← Book details Inayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 65

Sashe 54

Inayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haj umma itama sosai ta saki fuska suka gaisa da Dr farhat din Dan yanda Dr farhat ta ringa gaidata cikin Jin kunya da girmamawa sosai yasa taga mutuncin Dr farhat din sosai.

Bayan tafiyar Dr umma yaganah itama wucewa tayi dakinta ta kwanta.

Har Inayah tayi bacci cikin sanyi tana Jin damuwar rashin ganin Abbi.

Da safe haka taqi fita aiki da wuri Saida tayi breakfast da kowa.

A dining tana zuwa da Abbi tafara hada Ido Yana zaune cikin Navy blue Ralph Lauren suit dasukai masifar yimasa kyau tareda fidda hasken lafiyayyar fatarsa dake cikin hutu.

Gabaki daya Qamshinsa ya hadu Dana English breakfast din dake jere a dining ya sauya gurin.

Cikin nutsuwa da kulawa da sanyin murya tace"

Good morning Abbi.

Idanuwanta ya kalla kafin ya dauke idonsa akai anatse Yana cewa"

Morning,
Yaya jikinki?

Complain zatayi umma yaganah ta katseta da cewa"

Yaya jikin Inayah?

Naji sauki umma,
Haj umma Ina kwana?
Umma yaganah good morning.

Zaunawa tayi tana kokarin fara cin abinci Haj umma tace"

Yaya kan?
Yayi sauki ko?

Eh naji sauki alhmdllh.

Fara cin toasted bread tayi tana daukan tea tafarasha.

Itace tafara gamawa ta miqe ta Zata fice Abbinta yace tajira zai ajeta asibitin.
##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/8, 9:46 AM] +234 703 262 0576: *_50_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ringing biyu wayar tayi anty Hafsat ta dauka tana cewa"

Dr Inayah majeed Yar gatan Abbinta Kuma amaryar Abbinta.."" ta qarasa zancen da Yar dariya.

Sanyi jikin Inayah yayi tana Jin dadin kirarin Amma Kuma duk wannan yanason kauduwa.

A sanyaye tace"

Anty Hafsat Yaya gida?
Ina my sweet Siyama?

Lfy kalau Inayah,
Ya kike?
Yasu umma yaganah da hajiya?
Ya abbin naki Kuma?

Bata tsaya amsa gaisuwar yasu umma ba tace"

Anty Hafsat Abbina ya canja sosai zuwan Haj umma
Kuma umma yaganah ta Hana nayi magana
Ni gaba daya Abbina yafara Zama kaman na nawaba.

Umman Dr Abdul tace na sauya bangaren Mata
Ni banganeba Anty Hafsat kizo gidan kigan yanda muke yanzu duk ba Dadi,

Ga Haj umma komai nayi saitace shiriritata da shirme kawai na iya.

Yanzu itace Mai kulawa da Abbi fa,
Umma yaganah ma yanzu Takoma Yar kallo abinci kawai take Masa.

Nidai anty Hafsat wlh bazan iyaba
Ina kallo Abbina ya Dena ji Dani kaman da
Bayan umman Abdul tace kamata yayi matsayina ya ninku tunda matsayina biyu agurinsa.

Numfashi anty Hafsat ta sauke tana jinjina zantukan Dan duk da kusan a shagwabe da damuwa Inayah ke fadan zancen idan ta fahimta Haj umma batai na'am ba haryanzu da Inayah a rayuwar AA MAJEED barema ta dauki auren da mahimmanci.

Wani numfashi takuma sakewa tana ajiye ruwan data kawowa CM ta juya ta fice daga palonsu zuwa dakinta Dan bazataso yaji zancen nasuba.

Tana Shiga daki ta zauna bakin gado tana cewa"

To kodai kina Mata abinda baimata bane Inayah?

A sanyaye tace"

Wlh anty Hafsat bana Mata komai
Kuma Ni bandamu data kaunaceniba
Nidai Abbina nakeson ya koma yanda yake kada ya rage ji dani.

Inayah duk wannan abin na tabbata Koda qwayar zarra kaunarki da matsayinki a zuciyar Abbinki Bata raguba
Bama Zata taba raguwaba qaruwa zatayi sbd har Koda yaushe kece kaman strength dinsa.

