Sashe 24
Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana gamawa ta nufi dakin umma yaganah acan tayi kwanciyarta tana chatting sama sama saiga su Mimi sun taho gidan dukkaninsu yiwa Abbi barka da zuwa aikuwa take gida ya kaure da hayaniya.
Mimi harda tsarabar wasu kayan atampopin tayiwa Inayah aikuwa umma ta gode Mata sosai itama Inayah din tanajin dadin kayan Dan haka ta gode mata.
Dakinta suka koma itada Safnah suna firarsu ta matasan 'yan mata,
Fira suke akan anty Hafsat da Bata isoba sun biya sun ajeta gidan yayar mijin qanwarta dasuke tsananin mutunci sosai, daga can zaa kawota Nan din.
Saida suka gama cin abincin Rana kusan karfe biyu da mintuna kafin Anty Hafsat ta iso gidan.
Da farin cikin ganin siyama Inayah tarbota tun daga harabar gidan.
Faruk Ismail shine Wanda yakawo anth Hafsat daga gidansu.
Kallo daya yayiwa Inayah yaji Tai Masa sbd shima tunda yayo karatu a Malaysia yadawo yakasa ganin macen datai Masa gashi dama iyeyensa sun takurasa akan aure.
Ganin dayayiwa Inayah da yanayin gidan nasu yasa Kai tsaye ya 'dan fahimci wayayyu ne jama'ar gidan,
Da alama sun danyi nasu yawon bude Ido wata qasar.
Inayah gabaki daya batama wani lura dashiba sbd hankalinta dake anty Hafsat da Siyama tana murmushi dukkanin kyanta na Kuma bayyana.
Anty Hafsat ce ta juyo ta kallesa tana cewa"
Ok faruk nagode sosai
Ka Isa gida lafiya.
Gyada Kai kawai yayi tareda tada motarsa yabar harabar gidan ya fice Yana ayyanawa aransa shikam yaga matar aure irin class dinsa dayakeso.
Inayah kam Anata bangaren ko kula batai dashiba Dan a daukarta driver nema yakawo antyn.
A gidan suka wuni Anata fira da hayaniya sai yamma da Abbin yadawo aka kaisu palonsa suka gaisa a matuqar mutunce da girmamawa.
Sai dare suka tafi bayan Abbi yayi musu kyautar kudi na Musamman ga Yara.
Inayah Jin tayi kaman kada su tafi sbd yanzu da qarfi da yaji tafara sabo da rayuwar hayaniya Dan duk Wanda zai Yi rayuwa a Lagos dolensa ya koya daukan hayaniya duk da sukam anguwarsu batada abinda ya hadata da hayaniyar ko hayaniyar ma Kai securities basa Bari magana suke maka sbd gudun shiga haqqin wasu.
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
*_22_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Lokaci ya tafi sosai dan tuni maganar aurenta da Faruk ta Gama kammaluwa aka saka lokacin biki hankalinta Dana faruk din ya kwanta sbd wata irin soyayya ce sukeyi Mai zurfi da qulafucin juna.
Shi kansa Abbin hankalinsa yafi kwantawa sosai da aurenta da Faruk akan can baya da Zaid.
Ba maganar komawarsu Australia saidai idan sunje hutu saikuma Abbin da shikam zai ringa zuwa akai akai sbd huldodinsa wasu dasuke can.
Daga Nan gidansu har familynsu Anty Hafsat da dangin CM Babu Wanda baya cikin farin ciki da murnar wannan biki sai Mimi wadda baqin cikin datake ciki ya hanata sukuni sbd bazata iya kallo Hafsat tasamu shiga jikin zuriar AA MAJEED ba fiyeda ita Dan kuwa ko yanzu akan wannan auren ba qananan arziki taketa samuba daga AA MAJEED harma da umma yaganah datake Jin Hafsat tagama Mata komai tunda tayi sanadinda Inayarsu tasamu kamilallan miji dayake sonta sosai.
Safnah kuwa Bata wani damu da damuwar da Mimin take cikiba sbd tadauka kishi ne irin Wanda Allah ya halitta a zuciyar Mata shine takeyiwa Anty Hafsat na ganin tasamu shiga a Inda itace taso tasamu shigar.
