← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** *** **** A satin da Shariqah za ta rasu na sami mai zuwa nan Turai na ce ta aiko min da gyararren wake da gyadar kunu. Kasancewar na san ba ta da kudi sai na turo ma ta da kudi na kashewarta da kuma wanda za ta sayi komai. Aka ce ita ta gyara min da hannunta, dan tayi-tayi da mai aikin ta yi ta qi mayar da hankali, dan haka sai ta yi da kanta. Ta rame sosai kasancewar ciwon ya na ta cinta. Na yi ta fama da ita akan ta turo min hotonta in gani amma ta qi, ashe ba ta so in ga yadda ta zama ne ta san hankalina zai tashi. A waya dai ga muryarta nan tangararai ashe jikin ba dadi. Koda yaushe muna hira a whatapp da sabuwar wayar da na turo ma ta, ta sare gaba daya ta ji a jikinta zata rasu. Muna hira na ce ma ta kwana biyu sai in ji zuciyata babu dadi, gabana ya na ta faduwa. Budar bakinta sai ta ce "ko ni ce zan mutu?" Na rasa amsar ma da zan ba ta yayin da hankalina ya sake tashi. Ana cikin wannan hali kwatsam Hamidah ta kira ni tana kuka ta ce min " Mama sai in ji na kasa bacci kirjina yana ta bugawa, zuciyata na tsinkewa." Nan ma na ji hankalina ya tashi matuka, na cewa Hamidah ta yawaita yin addu'a sosai da yawan alwalla da sadaka. Shariqah ta bani labari a waya ta ce ta kasance tana yawan yin barci mai nauyin gaske a koda yaushe, ba dare ba rana ba safe. Baccin da kowacce irin hayaniya ake yi ba ta ji, sannan kuma ayi ta tashinta ana girgiza ta dakyar take tashi. Ta tabbatar min wata duniya take tafiya, tana ganinta tana biye da wani mutum. Mutumin ya na hawa saman duwatsu, tana biye da shi. Sai ta waiwayo ta dubi bayanta sai ta ga 'ya'yanta guda biyar din nan dukka a warwatse wancan a wani lungu wancan a yashe a wani waje daban, sai ta zo ta na ta kokarin harhada su a waje daya amma sun ki haduwa. Sai ta hada wadannan sai ta sake hango wancan a can wani a wani waje, in ta dauko shi sai ta ga wancan a wani lungun. Tayi-tayi ta hada su a awaje daya ta kasa. Da ta fada min sai na yi shiru dan akwai tashin hankali babba a cikin labarin mafarkinta. Nima ina can ina yin nawa mafarkan, na ga daki guda ya kama da wuta, sai na fito a gigice da yara guda biyu a hannuna. Da na fada ma ta sai ta ce "ko dai mutuwa zan yi" Ban san ciwon ta ya kai haka ba, har nake ta kokarin ba ta kwarin guiwa, na ce ta fara yin business zan turo ma ta da kayan yara da takalma ta fara siyarwa. Ta amince nan da nan take ta murna. Akwai wani gidana karami da na taba siyar ma ta, ba ta fada min kai tsaye cewa mijinta ya qi kai ta asibiti ba amma ta ce min in karbi gidana in mayar ma ta da kudinta har ma ta yi mun ragin 500k hakan ya nuna a matse take da kudin. Ashe lafiyarta ta ke so ta tafi ta nemo. Na Amince har na tura ma ta wasu daga cikin kudin na fara biya. Hamidah ta dauke ta a hoto ba tare da ta sani ba ta turo min "innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Ashe babu Shariqah, a kashi goma saura kashi uku, Shariqah ta kare ta rame sai kashi ga gayo tana yi. Karfin hali kawai take yi da take iya magana, ba ta daina aikin girki da yiwa miji wanki ba. Bayan kwanaki biyu Hamidah ta kira ni a gigice ta ce ga Muminta Shariqah babu lafiya, ta zo gidan ta same ta a yashe a kasa a falo, mijin ya fita bayan yaran sun je da gudu sun fada ma sa ba ta da lafiya, ya zo ya kai ta a asibiti. Ya ce baa fada masa da wuri ba, shi yanzu fita zai yi. Ko leqawa bai yi ya ga yanayin jikin ba. Bayan Hamidah ta wuni a makaranta ta je gidan sannan ta iske ta a cikin wannan hali. Daga ita sai yara kanana da mai aiki. Na cewa Hamidah ta samo adaidaita ta kai ta asibiti, yariyar nan karama ita ta saka ta a cikin adaidaita sahu su ka tafi. Kowanne asibiti baa karbe ta ba saboda babu gado kuma ba su da na'urar oxygen din da zaa saka ma ta saboda numfashi ya dawo sama-sama. Hamidah ta kira su Bello da sauran dangi aka hadu da su aka dinga fama. Mijin nan bai dauki waya ba har dare, babu irin kiran da baa yi ma sa ba ya qi dagawa. Karshe dai suka kai ta wani asibitin kudi, tunda babu gado ana gwamnati kasancewar a lokacin ana wani irin anobar zazzabi. Aka ce sai can da daddare mijin ya zo ya na ta yi ma ta tsawa. Wasu daga cikin dangi su ka hau kansa da fada sannan ya sassauta. Da kyar lokitoci su ka ceto