Sashe 9
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na gidanta aka yi zaman makoki aka gama kwana bakwai kowa ya watse. A ranar aka yi zaman farko da mijinta akan maganar yadda zaa yi da yaranta. Da ni da wasu daga cikin dangi, ga kuma babban yayanmu yaya Bellocity. A lokacin Adamu mijin Shariqah ya fara wasu kame-kame wanda baa gane in da ya nufa. Ya ce a bari ayi arba'in akwai wani tsarinsa da yake yi, aka bani hakuri aka ce mu zauna a gidan har a yi arba'in din. Mu na zaune a gidan ni da yayata daya da muke uba ya daya sai kuma kanwar mahaifiyarmu. Sai yarinyar da Shariqah take riqewa 'yar yayarmu ce mai suna Nidal mai kimanin shekaru goma sha uku, da ita yaran su ka saba sosai duk inda ta yi su na biye da ita. Su na zuwa makaranta su na dawowa. Sai kwatsam mu ka ji wata magana wai Adamu ya na so a bashi wannan karamar yarinyar da take rikewa wato Nidal zai aura. Yarinyar da take zaune a gidansa bai taba yin kara ya biya ma ta school fees ba, aka ce an sha koro ta daga makaranta idan Shariqah ba ta da kudi sai dai ta zauna a gida ta kusan cinye term amma ba zai biya ba. Da abu ya ci tura ma ta kasa Biyan private school sai kawai ta mayar da ita ta gwamnati Kuma me shekaru goma sha uku ce za ta reqe yara biyar? A lokacin ma babbar 'yar Shariqah ta na da shekaru tara, meye banbancinsu? Su dukka rainonsu ake yi. Dangi su ka yi masa caaa aka su ka ce ba zai yiwu ba, a ranar da ya furta kalmar nan a ranar aka zo har gidan suka dauke ta. Na kasa magana na zuba ido ina kallon true color sa, gaba daya kai na ya daure. Adamu fa da gaske yake ya kamu da son Nidal, har kama kafa ya je yana yi da iyayen yarinyar da kamanninta da sauran dangi, shi dai a bar shi ya aure ta, zata karasa karatun gidansa. Abin tambaya anan shine daman ya na son ta tun Shariqah na raye ne? Tabbas alamu sun nuna hakan, wato an tabbatar masa da cewa Shariqah za ta mutu har ya gama nasa plans din. Ikon Allah! Kaina fa ya daure ina kallonsu kawai. Shi dai dubararsa ita ce kada a fita da yaransa daga gidansa. Na dade da gane hakan, da ya fada min maganar Nidal, tambaya daya kawai na yi masa daga ita ban sake ba. "Shin me shekaru goma sha uku ce zata iya raino da tarbiyyar yara guda biyar?" Akwai wata yayarmu uba daya muke, bazawa ce, ta na da kirki sosai dan tunda aka yi rasuwar da ta zo ta dinga hidima da yaran nan, ita ce goyonsu, wankinsu, dafa abincinsu, wankansu, wasa da dariya da su. Nima hankalina ya kwanta da ta aure shi muddin an saka masa doka akan babu zalumci da tauye ma ta hakki kamar yadda ya yiwa Shariqah. Ba zaa sake zuba masa ido ayi shiru ya na yin abinda ya ga dama ba kuma. Saboda abinda na hanga na hango wannan hanyar shine kadai mafitar yaran dan muddin aka ce zaa fitar da yaran zaa sha rigima ba kadan ba. Ni kuma na rasa 'yar uwata na rasa dukkan wani farin cikina bana son wani tashin hankali kuma. Na ga alamar itama tana so sai aka yi shawarar cewar ya aure ta mana. Da aka fada masa sai nan da nan ya bata fuska ya ce shi sam babu tsarin auren bazawa a wajensa, haka ba zai iya auren babbar budurwa mai wayo ba. Sai dai 'yar shila wacce zai aura ya juya yadda yake so. Kuma alamu sun nuna ba dan 'ya'yan yake son yin auren ba kenan, bai damu da wacece za ta iya kula da su ba, kawai dan sha'awar kansa ne. Aka gama wannan sai ya gangaro maganar 'yar autarmu Dinar, 'yar kimanin shekaru goma sha takwas, wacce na ce miki a baya idan ta zo hutu gidansa sai dai a boye ta dan idan ya ganta korar ta zai yi. Ya ce itama a bashi zai aura, na ce masa ai gata ga shi ga kuma Mamarta. Anan na sami dama na fada masa dukka kuskurensa da yadda ya munanawa Shariqah. Ya firgita sosai dan ai ya zaci duk baa san musgunawar da yayi mata ba, tunda ya ji babu wanda ya taba tarar sa ya yi ma sa maganar. Da yake yana so a bashi kuma ya tabbatar ya aikata din, ai bai yi musu ba, sai ya shiga tuba gami da yin alqawarin zai gyara halinsa in sha Allah. Har dai aka cika kwana arba'in baa sami matsaya ba, da yawa daga cikin dangi sun nuna rashin amincewarsu ta yadda zaa sake daukar karamar yarinya a bawa mutumin da kowa ya san wahalar da ya bawa waccan. Hasali ma baqin ciki ne ya sa ta kamu da ciwon zuciya har ta rasu, babu wata kulawa da ya yi ma ta. Wannan abu a bude yake kowa ya tabbatar da