Neesah kam Dole da qarfi da yaji tazo Nigeria tareda momy Dan haka Murna a gidan takuma Zama sabuwa.
Ta bangaren Dr Abdul son Inayah Bai taba raguwa acikin ransaba saima Jin dayake kaman zuciyarsa bazata iya daukaba ganin Inayah ta aura wani tabarsa,
Amma iliminsa na addini Dana bokon daya kedashi Bai barsa ya qullata komaiba saima nesa nesa daya Dan farayi da Inayah sbd zuciyarsa bazata iya cigaba da daukan kishinta Mai tsananin gaske dayake ji Amma Inayah Bata iya nesa dashi sbd yariga yazama tamkar wani babban bangare na rayuwarta a Nigeria,
Tayi sabo da shaquwa Mai tsananin gaske dashi da har kaunarsa ta ginu a ranta amatsayin aboki Kuma Dan uwan Dan haka idan yaqi kiranta itace da kanta take kiransa.
*****Bikinta Saura sati uku Dr Abdul yabar Lagos yakoma Adamawa
Farko hankalin Inayah din yatashi sosai da barinsa Amma hidima da shaanin biki yaqi barinta maida hankali sosai kan tafiyar tasa
Sai kawai tabarshi akan idan angama bikin Zatai magana dashi.
Anfara gyaran Amarya INAYAH tako Ina,
Umma yaganah baji ba gani ta dauko masu gyara daga maiduguri ana gyaran Inayah ta ciki da waje.
Anty Hafsat ma ba Zama kusan kullum saitaxo gidan da nata kayan gyaran.
Neesah dai kam tana gidan sbd suna sauka Abuja can gidan iyayen momy kwana biyu kawai tayi ta biyo jirgi zuwa Lagos Dan haka duk sauran shirye shiryensu tare suke yinsu
Ko Safnah ma kusan kullum gidan take wuni.
Umma yaganah taje maiduguri kusan kwananta biyar acan daqyar daqyar ta iya samun wasu daga cikin 'yan uwanta Amma sauran kam duk sun rasu wasu Kuma ba'a San Inda sukeba kaman ita.
Wainda ta sama cikin Yan uwan nata bama irin Yan uwan kusa bane
Kawun malam mijinta ne da iyalansa ta samu sunkoma kauyensu da aka watse sai wasu daga cikin amininan iyayenta saikuma kishiyar mahaifiyarta da itama ta tsufa sosai.
Tayi musu Sha Tara ta arziki tabaro tadawo maiduguri tasake kwana daya tabi jirgi Takoma Lagos.
*****A daren da zaa saka amarya lalle saqon wani mugun labarin ya isowa umma yaganah ta hanyar Mimi.
Rigimace ta barke a gidansu faruk da iyayensa da shi harma da mahaifin dadynsa..
Wannan wata babbar maganace data girgiza umma da ita kanta Inayah sbd basu taba tsintar wannan mumunar kalmarba sai ranar.
AA MAJEED ya Haifa Inayah bada aureba,
'yar gaba da fatiha ce...
Tashin hankali Mai girman gaske umma yaganah da Neesah suka Shiga sbd kalmar tayi Muni da yawa.
Inayah kuwa zuciyarta ce taji tana harbawa da sauri da qarfi
Wani irin zufane masu dumi suka ringa tsatsafo Mata.
Dafa kujera tayi ahankali ta zauna tana Jan numfashi da sauri sauri.
Ruwa zubbi taje da gudu takawo tabawa Neesah dake Kiran sunanta da Dan qarfi tana cewa"
Inayah karki daga hankalinki please
Wannan labari ne fa kawai aka kawo.
Karban ruwan tayi takai bakinta da Dan sauri ta kwankwada ta miqawa zubbi cup din tana miqewa tsaye tace"
Faruk yasan wannan zancen shirme ne,
Ina ruwansu data yanda mahaifina ya haifeni,
Idanma Ni shigeyarce an haramta auren shegu ne?
Tunda Ina tareda mahaifi ai banajin zan karba suna kokuma bin layin shegu..
Umma yaganah ma cikin damuwa da tashin hankalin datake dannewa tace"
Menene Kuma na wannan zancen ma Kuma yanzu?
Yarinya da ubanta Dan Allah bamason janye janye da wulaqanci,
Waye yafara kawo wannan zancen?
