Sashe 3
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
*** *** ***
Maman Samha ce take ta kiransu a waya hankalinta a tashe yake, ta kira lambobi kowannensu bai amsa ba. Ta shiga gagarumar damuwa dsn ta na zaton fatalwar ce ta tafi da su.
Sai yanzu wayar Samha ta shiga girgiza, ta dauko da sauri ta duba taga 7 missed calls din Mama.
Ta dubi Anas da Aliyu a gigice ta ce "Mama ce fa take ta kira ashe. Waye ya ce ma ta mun fita ne?"
Anas ya tabbatar ma ta da cewa shine ya fadawa Samira, ko da ta Allah kan kasance aksnsu asan inda suka tafi . Kowannesu ya zaro wayarsa daga aljihu ya duba ashe ta kikkira su babu adadi.
Anas ne ya zabura ya tashi da sauri ya ce "bari in sauka kasa in kira ta."
Ya na sauka ya kira Mama ya fara yi ma ta bayani.
Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " dole hankalin Mama fa ya tashi, kun zo gidan fatalwoyi ta ji shiru, ku ce ina gaishe ta kuma zan kawo ma ta ziyara."
Sai su dukka suka kwashe da dariya har da Sharifah. Yayin da Samha da Aliyu kowannensu nauyinta ya kama su.
Anas dai ya na ta faman yiwa Mama bayanin cewar ga su ga Sharifah da iyalanta mutane ne ba fatalwa ba, ta fayyace musu komai ashe duk rashin fahimta ne ya sa ake yi ma ta kallon fatalwa.
Mama ta ji bayanansa banbarakwai zuciyarta ba ta yarda ba.
Ta hau shi da fada ta ce "babu irin sigar da shu'umar yarainyar nan bata iya biyowa ba, dan ta yaudare ku, ta halakar da ku. In ga fatalwa da idanuwana har sau biyu. Daya da yamma a gidana daya a asibiti da tsakar dare a sigar gurguwa yanzu ka yi min musu ka ce ta gyaru ta dawo mutum. Ka fadawa Samha da Aliyu ku gaggauta barin gidan nan ko in yi muku baki."
Anas ya zabura ya ce "Ah Mama me ya yi zafi haka? Allah Ya baki hakuri bari in kira su mu taho. Menene abin yi mana baki kuma? Tunda ba ki fahimta ba shi kenan ai."
Anas ya ji nauyin yadda zai shiga ya fada musu wannan sako na Mama a gaban Sharifah, ga labari ya kwaranyo dadi.
Anan ya tsaya ya tuttura musu text massages ta waya ya ce lallai-lallai su taso su tafi, ran Mama ya baci ta ce su taso."
Kowannensu ya karanta sai suka hada ido su ka yi shiru, can da aka jima kadan sai Anas ya shigo ya sami waje ya zauna.
Sharifah ta duba agogo ta ce "ya kamata ku tafi Mama na kira nima.kuma ina da ganawa da zan yi da Matar gwamna akan wasu harkoki. In sha Allah za mu hadu wataran ma karasa labarin."
Daga dukkan alamu ta fahimci abinda Mama ta ce da sakonni da Anas ya turo mu su a waya.
Sharifah ta raka su har kofar gida bakin get inda suka ajiye motarsu suka shiga su ka tafi.
Kowannensu zuciyarsu cika da mamaki su na ganinsu kamar a mafarki, ga su tare da Sharifah da ake gudun famfalaqi idan an ganta, yau gata ga su har ta yi musu rakiya.
Tabbas su na cike da mamaki gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Allah Ya sa suka gane ba fatalwa ba ce, sannan kuma dan cikin Samha mutum ne.
Gidan Mama aka wuce kai tsaye aka same ta a farfajiyar get ta na ta kai kawo ta kasa zama a waje daya dan fargaba.
Ta na ganinsu sai ta ji hankalinta ya kwanta bayan sun gaishe ta, aka dunguma zuwa cikin gida. Bayani suka yi mata tsaf akan tabbacin Sharifah mutum ce ga dalilan abubuwan da suka faru har ake zaton ba mutum ba ce.
Wasu dalilan Mama ta aminta wasu ne basu kwanta ma ta ba, ita dai koma menene ayi baya-baya da Sharifah kawai.
Samha da Aliyu suka sauke Anas a gidansa, kamar yadda suka dauko shi sannan suka wuce gidansu suma. Samha na shiga gida ta bugawa kawayenta su Nana Ahmad waya ta basu labarin Sharifah cewa mutum ce ba fatalwa ba ce.
Ta fada musu dalilan da ya jawo suke tunanin ba mutum ba ce. Su ka tambaye ta ko ta bata labarin abubuwan da suka faru da rayuwarta ya jawo har kamanninta suka canja kuma menene maqasudin shariar ta a kotu?
Samha ta tabbatar musu Sharifah ta shirya bata labarin rayuwarta bayan rabuwarsu sai kuma Mama ta kira su ta tubure ta ce su bar gidan. Amma za ta samu ta lallaba Mama ta bar ta su sake haduwa da Sharifah don jin ci gaban labarin. Sai dai ba ta sani ba ko sirri ne tsakaninta da ita, ko ita kadai ta fadawa ko kuma zata so kowa ya ji. Idan sirri ne toh ba za ta fada musu ba amma idan Sharifah ta amince kowa ya ji toh za ta sanar musu.
Su Nana suka nemi da ta samo musu lokaci su hadu su dukka su je gidan Sharifah su ba ta hakuri akan gudun ta da suka yi, a lokacin da ta kawo musu ziyara gidajensu. Samha ta tabbatar musu cewa zata fada mata.
Aliyu ya kula da matarsa ta dawo yadda take ada, ga hira da girken-girken da aka saba yi masa ana yi yanzu, bayan kwalliya da kalaman soyayya wanda dukka ya rasa su a baya.
Sai ya ji dadi sosai kuma sai a lokacin ya sanarwa da 'yan gidansu labarin bayyanar cikin Samha. Dan duk tsawon lokacin nan bai fadawa kowa ba dan ana tunanin fatalwa ce ta yi ajiya. Amma yanzu komai yayi daidai dan haka ya daki kirji ya fada.