bacci yakeyi ba idan har ba fita yayiba to a irin wannan lokacin bacci yake komawa bayan yayi geamin.

Baya Palo Yana bedroom dinsa Dan hakanta juya ta fito tana waya da Neesah data Isa gida lfy.

Dakin Haj umma taje ta gaidata da Anty juwairiyyah wadda har lokacin Bata wani sakar Mata fuska sbd ganin taqi zuwa daki ta rufe kanta tayita kuka ita uwarta ta yarda ita ta gudu Wanda ita Kam Sam bataga abin Kuma garetaba Dan hakan yafaru sbd Allah Bai bari ta tagayyaraba,

Allah yakawo uban daya Zama gatanta fiyeda masu uwa da uban Dan haka bazataiwa Allah butulciba tayita kukan akan hakan Dan ita Sam lamarin Bai wani damu zuciyarta ba babban abinda zai damu zuciyarta shine abinda zaisa ace zaa rabata da Abbi Takoma hannun uwarta wadda har lokacin takasa Jin shauqin dawowarta gareta,

Ta jima tana fatan ganin uwar data haifeta saidai Bata taba tunanin ta hakan uwar Zata bayyana garetaba Dan a tunaninta Abbi da koma wace uwar tata suka haifeta.

Tea Tasha sai plantains da kwai ta goge bakinta ta fito da key din motarta a hannu ta fada mota ta fice zuwa asibiti.

Tana parking motar Dr Abdul na parking gefen tata.

Fitowa tayi Tata motar riqeda Jakarta da Lcoat dinta a hannu tana kallon motarsa.

cikeda mamaki take kallon Dr Abdul daya fito motar shirye tsaf kaman bashiba Amma yayi Rama sosai wadda take bayyanarda quncin da zuciyarsa take ciki har lokacin
shima Kuma yau din yadawo aiki...

Kallon kallo sukai kowanne yarasa abinda zai fara cewa Dan uwansa..

Umma Hadiza ce tafito daga cikin motar daga bangaren drivern motar da alama itace takawo Dr abdul din aiki.

Kallon umma Hadiza din takeyi sosai idanuwanta a sanyaye harma da jikinta da yayi sanyi da ganinsu lokaci daya.

Mahaifiyarta,uwarta data haifeta itace wannan agabanta Kuma itace ta Haifa Dr Abdul dinta.

Maida kallonta tayi kan Dr Abdul din dashima ita yake kallo tuni.

Ahankali ta bude Baki murya a sanyaye da nutsuwa tacewa Umma Hadiza"

Good morning.

Hadiza dakejin kaman ta janyo Inayah ta rungume cikin jikinta ta qanqame taji dumin yarta
daqyar ta bude Baki kwadayin Jin yarta ajikinta a fili tace"

Inayah kin tashi lfy?
Ya kike?
Ya umma yaganah?

Lafiya kalau" ta amsa a takaice sbd Batasan me zataceba.

Dr Abdulsamad ta kalla a hankali ta furta Masa gaisuwar shima.

Kasa amsawa yayi Saida umma Hadiza tayi saurin tabasa tana cewa"

Abdulsamad karkayi haka
Shedan ne zaiyi Wasa da tunaninka yakaika ga aikin kunya da danasani,

Inayah Yar uwarkace anyita maimaita maka Dan haka yimata kallonda ya fita Sharia zai kaika ga hanyar 'batane.

Inayah najin haka ta juya ta silale ta wuce tabarsu agurin tanajin wani iri na gata ga mahaifiyarta da Dan uwanta Amma ba a yanayi na dokin junaba da maraba da juna.

Bata sake ganin Dr Abdul dinba harta tashi aiki sbd Bai nemetaba itama batasan yaya zasu iya tsayawa su fuskanci junaba kaman da Dole sai zuwa gaba idan kowannensu yasamu ya Gama rungumar wannan Al'amarin tukuna.

Sai 3 tadawo gida a gajiye Dan haka kaman yanda ta saba Bata Shiga da kayan data dawo asibiti dasu dakinta Musamman idan tayi aiki sosai a ranar.

Kai tsaye hanyar gefen kitchen dazai kaita dakinsu zubbi ta tsaye ta zare nadin kanta tareda bawa zubbi Jakarta da takalmi takai Mata daki ita Kuma ta tsaya ta zare doguwar rigarta agurin Takoma daga ita sai dogon skin tight dake jikinta black da black singlet data kwanta jikinta dakyau.

Kitchen tashiga tana amsa gaisuwar Salimat suna Dan fira sama sama ta wanke hannuwanta ta dauki ruwan roba ta fito tana Sha ta nufi dakin umma yaganah suka gaisa ta fito Zata wuce dakinta saikuma ta juya ta nufi dakin Haj umma itama ta gaidata kafin ta shige.

Kai tsaye dakin ta shigo tana rufe robar sauran ruwan datasha.

Abbi da Haj umma da Anty juwairiyyah ne suka juyo dukkaninsu atare suna kallonta.

Ba damuwar komai tace"

Haj umma Ina wuni?
Ya jiki jiki?

Anty juwairiyyah Ina wuni?

Tare suka amsa kadaran kadahan.

Gun Abbinta ta maida kallonta tareda sakin qayataccen murmushin farin cikin ganinsa tayo gurinsa Kai tsaye tana cewa"

Abbi kana gida ashe yau.

Da sauri Haj umma ke kallonta ganin da gaske gurinsa ta nufo din da shegun kayan dake jikinta Wanda zallan shape dinta suke bayyane Musamman shafaffen cikinta dayasa kirjinta dake cikin push-up bra fitowa dakyau.

Abbin kuwa Jin yayi kunyar ummansa ta kamasa da sauri ya miqe sbd fita da Inayah din saidai Yana miqewa tana qarasowa ba damar dakatawa sbd tariga ta qaraso ba tsammani kirjinsu ya hadu.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
#AA/AYSHATOUH INAYAH.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/7, 10:23 AM] +234 903 125 2820: *_47_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Firfito da idanuwa Haj umma tayi tana dauke kanta daga kallonsu batareda tasan tayi hakan sbd rudewa.

Anty juwairiyyah ma dauke kan tayi tana shafawa Al'amarin Inayah Ido Kuma daga Nan.

MAJEED Daya riqe balance dinsa da kyau sbd kiris yarage su Fadi har ita
cikin yanayi na kokarin daidaita kansa da 'dan fada a shaqe yace"

Inayahhh,,,me ke damunki ne?
Ki nutsu mana...

Matsar da ita yayi daga jikinsa batareda ya kalli kowaba yaja hannunta suka fice dakin.

Itama kasa cewa komai tayi sbd Batasan yariga ya tasoba kodata iso idonta nakan Neman Inda Zata ajiye robar ruwan hannunta Dan haka ba zato tajisa ya miqe Bayan tariga ta iso dad dashi.

Suna fitowa Palo su zubbi dake gyaran yamma da sauri suka sauke Kai qasa daga kallonsu.

Umma yaganah data fito lokacin taci Karo dasu Yana gaf da shigewa da ita dakinta tabisu da Ido cikeda mamaki sbd ita kanta Batasan Yana gidaba alokacin.
Chapter 50 · 0% Book details