Sashe 10
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dawo kanki kuma?" Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " ke ma kya fada. Ni ko can asali ma ban taba sanin auren kulle ba, balle yanzu, ba mijina ba komai ba ya ce zai takura min. Da gadara yake tambaya sai ta, ya ce min yaya maganar aurensa da Dinar? Amsar da nake bashi ita ce ga ka ga ta nan ai, ku daidaita. Sai ya ce "ai ita yarinya ce ke za ki yi ma ta dole." Na ce "ba zan yi ma ta dole ba ko da kuwa ni na haife ta balle ban haife ta ba, dan yanzu an wuce yin auren dole." Samha ta ce " tab daman har yanzu akwai mutane irin wannan mutumin. Tun yaushe aka daina irin wannan rayuwar?" Sharifah ta ce "neman rigima ce kawai da nuna isa da izza. Irin wacce ya saba yiwa matansa, yana nuna musu mulki da sarauta shine abu ya dawo kaina. Da son takurawa mutane da neman fada. Ya nunawa kowa bai isa ba sai an bi abinda yake so kuma yana ganin kamar bani da kowa. Ashe ta karkashin kasa dangina da dama sun bashi goyon bayan ya yi min hakan. Da na gane inda ya nufa sai na cire tsoro da shakka, zuciyata ta dake. Da na ga ya fara bin dangina yana kama kafa da su sai na zuba ido. Anan aka sami mararsa kaunata da wasu masu kaunata. Aka sami wata da ta bashi labarin cewa anan qasan gidan da muke ma Dinar ta yi saurayi kuma ina sane amma na bar ta take kula. Ya zo a gigice kuma a fusace zai hau ni da fada wai ya ji labari Dinar ta yi saurayi kwanan nan kuma ina sane. Na taka masa burki na ce ka sani fa Dinar ba jaririya ba ce 'yar goye kuma tana da zabi, sannan ni ba zan yi ma ta dole ba kuma munafukar da ta fada maka haka ka je ka fada ma ta an yi din. Kuma wallahi a lokacin ban ma san komai akan maganar wani saurayi da Dinar ta yi ba, abinda na sani yaron yana da shago a kofar gidan da nake yana da kirki yana taimaka mana da aike da sauransu ko sunansa ban sani ba ma da farko. Daga na fita zan ga yana ta gaishe ni. Shine har su 'yan waje da suke wata unguwa har su ka san da labarin yaron aka je aka dinga juya magana. Nan fa ya fuska ya dinga zagayawa gidajen wasu daga cikin dangina aka barke da gulma kala-kala, ana zuga shi." Samha ta ce "ikon Allah yanzu a danginku har a sami mai bin bayan mutumin da ya azabtar da 'yar uwarsu? bayan duk abinda ya yiwa Shariqah? Kai amma zumunci ya lalace wallahi." Sharifah ta gyada kai ta ce "me kika ji ma ai abu na gaba kawata, za ki sha mamaki ace jininka ne yayi ma ka haka. Can kuma ga Shariqah ta kasa kwanciya a cikin kabarinta akan wannan dalilin." Sai Samha ta zazzare ido ta ji gabanta ya yanke ya fadi dan an dawo kan labarin matattu kuma." Cikin jimami Sharifah ta ci gaba da cewa "Ga ni na da ita na farko a bakin wata rijiya ne, na ganta ta na zaune ita kadai ta yi shiru ta sunkuyar da kai qasa idanuwanta a runtse. Na yi ma ta magana, ba ta dago ba. Na jijjiga ta ta runtse ido ta qi dagowa. Daga nan ta bace min da gani, na yi ta duba ta ban kara ganinta ba." Sai Samha ta dafe kirji ta ce " Ya salam! A bakin wacce rijiya kuma? Da safe ko da daddare?" Sharifah ta ce " gab da magrib. Daga nan na fara tunanin akwai abinda ake yi wanda ba ta so. Ina tare da yaranta zuciyata na quna na rasa karamar kanwata, na rasa babban yayana wanda nake ganin shine namijin da zai tsaya min a dukkannin lamurana. Rayuwa ta tsananta a lokacin ba na so in ga kowa ko in yi magana da kowa. Lokacin mutuwar tana tsaka da cin zuciyata na tana cin zuciyar Hamidah sosai kowa a cikinmu babu kuzari. Yaran Shariqa musamman masu wayon su na cikin alhini su kan shiga daki su kwanta akan kayanta su na kuka. Ina ta faman amsa tambayoyin kananan yaran, su na tambaya ta cewa Muminsu ta na asibiti amma me yasa har yanzu baa kai su sun duba ta ba. Ina iya kokarina wajen kawar musu da hankali. Ina ta shirya karya kala-kala wajen kwantar musu da hankali. Kowa da irin yanayin da ya fi so ya kasance idan ya shiga damuwa, wani ya fi son ya zauna yayi shiru, wani ya fi son yayi ta barci, wani ya fi son yayi ta kuka, wani kuma ya na son ya shiga cikin mutane, wani baya san ya ga kowa a kusa da shi. Nawa yanayin na fi son in zauna shiru a daki, bana so in yi magana, ba na so ayi min. Idan na kebe ni