← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 23

Sashe 14

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

ci gaba da cewa "shin ba ki bata labarin baqin karen da ya cije ki ba ne, har ya zama ajalinki ba ne?" Sharifah ta girgiza kai ta ce " ban bata wannan labarin ba dan na san kwakwalwarta ba zata taba ganewa ba Fanna. Mu kadai ne muke gane labarin juna." Samha ta fice daga falon ta isa farfajiyar gidan, sai ta fara tunanin ko ta fice ta shiga maqwabta duk da bata da gyale a jikinta, dan ba zata iya zama a kusa da ajalinta ba. Ba ta ankara ba ta ji an dafa bayanta, sai ta daka tsalle ta waiwayo a gigice. Sharifa ce dauke da mayafinta da mukullin mota da alama zata tafi. Wannan karon da Bello take magana a waya, ya na jiranta ne a gida zai fita da motar. Ba su sami damar yiwa juna magana ba, sai dai suka dagawa juna hannu, Sharifah ta fice da sauri.
Chapter 14 · 0% Book details