Kawai dai inaga aurenku ne Bata aminta dashiba sbd ganin kaman bazaki iya kalawa da AA MAJEED dinba kinyi qanqanta....

Aikuwa wlh Ni inason auren yanzu bazaa rabani da Abbi ba,
Ko shima Ni Zan fada Masa inason aurena bazan rabu dashiba.

Da mamaki anty Hafsat tace"

Yanzu Kuma kinason auren kenan?
To kinason auren yanzu harzaki tsaya kina kallo auren na Neman fara rawan tun baigama tsayuwa ba,

Wannan rashin amintar da Haj umma tayi kome zai iya faruwa
Dan kuwa ko auren be rabuba MAJEED Kam zai iya samun matar dazata kular Mata dashi....

Wani mummunan faduwa gaban Inayah yayi ta tashi zaune ahankali dakyau tana cewa"

Sai tasashi yayi wani auren anty Hafsat?
Shima abbin sai yayi wani auren?

Wani mugun sanyi taji Yana shiga qafafunta tayi shiru tana jiran amsar anty Hafsat wadda taji rashin kamatan yin zancen da Inayah Dan haka ta Dan gyara murya cikin nutsuwa da kulawa da rarrashi tace"

Idan kika tsaya shirme nake fada Miki hakan kila zai iya faruwa,
Dan haka yanzu ki nutsu kema ki ringa kulawa da Abbin kaman matarsa sbd wannan right dinki ne dake Zaki bawa kanki.

Kasa cewa komai tayi sbd jikinta daya Gama mutuwa da wani irin tsoro dan kuwa tana fama da zuciyarta akan Haj umma idan Abbi ya auro wata Batasan ya Zata iya dauka.

Ganin ta Dena gane abinda take fada yasa Anty Hafsat yimata sallama da cewan Zata shigo gobe Inshallah.

Aje wayar tayi hannuwanta na Dan rawar data kasa gane Kota menene.

Kasa qarasa cin abincinta tayi ta miqe tareda daukan tray din ta fita zuwa kitchen.

Tana ajiye kayan data kawo kitchen kasa juyawa tayi ta tsaya agurin tana shiga tunani
Ita gabaki daya kanta ma ya toshe takasa gane komai,

Ita Abbinta kawai takeso ita kadai.

Juyawa tayi ta fito tana kokarin Isa hanyar bedroom dinta taji Qamshin Boadicea ta dakata sbd tasan Abbinta ne yadawo.

Juyowa tayi tadawo palon daidai Yana shigowa sanyeda kaftan
Navy blue best kalar dayafi amfani da ita.

Ganinsa yasa idanuwanta cikowa da hawaye tanajin wani irin nauyi a zuciyarta da abinda anty Hafsat ta fada dazu.

Kallonta ya qaraso yanayi zuciyarsa na tabuwa da kallonda take Masa idanuwanta da Hawaye Wanda yasan na kewansa ne.

Ahankali ya bude Baki zaiyi magana ta fada jikinsa ta qanqamesa tana sako hawayenta.

Shiru yayi Yana kokarin daidaita kansa sbd ba zatan datai Masa.

Qamshin Turarenta na black opium ya shiga hancinsa da kyau
Take yaji kansa ya Sara ya bude idanuwansa akanta tareda daga hannuwansa zai zareta daga jikinsa Amma ta ture hannunsa tana sake shigewa jikinsa hawayenta na sake gudu zuciyarta na bugawa da zancen anty Hafsat har lokacin.

Maqoshinsa yaji Yana Neman bushewa sbd yanayin yayi Masa nauyi Musamman Haj umma ko umma yaganah wani zai iya samunsu ahakan.

Numfashi ya sauke ahankali tareda Dan nutsuwa cikin kulawa yace"

Me kikeyi Inayah?
Lafiya?
Akwai abinda ke damunkine?
Taso naji matsalar...

Girgiza Kai tayi tana qin sakinsa tace"

Abbi Dan Allah karka rabu Dani Ni inason auren....

Wani irin duka zancenta yayiwa zuciyarsa har baisan lokacinda ya rintse Ido ahankali ba tareda budewa zuciyarsa na Neman yin sanyi sbd a bazata yaji zancen.