kadai a lokacin nake iya yin kuka ba tare da wani ya ganni ba. A daidai wannan lokacin da bana so in ga kowa in yi magana da kowa shi kuma mijin Shariqah ya kafa zarya a gidana yana kulafucin yaransa. Ya na ciyar da su yadda ya kamata abubuwan da bai basu a baya ba ma a yanzu yana kawowa, komai baja-baja amma bai dame mu ba. Babu mai iya ci, mai aikina ce da wasu kalilan daga cikin yaran ne ma ke iya ci. Dinar da Hamidah ba komai ne yake burge su ba sai sun zaba. Dokoki dai na takura barkatai alhali a lokacin bana son a takura min ko kadan abinda yake damuna shi yake damuna. Wannan dalilin ya sa ma na yanke alaqa da dukkannin kawayena ban sanar da su rasuwar ba ma dan bana so a dinga zuwa inda nake. Sauran kawayena wadanda na saba da su daga baya a harkar kasuwanci ko a gari su ma na guje su, babu wanda ya san a ina nake mo me nake ciki. Abinda zai ba ki mamaki zai daure muku kai shine na baro dukka abinda na mallaka na kasuwanci a hannun abokiyar kasuwancina Fatima kt. Ni ce karfin tsayawa har kasuwancin ya kafu, jarina ne ya fi yawa. Na rantse da Allah matar nan da yake bata tsoron Allah sai ta hada dukka ta cinye. Bayan ta fada min bakaken maganganu ta yi blocking dina a dukka wata kafa da zan same ta. Na sayi ticket zan je in hado kayana amma matsalar Corona ta ballo kai babu shiga babu fita. Haka aka soke tikitin ban Sami tafiya ba. Ashe bala'i ya na gaba, dukka wannan wasa ne. Ina zaune ina ci gaba da kula da yara su na zuwa makarantu islamiyya da boko ga kanwata ga mai aiki kowa yana iya kokarinsa. Ban San yadda ake raino ba dan ban iya shi ba ma, saboda nawa rainon Shariqah ce ta yi min. Yanzu Allah Ya juya lamuransa ni ce nake yi ma ta rainon. Daman haka aikin alkhairi yake idan ka yi abin alkhairi ko bayan ranka za ka tsince shi a gaba. Ga shi dai yadda ta yi min wahalar raino ba tare da ta yi tunanin zan biyata. Duk duniya banda yaran Shariqah babu wanda zan iya riqewa haka. Na salwantar da duk abinda nake da shi na yarda in rasa komai, na yarda in takure rayuwata in zauna waje daya dan kawai in kula da yaranta. Akan maganar auren Adamu da Dinar Allah shine shaidata na kira Dinar na zauna da ita na bata shawara akan ta nutsu ta yi tunani ta gani ko za ta iya yin wannan jahadin ta aure shi dan ta riqe yaran 'yar uwarta. Amsar da ta bani ita ce ta sa ban sake shiga maganar ba, ta ce dani ta rantse da Allah ko kwana daya ba za ta iya auren mutumin nan ba. Ta zayyano min wasu daga cikin mugayen halayensa wanda ta gani kuma wasu ta ji labarin wasu. Na ce ma ta amma ai ya ce ya tuba zai gyara halayansa, daga yanzu mace za ta sami 'yanci. Ta ce min "haba Aunty ko watanni uku baa yi ba fa da na je gidansa aka boye ni dan idan ya gan ni kora ta zai yi. Mutumin da ina matsayin kanwar matarsa uba daya amma bai san ni ba ban san shi ba, tsabar bai dauki danginta da muhimmanci ba." Na gasgata maganata, maganar kyautawa sam bai kyauta ba, amma yaya zaa yi tunda zuri'a ta hada, yara ba ba daya ba ba biyu ba har guda biyar. Ni kaina ina neman mafita ne dan ba zan iya zubar da yaran nan in tafi ba, in dai ba na sami takamaimai in da na tabbatar zaa kula da su ba ne. Idan kuwa babu dole in zauna da su, in hakura da komai nawa na rayuwa. Wannan shine ma abinda zai fiye min kwanciyar hankali tunda 90% na tabbatar bayan uwar da ta haife mu ni da Shariqah babu mai riqe yaran nan kwatankwacin uwarsu irina. Saboda haka ko da ace aurensa da Dinar ya tabbata ba zan ba ta yaran dukka ba sai dai in ba ta masu dan wayon su biyu zuwa uku kanan sai dai in riqe su. wala in zauna da su a kasar nan ko in tafi da su kasar da nake zama. Wanda na san halinsa ba zai yarda ba sai dai in an kai ruwa rana. Mu na cikin wannan hali maimakon dangina su shiga maganar a sasanta.A' a sai zuga da ake ta kai masa, gulma kala-kala, sai da aka bata a alqata da shi gaba daya. Wata rana ya zo ya same ni ya ce yana so akai masa yaran weekend su dukka har yar karamar da bata shiga makaranta ba. Na ce manyan dai su uku banda kananan ya ce su dukka yake so. Hamidah ta ji hankalinta bai kwanta ba ta ce da ni "Mama kada ki bayar da su dukka kada ya hana su fa." Na ce haba dai shima ba zai fara ba. Haka