Wane Mara hankalin ne zai kawo Mana fitina muna shaaninmu cikin Jin Dadi da farin ciki?
Kuka sosai anty Hafsat keyi agaban Umma yaganah din sbd batama San Mimi tafara kawo musu zancen basu yardaba sai yanzu datazo da kanta sbd Al'amarin ya tsananta acan familyn Anata rigima da tashin hankali,
Mahaifiyar faruk da mahaifiyar dadynsa sunyi rantsuwar bazaai aurenba Dan faruk bazai aura Inayah ba sai mahaifinta ya sanar dasu Gaskiar wannan zancen da aka kawo musu.
Dadyn Faruk yasan saidai afasa auren har abada Amma AA MAJEED bazai zauna yiwa kowa bayaniba Dan a aura 'yarsa
Kai tsayema za'a samu babbar matsala dashi Dan kuwa suna shegenta Masa 'ya ne Kai tsaye da kalamansu.
Shi kansa Alhaji baba kakan faruk din Bai wani goyi bayan faruk da mahaifinsaba sbd ganin kaman harda kwadayin suna da arzikin AA MAJEED sukeson rufe Ido su hada zuria dashi koda da gaske Inayah din 'yar gaban fatiha ce.
Dayake maganar a tsakanin mata tafara har lokacin Abbi baisan abinda yake faruwaba dagashi har CM Dan haka su sun Riga sun Gama rabawa jama'arsu katikan daurin aure da invitations na special lunch da zaai bayan daurin auren sbd abokanan huldodinsu Christians da turawan dake Nan tunda su ba daurin aure suke zuwaba.
Wasa Wasa saiga zance dai yazama Babba Dan kuwa Dadyn Faruk yasamu CM da zancen har gida sbd bazai iya tunkarar AA MAJEED ba,
Ko daya girma MAJEED sosai yanajin kunya da nauyinsa yaje Masa da maganar Dan haka yasamu CM da zancen.
Sosai cm ya girgiza da wannan mugun sakon, dan haka baiyi saurin isarda sakonba saiya samu Alhaji baba dasu hajiyar yayi kokarin fahimtar dasu illar abinda zaayi din Dan tamkar tozarcine Kuma wulaqanci ga AA MAJEED da 'yarsa ace zaa tambayesa yanda ya Haifa yarsa.
Sam kasa fahimtar juna sukai dasu dashi Dan haka baida wani zabi sai sanarda AA MAJEED halinda ake ciki.
Shiru yayi bayan yagama sauraron bayanin CM cikin nutsuwa.
Bai bayyanarda bacin Rai ko fushiba saidai kam idanuwansa wannan karon sun bayyanarda tsananin 'dacin daya Kama zuciyarsa.
Ba'a taba cin fuska ko cin mutuncin Martabarsaba sai wannan karon,
Ko alokacinda yake talakansa baida girma ko qima a idon mutane tunda shi talakane baa ci zarafin mutuncinsa kaman wannan lokacinba.
Idanuwansa ya Dan juyo ahankali ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya Nemo numbern umma yaganah ya saka Kira.
Zaune suke gabaki daya gidan yanzu Murna na Neman komawa ciki tunda wannan muguwar magana ta bayyana.
Tashin hankalin da Faruk yake cikine ya tabbatarwa dasu Inayah Al'amarin ya girmama,
Babban tsoro da fargaba tareda tashin hankalinsu shine idan zancen yaje gaban Abbi yanda zai karbesa.
Sbd farin cikin Inayah sunsan zai iya komai hakama sunsan bazai taba bawa Wainda suka shegantata suka alqantata da 'yar gaban fatiha aurentaba,
Zancen na zuwa gabansa sunsan maganar bawa su faruk aurenta Kuma ta mutu saidai wani ikon na ubangiji.
Hakan yasa Kiran abbin na shigowa wayar umma yaganah duk jikinsu yakuma sanyi sbd sunsan cm na gidan tun dazu suna magana.
A natse ta dauka tareda sallama a sanyaye tace'"
Naam ABDULMAJEED.
Umma kuzo Palo akwai sako.
Ina Inayah?
Gatanan kwance tana fama da Dan ciwon Kai ne.
Kizo harda ita din.