← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*** *** ***
Bayan kwana biyu da rana misalin karfe biyu, Aliyu yayi tafiya, Samha na zaune ita kadai a falo ta na kallon talabijin. Sallama ta ji a bakin qofar falonta ba tare da ta ji an taba get ba, duk da ma dai get din a bude yake amma tana jin karar sa idan an taba.
Muryar da ta ji ta daga ma ta hankali, ta yi kama da muryar Sharifah ko Shariqah ko Hamidah. Sai ta zabura ta miqe ta koma bayan kujerar lungu ta tsaya, ba tare da ta iya amsawa ba.
Ta ga an bude labule an shigo sai ga Sharifah ta bayyana muraran, hannayenta dauke da manyan fulasanta na abincin da suka kai ma ta.
Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu sannan Samha ta tuna ashe bakuwarta ce, kuma sannu da zuwa da murmushi ake yiwa baqo.
Samha ta washe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "yau Sharifah a gidana? Sannu da zuwa, ki zauna."
Sharifah ta yi murmushi sannan ta sami kujera ta zauna. Yayin Samha ta shiga kicin hannunta na rawa ta dauko lemo da ruwa ta kawo ma ta. Sannan ta sami kujera daga nesa-nesa ta zauna. Kirjinta na faman dukan uku-uku.
Bayan sun gaisa Sharifah ta ce "daga makabarta nake wallahi, na ce dai bari in biyo in ajiye miki fulasan nan in yi miki godiya."
Samha ta dafe kirji ta maimaita "makabarta kuma? Me ake yi a makabarta? Waye ya rasu?"
Sharifa ta shafa kai ta ce " na je ziyara ne. Na jewa Shariqata visiting. Kin san ana je musu visiting da guzurin addu'a ko?"
Samha ta gyada kai cikin matsanancin tsoro ta ce "eh haka ne. Ina zuwa."
Ta shiga daki ta dauko takarda da biro ta rubuta wasiyya.
Ta ce "idan kun tsinci gawata ko an rasa ni na bace toh Sharifah ce, ta zo gidana ga mu mu na tare daga ni sai ita a gida."
Kamar daga sama ta ji Sharifah ta kwalla ma ta kira, sai ta fito a gigice.
Sharifah ta kalle ta ta yi dariya, ta ce "canza min tasha ina so in kalli wani horror fim a MBC 2, zasu maimaita yau. Jiya na fara kallo na yi bacci. Fim din Matattu ne, su na fitowa daga kabarurrukansu. Daga sun ciji masu rai sai su ma su zama su."
Samha ta ji gabanta ya fadi da alama yau ta zo ta cije ta itama ta zama su. Hannunta na rawa ta dauko remote ta miqawa Sharifah yayin da ta yi wuqi-wuqi da ido, ta yi baya-baya ta zauna daga nesa da ita.
Ana gama fim din da ake yi yanzu zaa fara wancan fim din na matattun da take so.
Sharifah ta na ta yi ma ta hirar yadda abincin yayi dadi, sun sha santi.
Har aka gangaro hirar su ta rannan akan rayuwarta. Samha ta fara sakin jiki akan babu yadda za ta yi dole ne ma ta sake.
Samha ce ke tambayarta akan a ci gaba da labarin rannan amma da alama ma yau Sharifah ba ta son hirar.
Samha ta ce "Su Nana sun ganki a wajen yayanta Barista kin je rannan sai suka ji tsoron yi miki magana saboda sun fi son su zo har gida su baki hakuri. Sun yi miki laifi ba dadi su baki hakuri akan hanya."
Sharifah ta galla ma ta harara har sai da gaban Samha ya fadi. Sharifah ba ta bata amsa ba, ta ci gaba da kallon talabijin.
Sai can ta ce "ai kun zo har gida kuma ku ka sake guduwa."
Samha ta sunkuyar da kai ta kasa bada amsa.
Sharifah ta kwashe da dariya har sai da Samha ta tsorata sannan ta ce " ku na bani mamaki, amma ba abin mamaki ba ne dan har yanzu ba ku san mutuwa ba ne ba ne, ba ku taba rasa wani makusancinku ba shiyasa har ku ke tsoron mutuwa da matattu."
Samha ta gyada kai ta ce "har da wannan ma."
Sharifah ta gyara zama ta ci gaba da cewa " Na tsaya a inda na ce a lokacin ina zama a kudu ni da mijina. A dalilin rashin lafiyar Shariqah na ji gara kawai in dawo kano in zauna a kusa da ita. Na kauro Kano na kama haya a kusa da unguwar da gidan Shariqah yake bai wuce naira hamsin a adaidaita sahu ba, na samowa Hamidah makaranta ta ci gaba."
Samha ta ce maigidanki fa?"
Sharifah ta tabe baki ta ce "a can na bar shi yana zuwa ina zuwa daman zamana da shi babu dadi na fi sha'awar mu rabu saboda daga ni har 'yarsa ba ma jin dadin zama da shi. Baya tsinana mana komai da albashinsa. Komai ni nake yi a gidan.Ya qi yin saki kuma baya kyautata min. So yake mu yi aure irin na 'yan duniya mu daki juna, mu zagi juna sannan mu fito titi mu tarawa kanmu mutane sai kuma mu koma gida mu bawa juna hakuri mu ci gaba da zama.
Da na fahimci haka yake sai na ja masa layi ba na kula shi sam, abinda na sani shine aure bautar Allah ne aljannar mace tana karkashin tafin kafar mijinta, idan haka ne ba zan taba samun aljanna ba a irin wannan rayuwar ta mu ba."
Samha ta gyada kai ta ce "wannan gaskiya ne, kin yi daidai."
Sharifah ta ce "Dan haka na dinga baya-baya da shi dan kada ya illata mu. Na matso kusa da 'yar uwata dan na kula da ita kuma na taimaka ma ta sosai da kudina da kuma jikina da shawarata.
Kwatsam wata dama ta samu ni da shi daman mun nemi tafiya turai Allah bai yi ba sai daga baya damar ta samu mu ka yi shawara mu kaura kawai.
Na bar Hamidah a gidan da na kama haya na dauko wasu daga cikin dangina suka zauna da ita. Ina so ta gama sakandire sai in zo in tafi da ita kawai.
Mu na can har mu ka shekara daman kamar yadda na fada miki a baya zamana da mijina a cakude a waje daya matsala ne, kullum fada.
Abin ya zamanto har da cin amana kuma na gano shi ya fara son wata kawata acan, na gane abinda ke faruwa kawai na sallame shi mu ka rabu, na kama gaba na ya kama na sa gaban.
Daga baya ma ya kasa zama ya dawo Nigeria ya ci gaba da lalacinsa. Ni ce daman me zafin neman na ci gaba da gina sana'a ta a can ni da wata kawata mai suna Fatima kt mu na zaune tare. Ina samun abin rufin asiri ina turowa gida ina taimakon 'yata da 'yan uwana musamman Shariqah.
Chapter 7 · 0% Book details