Ahankali ya daga hannuwansa Yakai kan hannuwanta Yana kokarin janyeta kenan saiga Haj umma da umma yaganah kusan atare sun shigo palon kaman aike....

Da sauri Haj umma ta dakata tana kallon ikon Allah lokaci daya tana dauke idonta Kuma.

Umma yaganah kuwa juyawa tayi abinta batareda ta tsayaba tana jinjina sangantar Inayah sbd tasan itace me wannan aikin ba Abbin ba.

Ganin Haj umma yasa duk yaji yana sake shiga wani yanayi na sanyin jiki ya janye Inayah din zaiyi magana ta sake komawa ta maqalesa tana cewa"

Abbi Dan Allah kabarni da aurena zanyi biyayya akan da....

Salati haj umma ta sake tana maido da kallonta kan Inayah dataqi Kota kan idonta tabi.

Ba Shiri Haj umma ta kamo hannunta tana janyota gefenta tace"

Yaushe zakiyi nutsuwa nikam 'yar nan?
Yanzu uban naki kike damuqa haka gaban mutane kina maganar aure.

Tashi cikin turawa haukane akace Miki?

Maza wuce daki kisan abinda kikeyi
Mace da kunya da kamun Kai aka santa.

Haj umma idan na Kama kaina to Abbi zai iya auren wata yabarni da wannan auren..

Daga Haj umma har abbin kasa magana sukai sbd zancenta ya mugun Basu mamaki
Ya dago ya zuba Mata indanuwansa dasuka sake kashe Mata jiki tanajin kaman zuciyarta Zata fashe akan kishin hada sunansa da wata takuma rabarsa.

Haj umma kuwa sake sallamawa Inayah tayi sai takasa cewa komai ta qwalawa umma yagana Kira.

Umma yaganah najin Kiran tasan zaa Rina Indai akan MAJEED ne Inayah Bataji hakama Haj umma da alama itama tanada aiki tunda tana cikin uwaye masu kishin yayansu.

Umma yaganah na fitowa Abbin na wucewa batareda ya tsayaba Dan baisan mezai iya tsayawa saurara ba kuma.

Yaganah meyasa Inayah bakinta baya tauna zance ne?
Kunga illar rashin kwabarta
Gashinan sai zantuka takeyi marasa kan gado.

Cikin nutsuwa da umma yaganah tace"

Ya aka iya sai hakuri da addua Haj
Inayah din ce akwai kuruciya sosai atareda ita.

Fada Haj umma tafara Yi umma yaganah na Bata hakuri aka dai kashe maganar taja Inayah zuwa daki.

Bataiwa Inayah fadaba sbd itama zuwa yanzu tafara ganin rashin kyautawar Haj umma saidai Kuma bazata nuna hakan gaban Inayah ba sbd kada taci da ganin rashin kyautawar Haj umma din.

Batace komaiba Dan batada abin cewar Dan haka ta juya ta fice Takoma aikin datakeyi kitchen.

AA MAJEED na Isa bedroom dinsa zaunawa yayi kan sofa ahankali tareda Dan rintse Ido Yana dafe goshinsa sbd Dan juyawar da kansa keyi.

motsawan da zaiyi Qamshin black opium ya Shiga hancinsa daga kayansa na Inayah Dan haka ya miqe ahankali ya zare ya janyo towel maroon ya daura a qugunsa ya nufi toilet Yana Dan sake dafe goshinsa.

Wanka yayo yafito ya shirya cikin Kelvin Klein sweatset yana qamshi Mai sanyi ya fito ya nufi masallaci sallar magriba.

Tunda tadawo daki haka kawai takasa samun nutsuwa da sukuni tayita hawayenta tagama ta tashi itama tayi alwawala tayi sallar magrib tana idarwa ta dauki wayar Neesah daketa faman kiranta.

Sun jima suna waya tana Bata hakuri da qarfafa Mata gwiwa akan aurenta kafin suka kashe.

Wanka ta tashi tayi sbd batai niyar fita cin abinci ba tana fitowa ta saka Riga da wandon Balenciaga masu kauri tana kokarin hayewa kujera chatting ta tuna gargadin Abbinta na rashin fitowa cin abinci Dan haka ta miqe da wayarta a hannu tareda zira slippers ta fito tana qamshin black opium Mai sanyi.
Chapter 54 · 0% Book details