hakan, an san halinsa an san halinda ake shiga a rayuwar gidansa. Wasu kuma su na ganin a bashi kawai saboda darajar yaran amma a ja masa kunne kuma shi ma da alama ya yi nadama. Yarinyar idan an yi ma ta maganar sai dai ta yi ta kuka ba ta amsawa. A zaman karshe wato ranar kwana arba'in Shariqah. Adamu ya so ace an gama magana an daura masa aure da Dinar kawai sai ta tare a dakin yayarta ba sai an kwashe yaran ba, amma abu ya ci tura dan baa tsayar da matsaya ba. Ransa ya baci sosai a lokacin da Bellocity ya tsura shi da tambayoyi ya ce "ka ce ba ka so a kwashe yara, mu kuma yanzu an yi kwana arba'in, zamu watse. Yaya kake so a yi da yaran? Ina za ka kaisu dan an ji kana hayaniya da uwar gidanka ta yi rantsuwa ta ce ba zata riqe su ba? Ko ta amince ma ai ba ita ce da alhakin riqon su ba, a addini dangin uwarsu ce. Sharifah ce ta fi cancanta ta karbe su, sai ta tafi da su. Wannan abu ya faru ne ba dan kowa ya na so ba. Sai Adamu ya fusata ya fada cikin fushi "shikenan a tafi da su." Ya tashi ya fice a fusace, ni na san kwarjinin Yaya Bellocity ne ya cika masa ido, dan mutum ne mai kwarjinin gaske, kai idan ka kalli fuskarsa ka san babu wasa. Ba ya so amma babu yadda Adamu zai yi muka kwashe kayan yaran, mu ka kulle kofar bangarenta, kowannenmu ya kama gabansa. Mu ka kauro gidan da su Hamidah suke zaune wato gidan da na kama haya wanda bashi da nisa da gidansa. A lokacin mutuwar ta dawowa kowa sabuwa fil, daga ni har yaranta da Hamidah. Haka muke lallabawa mu na rayuwa zuciya babu dadi. Na dauko Dinar daga hannun Mahaifiyarta don ta zo ta taya ni zama da kuma kula da yaran, sannan na samo mai aiki. Abinda ya fara damuna shine Adamu ya hana mu sakat, a koda yaushe safe da rana da yamma sai ya zo ganin yaransa. Sannan islamiyya ya ce bai yarda a saka su a ta kusa da mu ba, ya ce sai dai kullum Hamidah ta kaisu islamiyyar kofar gidansa kuma ta koma ta dauko su. Dan a zauna lafiya haka na takurawa Hamidah sai ta ajiye su sannan ta tafi ta su islamiyyar, sannan idan an tashi sai ta hau adaidaita ta dauko su. kullum sai baya magrib suke dawowa gida. Dokoki kala-kala dai mu na ta bi, bayan nan kuma ya ce duk asabar da lahadi a can gidansa zasu dinga yi, dan su dinga zuwa tahfiz tare da sauran yaransa.Nan ma na yi hakuri da hakan ake yin haka kullum. Bayan arba'in din Sharifah da sati biyu, kwatsam sai aka sanar da ni rasuwar babban yayanmu wato Yaya Bellosity ya rasu bayan yayi fama da gajeriyar jinyar kwana biyu." "nnalilahi wa inna ilaihi rajuun."Sharifah da Samha ne suka hada baki, suka fada a tare yayin da kowannensu ya yi shiru ya yi tagumi. Sharifah ta dago da jajayen idanuwanta ta ce "shine Bellon da nake sanar miki ya rasu na san baki san shi ba. A lokacin da muke yara har yayi aure, ya rasu ya bar mata uku da yara sama da ashirin shine babba a dakinmu. Shine mu ke ganinsa kamar uwa kuma shine uba, shine yake tsaya min akan komai nawa. Magana kuma ta kare Sharifah ta zamanto ba ta da iyaye bata da dangi, kusan dukkan masoyana sun tafi." Wannan karon Sharifah ta zubo da wasu hawaye masu zafin gaske yayin da tausayinta ya kama Samha matuqa. Samha ta sharce hawaye ta ce "sannu qawata ashe irin wannan tashin hankalin kika shiga amma baki taba nemana ba? Haba Sharifah ko dai ba zan amfane ki da komai ba amma mutum ai rahama ne, idan ina kusa da ke ai zan baki shawara, kuma in jajanta miki ai za ki ji dan sanyi " Sharifah ta sharce hawaye ta ce "na rantse da Allah ko motsi da kyar nake yi, ba na son yin magana ma, shiyasa bana riqe waya. Ba na bukatar taimakon kowanne bil'adama sai na Rabbul samawati. Ana cikin wannan hali na gigita da tashin hankali ga waccan ta Shariqah ga wannan ta Bello amma bawan Allah nan Adamu kullum yana cikin yi min kuri da barazanar zai kwashe yaransa. Dan ya ga na damu matuqa da son rikon yaran, kuma ina bin dokokinsa. Sai ya zamanto ma ya fara na nuna min, ai dole ma in bashi auren Dinar ko kuma ya kwashe yaran. Daga baya na fuskanci baya neman amincewar yarinyar dan ko ya zo bata kula shi ya san bata sonsa dan haka ni ce zan yi ma ta dole. Ko unguwa na fita sai ya fara bambamin fada yana kumfar baki wai na fita na bar yara zai kwashe su." Samha ta kama haba ta ce "ikon Allah sai kace shi yake aurenki. Kullen da ya saba yiwa Shariqah ne ya