rayuwarta, ta samu ta warware kadan, har muka yi magana a waya da ita.Bayan kwana biyu tana asibitin jiki ya sake rikicewa, na kira su a waya yadda na ji kowa a rikice na san Shariqah kuma babu. Na yi addu'a, na yiwa Allah SWA bakance, na yi sadaka, na saka dukkannin Malamai bayin Allah da na sani su sauke ma ta qur'ani akan Allah Ya jinkirta ma ta, Ya tashi kafadunta. Na yi tawasali da dukka kyawawan ayyukana da kaunar da nake yi wa Annabinmu dan gatan Allah Muhammadu Rasullulah (S.A.W)." Sharifah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa yayin da hawaye ke zuba kamar an kunna famfo. Samha ma sharce hawaye take tayi ta yi dan yaqi tsagaitawa. Ta miqawa Sharifah tissue ba tare da ta iya magana ba. Sharifa ta karba ta goge ta face hanci, ta dago ta dubi Samha da jajayen idanuwanta Ta ce "Allah sarki Samha na zo na ba ta miki mood dinki, na tayar miki da hankali, na saka ki kuka." Samha ta ce "in ban tsaya na saurari labarinki ba ba zan taba yafewa kaina ba." Sharifah ta gyada kai ta ce "Na gode da kulawa sosai." Samha ta ce "ci gaba da labarin ina sauraro." Sharifah ta cije baki ta ci gaba da cewa " Wane mutum, babu gudu babu ja da baya idan lokaci ya yi, ko sakon daya Allah ba zai qara ma ka ba. Duk duniya babu mai iya hanawa, me afkuwa ta afku. Ba zan taba manta da yadda na ji baqin labarin nan ba. Shin mafarki nake yi zan farka ko da gaske ne? Haka nake shafa jikina dan in tabbatar. " Innalilahi wa inna ilaihi òrajuun." kawai na ke ambato. Kamar in yi fuffuke in diro Nigeria haka na ji. An sanar min ga Hamidah ta suma ga Bello ya dimauce. Babu abinda zan iya yi, nima ta kaina nake yi, ni kadai a kasar da ba tawa ba, sai ni sai kawaye da abokan arziki ne ke kewaye da ni su na bani hakuri. Na kasa kuka ma sai kirana ake ta yi a waya, daga ko ina a fadin Nigeria saboda ni na fi cancanta a yiwa jaje akan rasuwar Shariqah. Ban qi in kwashe dukkannin kudina da na mallaka a duniya dan in sayi sabon tikiti ba, in har zan samu tafiya a ranar.Mutumin kirki wani Alh. Musa ya yi min dukkan kokarin da zai yi, na hau kan return ticket dina ba tare da an kashe wasu kudi da yawa ba. Ta rasu cikin dare ta yi kwanan kaso da safe aka yi ma ta Jana'iza, ana sanar min da komai a waya. An fadi irin taron jama'a da suka sami halattar jama'izarta, ana yi ma ta kyakykywan zaton samun rahamar Ubangiji. Bayan ta cika da kalmar shahada kowa ya budi baki kyawawan halayanta ake ambato, fara'a, da kyauta, wasa da dariya, ta zauna kowa lafiya. Alhamdulullah ." Sharifah ta yi shiru zuciyarta na bugawa da gudu yayin da idanuwanta su ka ci gaba da zubar da hawaye masu zafi. Ta ci gaba da cewa "Wannan rana ta na daya daga cikin baqar ranar da ba zan mantawa ba. Baqaqirin kuwa, mai duhu gami da daci. Ban sami tafiya ba sai washe gari cikin dare, kowa a cikin Jigin nan sai da ya gane ina cikin bala'i. Na kasa tsayar da hawaye, komai ma na kasa ci ko sha. Ma'aikata masu kulawa su ka dinga zagayowa su na bani hakuri haka fasinjojin da suke zaune a kusa da ni su ka dinga lallashina. Hawayen ya na kwaranya da kansa ne ba tare da ina so ba. Radadi nake ji a can cikin zuciyata kamar ana gobara, na tabbatar na yi rashi a rayuwata, na sake samun qibi wanda ba zan taba dawowa daidai kamar da ba. Farin cikin rayuwata fiye da rabi ya tafi, babu dawowa sai dai maleji." Fuskar Samha ta jiqe sharkab da hawaye yayin da itama radadi da zugi ya mamaye zuciyarta. Ta dafa kafadar Sharifah ta na lallashi ba tare da san kalma daya tak da zata furta wacce zata kwantar ma ta da hankali ba. Sharifa ta sharce hawaye ta ci gaba da cewa "Na isa airport din Kano masu zuwa daukana su ka zo suka dauke ni, ban ma kira dangina ba dan na san su na cikin alhini, na fi son su gan ni kawai. Kwatsam dangina suka gan ni na diro, kowa ya ganni sai ya fashe da kuka amma fa ni na kasa yi. Yaranta na fara nema aka kawo min su, kanana da su abin tausayi. Allahu akbar! Na saka a raina kuma na furta a sarari "kun rasa uwa a zahiri amma ba ku zama marayu ba, tunda ina raye." A lokacin ban ma san ta bar wasiyya a fada min ba cewa kada in bar yaranta su rayu a wannan gidan ba." [3/1, 2:17 PM] Jamila Umar Tanko: 4 Ashe tashin hankali na gaba, na baya dukka wasa ne. Mu
Chapter 8 · 0% Book details